← Book details Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 98

Sashe 48

Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

BIKI-BIDIRI
Ga al’adar mutanen Giwa da yammacin Laraba ne muke kamu, washe gari alhamis kuma ayi budar kai. Don haka ban yi mamakin jin hargowar jama’armu ba daga ko ina cikin garin Giwa, Zaria, Kaduna da makotansu sun cika A.B Estate. Masu kidan kwarya sun soma wasa korai da gyaran murya cikin lasifaka, masu guda na yi, maroka na ma Hajjah kirari duk inda ta gifta.
Na tabbatar dai al’amarin nan da nake dauka almara nema yake ya tabbata, za su hadani rayuwa da Ya Fa’iz ne ko babbaka su zan yi. Lallashin ma babu mai lokacin yi min shi, shima Yaya Aliyun tun ranar da yasa kafa ya bar gidan ban kara jin ko tashin muryarsa ba.
Ummi da Zanirah babu wacce ta kara shiga sabgata, na kan ga dai Fa’iza ‘yar Zanirah ta rarrafo dakin da nake tana wasanta, ta yi ta gaji ta fita ko sanin da halittar dan Adam bana yi a dakin, domin ruhina da kulliyar tunanina baya wannan duniyar tamu, yana cikin wata duniya ta kunci, azaba da tafasar zuciya da zabalbalar kwallah.
A yau na yi amanna da cewa, zan zama matar Fa’iz in na bari tsofaffin nan suka shafa min lalle. Na yi tunani iyaka tunani bani da mafita, bani da mai mara min baya, babu mai duban hujjata da idanun basira in dai a kan Fa’izu Abubakar ne. Wani yaro cikin ‘ya’ya da jikoki da suke matukar so duk da tarin aibobinsa. Don haka na yakewa kaina mafita ta karshe.
Na janyo (travelling bag) dina na shiga shirya kayana da ba za suyi min wahalar dauka ba a gurguje.
Adda Hanne kanwar Maman Kaduna da tawagarsu suka yane labule suka shigo da guda da sallama, duk suka cika dakin taf! Tsokanar duniya babu irin wacce basu yi min ba, in gadon dakin ya daga ido ya dube su to nima hakan. Kaya nake ninkewa daga sif ina dannawa a jaka.
Adda Hannatu ta yi kwafa ta ce, “Ke ‘yar tawaye, mun zo kama ki ne kinyi kamar baki ganmu ba saboda kin isa”.
A yayin da ta bincire hancin kwalbar turare “intimately beckham” suna ta raha suna darawa cike da unexpressable nishadi da farin ciki bayyananne a zuciyar su da fuskokinsu.
Na dago jajayen kumburarrun idanuna na yi musu wani kallo a kaikace ta kasa-kasan ido a hankali na ce, “Ku kama uwarku dai”. A yayin da na sunto dankwalin kaina na yi damara a kugu gashina dake daure cikin (bound) ya sunce gaba daya ya cika fuskata da wuyana baki daya, ban damu ba, ban kula ba, jikina har tsuma yake ina jiran mai kwarin kashin da za ta fara matsowa gare ni.
Adda Hannatu ta ce, “Eye! Dambe za ki yi damu Fa’izah! Lallai da aka ce kin haukace ashe ba ayi kuskure ba. To bismillah ma ga mai kwarin kashi tsakanin ni da ke”.
Zaneerah cikin zafin cewa da na yi su kama uwarsu ta ce, “Eh, uwarmu zamu kama mana, tunda dai babban Yaya uba ne kamar yadda matar babban Yaya ta zama UWA...... wadda za ta cika mana gida da ‘ya’ya ta sauke tukunya ta dora mana abinci...... ta sa mana kula ta sabe mana babbar riga ta yiwa ‘ya’yanmu tarbiyyah irin ta gidanmu ba irin tata ta rashin neman albarkar iyaye da son gamawa da duniya lafiya ba.......”
Daga haka suka shiga kwararo min turaruka ta ko’ina gaba da bayana har tsakar kaina zuwa yatsan kafata, har kuma cikin idanuna.
Ashe dama kowaccensu da guzurin abinta cikin mayafi, ba Adda Hanne kadai ba. Azabar turare cikin kwayar idona ta rudani ta gigita ni na soma kara ina murza idanun da dukkan hannuwana, ina fadin “Idona.... idona..... wayyo Hajjah sun fasa min ido”.
In sun fasa to ke da baki nan kin fasa karatun nan, sai dariyarsu suke. Kasa na sulale na kwanta ina birgima ina murzar ido dake neman tsiyayewa.
