Sashe 54
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kake yi min ne ya sanya baka barni da dabarar kaina...ba". Rabi ta fashe da kuka ta kama ni zata rungume ni, na ingijeta da karfi. "Kada ki kuma zuwa kusa dani, yau na tabbatar ba Fa'iz ne kadai mai kina da mahaifiyata ba har da ke Ya Rabi". Na soma ja da baya, Momi ta miko hannu. "Ji ni nan Fa'izah, ki daina fadin maganganun da kike fada, Rabi tayi abu ne akan rashin sani, Allah baya kama laifin da aka yi bisa rashin sani, kuma babu mai laifi sai ke, ko me Rabi ta ce min ke kika jawo min, ke ki ka shafa min kashin kajin da bani da yadda zanyi in goge shi cikin danginku. Baki kyauta min ba, kin sani cikin bala'in da ba zan iya fitar da kaina ba". Ta soma kuka, Ya Rabi ma kukan take da na durkusa na saki wata kururuwa dukkansu ficewa suka yi daga dakin da gudu. Fa'iz Mukhtar Abubakar Giwa, ya yi parking mota kirar 'Sienna' ta Baban Kaduna da ya tuko daga Kaduna zuwa Zaria. Ya fito sanye cikin wata shadda-shadda boyel-boyel ruwan madara kirar (filtex) kanshi babu hula, sakamakon hakan, tarin sumar kanshi ta bamallin usli wadda bai fiya tajeta ba sai dai kula da ita ta kwanta tayi linkif a kansa sai sheki take bakikkirin, murdaddiya kuma kamar yana (relaxing) dinta, kamar kuma haka take a halicce. Ya yi sallama a falon gidanmu inda ya tadda Momi da Ya Rabi na kuka da girmansu da komai. Da sauri Rabi ta ce. "Ka koma Fa'eez, Fa'eezah TA HAUKACE! Muddin kaje inda take a halin yanzu abin ba zai yi kyau ba. Duk ni na jawo da na fada mata rasuwar Dr. Nazir, ni Rabi'atu wa ya aike ni?" Fa'iz ya yi dan dawurwura da manyan idanunshi akansu. "Waye haka Nazir?" Ba kuma tare da ya tsaya jin amsarta ba ya murda kofar dakin Abdallah gaba dayanshi ya shiga gaba gadi ba tare da tunanin komai ba ko wata fargaba cikin ransa. Durkushe nake akan gwiwoyina na aza kaina bisa gadon Abdallah ina sharar kuka babu ji babu gani, fatana kawai adai-dai wannan lokacin nima mutuwar tayi min adalci ta zo ta dauke ni, ta sada ni da masoyina, muyi aurenmu a kiyama ya fiye min wannan rayuwar da bani da sauran masoya a duniya sai rundunar makiya da burinsu a duniya shi ne zubar hawayena da shigata cikin kaka-nikayi, wato iyaye da 'yan uwana na jini. Na dago ido shargab da hawaye, jajur kamar gauta, don naji alamar tsayuwar mutum a kofa, ya kuma jima cikin dakin ba tare da ya yi motsi ko magana ba. Ban tabbatar ba, amma wannan matashi mai jini a jika ya yi min kama da FA'IZ BAMALLI dana sani wasu shekaru masu yawa a baya. Fari sol, har da surkin jaja-jaja kamar Bahurghade, ingarman mutum dan asalin garinmu Giwa, kuma jika ga Hajja Da ga Baban Kaduna da mama Asma'u. "Yau ko ni ko kai tunda Dr. Nazir ya tafi kai din zaman me zaka yi a duniyar banda zaman ka ci gaba da kuntata mini?" Da na mika hannu ga bangaresn dama na sai naji ya fada kan kwalbar lemo (7up) da Walida ta kawo mini na gama sha dazu,, na riketa katamau ina kallonshi kallon kura taga nama, kallon tsintsu daga sama gasasshe. Ya soma daga min hannu yana fadin cikin lumana. "Ki saurare ni