Sashe 22
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya zo”. Jikinta a sanyaye ta koma gadon ta kwanta tana fadin “Zan dan kwanta in samu bacci kafin kiran sallah, in sun dawo don Allah ki tashe ni”. Wai Zanirah ta dauka kwanciyar nan da ta yi ban san cikin damuwa take ba. Damuwar ce ta yi mata yawa ba ta so na gane shine dalilin da yasa ta zabi ta kwanta din a dalilin dauriya da juriyarta sun kare. Umh! Na fa soma tunanin akwai wani abu tsakanin Yaya Aliyu da Zanirah, kai to mene ne.... kai babu komi.... to mene ne ma zai shiga tsakanin nasu? Oh! Ni Fa’izah! Anya ba son Yaya Aliyu Zanirah take ba?????? “..... Ina kammala makaranta zan kawo mata mijin..... Ki rike Yaya Aliyu da kyau, ki yi mai rikon magnet..... Yaya Aliyu ba irin mazan da ake yiwa rikon sakaka bane..... He has all the qualities and all the attributes to be loved upon.... ina da kyakkyawan zaton cewa, muddin Yaya Aliyu ya zamo miji a gare ki babu ke babu ganin wulakancin namiji da ‘yan’uwa mata ke suffering.... Saboda Yaya Aliyu na daban ne.... domin Aliyu uwa ne, uba ne, aboki ne, dan’uwa ne.... miji ne abin so da duk wata diya amce za ta yiwa kanta burin samu...... Imagine Fa’izah, yadda za ka zauna da wani alhajin zuciyarka da tunaninka, ruhi da gangar jikinka duka suna ga kaunar wani can daban.... Na tuno kalaman Zanirah! Na tallabi kaina da hannayena biyu sakamakon wata irin kwankwatsa da yake yi min tamkar zai dare gida biyu. Ko da yake an ce az-zannu zambun, wato zato zunubi ne bai kamata in yi saurin gaskata hasashena ba, har sai na ga diary din Zanirah da take boyewa, sai na ga abin da ta rubuta dazu, sai na ga damuwarta ta shekara da shekaru wadda a kullum ke zane a fuskarta. Ko mene ne ni zan yi kokari in magance mata damuwarta in har ba soyayyar Yaya Aliyu bane, zan taimake ta insha Allah ta fita daga halin damuwar da take ciki. ...... Shigowar Walida ya katse tunanina. Ta ce, “Yaya Fa’izah, Yaya Aliyu ke kiranki yana cikin mota zai tafi”. Duk da ina jin nauyin Aliyu ba zan iya kasa yi mishi sallama ba. Na rufe kaina da mayafi na bishi. Yana zaune cikin mota duka kafafunshi suna waje, ya jingina da makarin kujerar idonshi a runtse. Har na karaso bai bude idon ba, sai da na kwankwasa gilashin kofar motar ya bude dukkan manyan idanunshi a kaina, sun kada sun yi jajir har sai da na ji gabana ya yanke ya fadi, ko amsar da na ba shi ne ya tayar da hankalinsa maimakon ya yi farin ciki? Kallon juna muka yi cikin ido na ‘yan sakanni, kafin mu saki ajiyar zuciya a tare. Cikin sassanyar murya ya ce, “Abin da kika fada cikin takarda Fa’izah haka yake ‘heart and soul!” Kunya ta rufe ni, na rufe ido da yatsuna goma ina dariya...... Ya ce, “Na gode, na gode kin ji Fa’izah. Ina fatan lokacin da na yanke ayi aurenmu bai zamo takura a gareki ba, wato watanni uku masu zuwa bayan kammala jarrabawar ku ta karshe?” na yi shiru. “Akwai babban dalilin da yasa na yanke wannan lokacin duk da bana so na takura ki, akwai