Sai da suka kusa karar da kwalabensu kana na sha duka kitif-kitif-kitif daga hannun kowaccensu, wai ban yi wanka da kwalliyar tarbarsu ba sai zagin da na yi musu guzuri da shi.
Kai wannan rana na ga wulakancin duniya da takaici da bakin ciki wanda ke kokarin fin karfin juriya da karfin halin da nake tinkaho da su. Nake amfani dasu ko yaya ne wajen ganin na kwato hakkina daga iyaye da dangina na A.B baki daya.
Sai da idanuna suka lafa daga zugin da suke yi min na kuma tabbatar da basu tsiyaye din ba kamar yadda nake tsammani. Na shiga toilet dinmu wanda dama like yake da dakin barcinmu na wanko fuska da ruwan famfo mai sanyi, tuni zuwa lokacin an kece da kidan kwarya mai dadin amo da dadin sauraro.
Wanda sautinsa ke amsa kuwwa cikin kwakwalwata yana zabalbalar min da ita. Ji nake shine amo mafi rashin dadin sauti da na taba ji a rayuwata tunda uwata ta haife ni.
Mawakiyar waka take yi cikin lasifika tana kiran sunana tana hadawa da na Fa’izu Abubakar-Hafizin Hajjah, angon Fa’izah sanyin idaniyar Hajiya Hadiza Giwa..... Kin isar, kuma kin cika, baki taba gazawa ba uwar zuri’ar Abubakar Bamalli.... Allah ya ja kwananki ya kara miki lafiya ki ci gaba da kulle tsintsiyar Abubakar Bamalli. Takawarki lafiya uwar maza uwar Muntari, uwar Na’ibi uwa ga Ahmadu, uwar Ibrahim, Sani, Salisu da Sadi. Ki bani mota ki kaini Makkah Hajjah Giwar mata, Giwar mutanen Giwa.....
Da gudu na fito daga bandakin ba don komi ba sai don tagarsa tana tsakar gidan dai-dai inda tsohuwar ke zaune tana wakar mai kama da banbadanci tana rawa daga zaune, saboda ba ta iya mikewa saboda kibar da ta yi mata katutu.
Sai na ji kamar tana amfani da wakar tata ne da karin (tune) ko kuwa (melody) mai gaya min cikin tsakiyar kaina cewa, abin da Hajjah ta yi dai-dai ta yi, ina so ko bana so kuma ba zan taba yin nasara a kan A.B ba, sune suka riga suka yi a kaina.
Wannan tunanin kamar anyi min wata irin allura mai kashe lakar jikin dan Adam ta karar da kuzarinsa, ta raba shi da BURIN sa da duk wani buri da ya ciwa rayuwarsa.
Hawaye na malala ta kowacce mabubbuga ta idanuna yana kwarara a kan fuskata na tube kayan jikina dake kamshi na fita hankali ma zan ce ba na tashin hankali ba na canza wasu. Sai da na saurara na tabbatar su Adda Hanne da iyalanta su Zaneera da ‘yan kanzaginsu sun shige gidan Baba Na’ibi dukkaninsu don su kama Ummi, na sulale ta gareji ina jan trolley dina wadda ban cika da kayan da za su wahalar dani ba na bi ta baskwata inda babu ‘yan biki, mazan kuma duk basa nan, na bi ta hanyar da suke bi zuwa masallaci na fice daga gidan. Maigadin yana can yana baiwa tantabaru abinci.
Tafiya nake bana ko waiwaye da wata irin sassarfa mai hade da gudu-gudu kamar zan tashi sama, bana ko ganin abin da yake gabana, ban kuma damu ba wai don mota ko babur sun buge ni ba, gara su buge nin in mutun in huta da nufin A.B a kaina.
Don dai ba zan iya kashe kaina bane tunda na san abin da zan tarar idan na aikata hakan, babu mai kamasho ciki da za a raba bana mutuwar kafirici tare ni kadai zan dauki dakon abuna. Amma shiga ta duniya ba ni kadai zai yiwa illa ba, zai yi laga-laga ne da zuciyar duk wani da ya kwana ya tashi cikin zuri’ar Abubakar Bamalli, su rasa kwanciyar hankali da nutsuwarsu irin wanda na rasa tunda kowannensu cikin farin ciki yake da yankan kauna da kisan mummuken da suka yi mini, ni kadai ce cikin halin kaka-nikayi.
Nema na su rasa alhalin sun san ba mutuwa na yi ba shine kadai kokari na karshe da zan iya, tunda kalmar fatar bakina da duk wani bore na ya gaza, abin dariya ne ma abin a zauna ayi ta dariya. Tunda su dai burin su ya cika, gara in mutu da su tausaya mani, su dubi al’amarina da zuciyar hankali da tunani.