tukunna... (just once) Fa'izah, kada ki aikata abinda zai sa kizo kina da kin sani. Na roke ki, ki saurari kalaman fatar bakina tukunna, daga nan na yarje miki ki zartar da duk hukuncin da ya yi miki....". "Ko uban da ya haifeka ban sauraron shi balle kai, kai da duk wani dan A.B ma kwansu da kwarkwatar su indai akan na karbi aurenka ne". Na daga kwalbar nan na wulwula na faskara mashi a goshi, ya yi saurin sunkuyawa ta wuce ta saman kanshi ta daki tsakiyar kansa. Kan kace meye wannan jini ya wanke shi tun daga tsakar kansa, goshinsa har zuwa wuyansa, amma don rashin zuciya zance ko bakin naci Fa'iz bai fasa dosoni ba, sake dosoni yake yana fadin. "Ashe da gasken kin haukace? Fa'izah (are you lunatic?)" Ya warware hannu ya shimfida min mari. Wani irin marin da ya tafi da ji da ganina na wucin gadi, na kuma ga gilmawar taurari goma. Amma bakina bai mutu ba. "Muddin ka iso gareni sai dai wani ba kai ba, baka ba da saki amma idan ka tafi inda Nazir ya tafi na saku ko babu takaba, iyakaci nima a kasheni. Na gwammace mutuwar da zama da kai wai a matsayin miji sau dubu gara mujiya da kai Fa'izu Mukhtar Abubakar Bamalli Giwa". Wani irin karfi da ban zata ba ya shigeni, na isa ga madubin dogon yaro dake like jikin bango wanda Abdallah yasa kusoshi shida ya kafa a dakinsa na soma kokarin banbaro shi daga jikin bangon, ban damu da yankewar da tsokar hannuna ke yi da gilashin ba har na samu nayi nasarar raba shi da kusoshin da suka tokare shi suka zame masa garkuwa daga fadowa kasa. Fa'izu Abubakar, ya tabbatar tsandara mishi mudubin nan zanyi, wanda hakan na nufin tsattsagewar jikinshim ta ko ina, alhalin ba karfinsa nafi ba, don haka yayi amfani da wani irin zafin nama wurin isowa gareni, ya kama mudibin ya yi mishi fisga daya ya wancakalar dashi a gefe ya kwankwatse, na sake doka tsalle don isa ga fashasshen gilashin in samo wani bangare daga jikinsa, ya isheni farkewa jikan Hajja ciki babu nadama, na jini baki daya cikin murdaddun damatsan Fa'iz Giwa, ya rungume ni gaba daya katamau cikin faffadan kirjinsa. Ban san sanda na tsala ihu ba. Wani irin ihu shi ba na karaya ba, shi ba na razana ba, haka shi ba na mika wuya ba. Ni kawai ban san na mene ne ba, ko mene ne ma'anarsa. Saboda wasu abubuwa ne naji cikin jikina masu kama da jan wutar lantarki (shocking) tun daga tsakar kaina har (toes) wato babban dan yatsan kafata shocking din azaba ne ake yi min irin wanda kiyayya ke haifarwa. Gam-gam Fa'iz ya rike ni. "Fa'iza saki dai kike so daga gare ni ko?" Zuciyata na bugu tashi na lugude, cikin masifa da bala'in da ba zai kwatantu ba na ce. "Indai kai dan halak ne cikin uwarka da ubanka... to ce ne an sake ki Fa'izah!". Fa 'iz yayi shiru yana gwama numfashi, kafin da ya tattara dukkan karfinshi yayi watsi dani gefe guda. Yana girgiza kai ya ce. "In aka yi hakan za'a zauna lafiya?" Cikin gyada kai mai nuna tabbatarwa. "Har da kwanciyar hankali, za'a zauna cikin A.B family gaba daya, (no more crisis... no confrontations...)". Murmushi yayi, wani murmushin da na kasa fassara ma'anarshi ko abinda