dalilin da yasa na yi hakan”. Na kara yin shiru idona a kan kananan duwarwatsun da suka rufe harabar gidan, da gaske ne har zuciyata ban shirya aure yanzu ba. A ranar na cika shekara goma sha takwas. A ra’ayina in samu ko karamar Diploma ne in yi kafin aure. To amma bana iya yiwa Yaya Aliyu musu saboda matukar so da kaunar da nake masa, ina son shi fiye da tunanina, fiye da tunanin duk wani dan adam. Bana iya musa mishi duk abin da ya umarce ni, don ina da tabbacin ba zai yi umarnin da zai zama cutuwa a gare ni ba sai wanda zai amfane ni. Har sau tari na kan ga kamar son da nake wa Yaya Aliyu ya ninka, ya dame ya shanye wanda shi yake mini. Wani lokacin na kan yi tunanin muddin muka yi aure ba zan iya batawa Yaya Aliyu rai ba ko inyi masa ba dai-dai ba daidai da kwayar zarrah, ko da shi ya bata min abu kadan zai yi ya shafe laifin daga idanuna da zuciya, komin GIRMAN sa. To amma dole in ji dalilin gaggawar tunda an ce ba a son garaje cikin aure, don gaggawar daga shaidan ce. Kamar wadda za ta gudu? Na ce, “Shin Yaya Aliyu to saurin na mene ne haka?” Ya saita kwayar idanunshi cikin nawa cike da damuwa ya ce, “Saboda SONKI Fa’izah! Na kai na kawo a sonki da kaunarki da son ganin mun zamo abu guda, na mannu da fatar jikinki which is always hunting my dreams.....” Na rufe fuska cikin jin kunya. Na ce, “Yaya Aliyu ai ba inda za ni, kullum muna tare. Ina laifin bayan candy da shekara daya? Bani da tunanin kowanne da namiji a duniya sai kai Aliyu Haydar......” Sai bayan na fada na san abin da na fada. Juyawa na yi zan tafi, Aliyu ya riko gefen mayafina. Ban juyo ba don haka ban san halin da yanayinsa ke ciki ba, ya ce, “Idan haka ne barshi a yadda na ce Fa’izah, watanni uku masu zuwa”. “Saboda me Yaya Aliyu? Gaggawa daga shaidan ce”. “What target do you have for making it longer haka Fa’izah? Wata babbar matsala ke neman fatali da farin cikinmu”. Ban san sanda na juyo gaba daya ba, na ce, “Matsala? Wacce irin matsala ce Yaya Aliyu?” Idonshi cikin nawa sun kada sunyi jajir, muryarsa a dushe ya ce, “Kina nufin baki sani ba? To Hajjah ke son in auri ZANEERAH!” Ji nayi wani abu ya kwashe ni yuuuu! Zai maka da kasa, na yi kokarin kama hannun Yaya Aliyu dake jikin motar gam-gam na rike. Muryata na rawa harshena na sarkewa na ce, “ZA-ZA-ZANIRAH Yaya Aliyu? Haba! Biri ya yi kama da mutum....” Na durkushe a gabansa kaina cikin cinyoyina, kamar in yi yekuwa a zo a tallafi rayuwata. Shi kansa Yaya Aliyu ya yi nisa a tunani, bai tanka min ba. Kowanne sakar da yake yi cikin zuciyarshi daban da na dan uwanshi. Kafin wata juriya da imani su shigeni ciki da bai dina. Na dago a hankali idanuna taf da kwalla na ce, “Ka je Yaya Aliyu Allah ya kai ka lafiya”. Ya dago ni daga durkushen da nake muka fuskanci juna. Don karfin hali irin na Aliyu murmushi ya yi min, nima ban san sanda na mayar mai da lallausar murmushi ba. “Kada ki sa abin a ranki fa. Everything will be alright. Don Baban Giwa (Barau), Baba Sadi da Baba