Da wannan tunane-tunane da zancen zuci da tafiya a kan hanya da kan titi bayan horn da zagi iri-iri da ga motoci da babura na bude ido na ganni cikin tashar motar garin Giwa. Ni da kaina na tabbatarwa kaina bani da wurin zuwa cikin danginmu kaf din su a karbe ni, in ka dauke gidan Baban Kaduna.
Sai dai kuma ai abin da kunya da nauyi, gudun auren dansu nake yi da suka tsuguna suka haifa, kiyayyarsa ke neman kashe ni da raina. Kuma su zamo sune mafakata idan ina da kunya?
Bugu da kari wanda ake bata kashin domin sa ba zai wuce can din ba, tunda baya Giwa wanda na rantse da in ga azzalumar fuskarsa na gwammace in yi arba da (arm robbers) cikin talatainin dare zai fiye min alheri da kwanciyar hankali fiye da sake arba da Fa’iz a sabuwar duniya da nake rayuwa bayan ta kuruciya ta shude da shi a ciki da duk wani al’amarinsa da na sani.
Duk da na san babu jituwa ko kankanuwa tsakanin Hafizin Hajjah, Fa’izu Abubakar da iyayensa da suka haife shi, Baba Muntari da Maman Kaduna, wani sako na kololu zuciya da kwakwalwata ya tuna mini da cewa DA har gobe sunansa DA a zuciyar iyayensa, ko da kuwa Hitler ne mai daukan rayukan al’umma babu dalili.
Da wannan tunanin sai na fada motar garin Zaria, wadda za ta kai ni har ABU in har DA shine DA a zuciyar iyayensa komin muninsa ko munin halinsa da munin ayyukansa, to kar in nemi gidan Baban Kaduna gara in koma ga tawa uwar wadda bana baiwa muhimmanci cikin rayuwata da hujjata ta banza mai cewa, ita ma ba ta bani kulawar da Allah ya ce ta bani.
Na tabbata idan duk duniya ta taru ta ki ni ta juya min baya a lokacin da bani da kowa, bani da gata, uwar da ta haife ni ko ba za ta kulani ba, ba za ta kore ni ba. Wadda ta sunkuya ta kawo ni duniya Fa’izun ke kamo sunanta yana zagi a duk lokacin da ya so, a dalilin ta haife ni kuma bare ce ba ta hada jini da iyayensa ba.
Bayan wannan ba ta yi masa laifin komai ba. Babban abin da ke damuna a wannan duniyar hujjar Fa’iz ta aure na? Har ya iya bude baki ya furta hakan bai ji kunyar kowa nawa ba? Duk da ba a auren na gani ina so cikin zuri’armu shi ya furta kuma an ba shi saboda fifikon da yake da shi a zuciyar Hajjah! Ko da zan mutu, zan so kafin isowarta (mutuwar) in samu amsar wannan tambayar, mene ne dalilin Fa’iz na aure na? Tunda na amince an halicce shi ne da kiyayyata ya girma ya rayu cikinta, ya bar kasar Nigeria cikin rainonta (kiyayyar), ya kuma yi gammon abarsa ya tafi da ita Rasha, ya kare shekarun da ya yi baya gida cikin soyayya da Ummi..... da kiyayya gare ni.
Na ce, kyawun da na yi ne wanda a da bani da shi, da tsabtar da na yi a yanzu wadda yake goranta min bani da ita a baya, yake kyara da hantara da wulakanta ni a kanta, su suka sa ya zo yanzu ya ce zai aure nin.
Hajjah ta ce ba su bane, ta kuma kafa hujjar ta da cewa, tunda Fa’iz ya tafi har ya dawo tsayin shekarun nan ko hotona bai taba gani ba, balle ya ga canzawar da ni nake ikirari.
To mene ne? Mene ne hujjarsa? Yana nufin alkhairi gare ni? Yana yi min tanadin alkhairi? Yana nufina da alheri da wannan auren ko ko ya yi shi ne don karasa cimma mummunar manufarsa a kaina ta ganin ya raba ni da duk wani farin cikin rayuwata? Na wulakanta na tozarta na tagayyara a rayuwa? Ina ruwan Fa’iz da duniya ta da burinsa kawai ya raba ni da jin dadina dake cikinta?
Tunaninnikan da nake ta yi kenan suna ci gaba da soya min zuciya, fuskata jage-jage da hawaye, domin iyaka tsinkaye da dan tunanin da Allah ya hore mini sun kasa bani amsar tambayoyina ko da guda daya daga ciki, har mai tasin da nake ciki ya hau kan titi dodar ya kama hanyar Zaria.
Mu karasa a
A littafi na 3
Takorin ku ce.
Chapter 48 · 0% Book details