yake nufi, ya ce. "Kin san ba'a saki cikin tashin hankali, ko cikin fushi, in aka yi hakan sakin bai saku ba. (Words and promises made in anger are like fire... you cannot reverse the damage they have done). Don haka share hawayenki, kije kiyi wanka ki fito kiyi sallar la'asar, ki kawo min biro da takarda. Shi kenan Fa'izah?" Haba! Ai ban san sanda na mike nayi toilet ba na sunce na sakarwa kaina shaya, sai a wannan lokacin ne radadi da zugi daga goshi da tsakar ka ya isowa Fa'iz. Ya kai hannu tsakiyar kanshi ya fitar inda yaga yadda jininshi ke ambaliya. Ya murda kofar dakin da sauri ya fito falo inda Momi da Ya Rabi ke zaune jigum-jigum. Momi ta mike tayi salati, ta tsarkake Ubangiji, tayi masa tasbihi, ta kadaita shi. Ta ci gaba da fadin. "Ba lafiyarta kalau ba, kuzo ku fitar min da ita daga cikin gida, ku kaita (psychiatric) kada tayi mana lahani cikin dare". Fa'iz ya samu kujera ya zube juwa da hajijiya suna kwasarsa. Ya yi murmushi. "Momi da hankalinta fa, bacin rai ne. Kuma tana da gaskiya da babu wanda ya tsaya ya kalla, amma shi kenan komai yazo karshe ai". Yaya Rabi ta cire dankwalin kanta ta daure mai goshin, ta sa mayafinta tana share mishi jinin wuyanshi da keyarsa, yayin da Momi ta dauko akwatin taimakon farko (first aid box) da yake ma'aikaciyar jinya ce, ta gyara wurin, ta cire kwalbar da ta nitse a wajen, ta dinke inda ke bukatar dinki duka idanun Fa'iz na lumshe har ta gama. Ta goge duk wani jini da auduga da ruwan (hydrogyn) tas. Ya mike tsaye sanda ya jiyo murda kofa daga (toilet) alamar na gama wankan na fito, yana ce da Momi ta kai min wasu kayan in sanya. Momi tana girgiza kai ta ce, "Wanda ke neman kashe mutum za'a kaiwa kaya ya sanya? Ni kam bana kai kaina mahalaka ina ji ina gani ba, kai dai kace kaji ka gani, bari in dauko maka ka kai da kanka, sai ince ga su". Ta shiga dakinta ta dauko doguwar rigarta da dankwali na shadda ta kawo masa, ya amsa ya murda kofar Abdallah ya shiga. Na takure can kuryar kuskurwar dakin ina mai kallon ceiling da zani kawai daure iya kirjina. Yau sati biyu kenan rabona da wanka, don haka ji nake ta ko ina wata iska mai dadi tana ratsani. Tsami da tashin da jikina ke ta yi kwana da kwanaki duk na samu saukinsa. Gashin kaina da na jika jagab da ruwa ya taimaka wurin suturta fatar bayana, ya kwanta lamban akan dogon wuyana ya sauka a kafaduna. Bai yi magana ba ya mika min rigar na amsa. Fa'iz ya kalleni na 'yan sakanni, ya ce. "Ina takardar?" Na mike na nufi littattafan Abdallah kan (study-table) dinsa na yago takarda harda daurawa akan littafi, na dauko biro. Ya zauna gefen gadon ya karbi littafin, ashe ma yana da nashi biron a gaban aljihun rigarshi kyakkyawa dashi (biron) ya dora akan takarda ya soma rubutu. Na koma jikin bango na tsaya hannuwana biyu sarke a kirjina ina kallonshi kasa-kasa. Ya ce a hankali, "Nawa kike ganin ya kamata in rubuta?" Na dan fiddo ido, da sauri kuma na ce. "Uku mana!". Har sai da na bashi dariya, ya yi murmushi, ni kuma na sake hade rai. Sai ya mai da fuskarsa ya kintsa ta. "Har uku, kina ganin