Ibrahim da Yaya Hauwa basa goyon bayan zancen sam”. Na yi shiru ban yi magana ba, a zuciyata cewa nake, “Ni da kai kuma Yaya Aliyu ai sai wani babban ikon Allah, wanda in haka ta faru na tabbata na yi asara wadda ba mayarwa”. Zuwa can na ce, “Wallahi ka je kawai Yaya Aliyu, ni ba zan damu ba”. “How sure are you ba zaki damu ba.....” Na ba shi amsa muryata na gab da barkewa da kuka. “I am sure!” Ya gyada kai. Ya sanya hannu cikin aljihun motarshi ya dauko daurin kudi ‘yan naira dari biyu sardauna sabbi kar ya miko min. Na bata fuska gab nake da rushewa da kuka, don ji nake kamar sallamar karshe muke yi ni da Yaya Aliyu, kamar babban shinge na shirin shiga tsakaninmu, kamar wata sabuwar rayuwa zamu bude wadda dukkaninmu bamu taba tsammaninta ba. “Kada ki min musu, ki karba kawai. Ban da yau na taba dauko naira tsurarta na baki?” Na mika hannu biyu na karba. “Yaya Aliyu na gode, Allah ya kara budi”. Ya yi murmushi a cikin kallona ya yi min alama da hannunsa in tafi. Har na juya na soma tafiya ya ce, “Au! Fa’izah!” Na juyo hawaye shimfide a fuskata wasu na korar wasu. “Kika ce ba za ki damu ba, to meye na kuka?” “Ni ba kuka nake ba hawaye ne”. Ya yi murmushi, “Hawaye?” Nima sai na yi dariya, ga hawayen fal a fuskata. “Su zuba kawai suke, kuka kuwa zuciya ke yin sa”. “Na yarda dake”. Ya miko hannu. “Wannan kyakkyawan hankicin na hannunki za ki bani mana?” Na girgiza kai na ce, “A’a!” Da mamaki Aliyu ya ce, “Dalili?” Na ce, “Wallahi haka nan kawai nake son hankicin bana son rabuwa da shi, ina son kamshin sa”. “Wa ya baki?” “A dakin su kawata Naja na ganshi a hostel dinsu cikin kayana, wallahi ban san na waye ba”. “Mu gani?” Na mika masa ya karanta rubutun (AHUBBIK (I love you!”) ‘WA ANA AIDHAN (me too)” Na mayar masa muryata na karkarwa. Ya miko min hankicin na juya da gudu na karasa cikin gida, ban san tsawon lokacin da ya diba kafin ya bar gidan ba. **** Ban tashi sanin fitinar so ba sai a wannan ranar. Ban yarda it is injurious ba sai a wannan ranar. Ban san cewa its unbearable pain ba sai a wannan ranar da na tabbatar zuciyata ba za ta samu abin da ta dade tana SON ba, wato Ali Na’ibi. A gaskiya so abu ne mai dadi in ya zo da matsala marar dadi. Kamar yadda Ya IM ya ce na (GIRMA YA FADI) “It’s so sweet, yet so painful”. Wai sai na kama jin haushin ‘yar’uwata Zanirah (kishi), a ganina duk ita ta yi saurin girman da ya gundiri Hajjah har ta yi tunanin aurar da ita, kuma ta rasa wanda za ta likawa duk gidan sai Aliyuna, Yaya Aliyu, Aliyu Haydar Na’ibi A.B Giwa. Daga ni har Zanirah, kowacce ta kasa barci sai juyi a kan gado. Da abin ya isheni kawai sai nasa kuka wiwi. Tunanin in na rasa Yaya Aliyu, idan ba Aliyu ne ya zamo mijina abokin rayuwata ba shin ya ya rayuwata za ta ci gaba da kasancewa? Ya Allah kada ka baiwa Hajjah ikon karfafa zumuncin akan wannan, ya Allah ka fidda Aliyu zuciyar Zanirah. Don na laluba na duba na hanga ko ina ban ga ta hanyar da zan iya cin kankanta in bar mata ba