Sashe 39
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
**** Ranar da muka kare zana jarrabawar zangon karshe na aji uku (300 level), ranar muka yi shirin tafiya Giwa, a dalilin dan uban aiken da Hajja da Baban ABU suka ishemu da shi lallai mu zo gida ana neman mu. Mun yi sallama da Aunty Rabi da alkawarin ita da kanta za ta rako iyayen Nazir Giwa a duk lokacin da suka bukaci hakan, domin Aunty Rabi ta tsinke da irin kaunar dake tsakanina da Dr. N, duk da binciken da Yaya Mufty ya yi ya nuna cewa Dr. Naziru Sani Galadanci yana layin samarin da iyaye ke tsoron ya dora mayaudaran idanunshi bisa ‘ya’yansu a fadin garin Kano da jami’ar Bayero. To an ce fadan da ya fi karfinka sai ka mai da shi wasa. Don haka dukkaninsu suka koma lallabani da bina da siyasa. Ashe abin da ban sani ba a nufin Hajjah karatun daga iya nan an barshi kenan mu da Kano sai zuwa da yawo babu wanda ya gaya mini. Na ga dai Ummi cikin damuwa, da zamu tafi kuwa sanda Yaya Mufty ya kunna mota kuka take yi wiwi har da sharbe, ni kuwa sai na ji gabana ya yi wani irin mummunan faduwa a sa’ilin da Yaya Mufty ya hau kan titi. Kaduna muka fara isa. A sa’ilin da Yaya Mufty ya sanya hancin motar cikin gate din gidan Baban Kaduna, a sa’ilin ne na ji wani irin faduwar gaba da ban taba ji ba a rayuwata. Muka yi sallama a babban falo, duka ‘ya’yan Hajjah in ka dauke Rabi auta dake Kano babu wanda babu a falon. Suna zaune duk sunyi jigum-jigum. Da na juya ido zuwa mahaifina Ahmadu A.B sai na ganshi cikin jan ido kamar gauta. Babu abin da ya zo raina face mutuwa ga tsohuwa Hajjah. Idanuna suka yi kwalkwal na dubi Maman Kaduna cikin hawaye. “Hajjah ta mutu ko Mama?” Na rushe da kuka bana ji bana gani, kuka mai tsananin gigitar da zuciya ma’abociyar imani. Wata irin tsawa Baban ABU ya daka mini, “Ke bama son sakarcin banza. In mutuwar ta yi abin da za ki yi mata kenan? Sakayyar da za ki yi mata kenan zubar hawaye?” Baba Barau ya ce, “Ita Hajjah din za ta so ta mutu Fa’izah ba ta rungume ‘ya’yanku ke da Ummi ba tunda ta rungume na Zanirah?” Sai ga mai kuka na dariya bayan ga hawaye shabe-shabe a fuskar “Zanirah ta haihu Mama?” Gaba daya na basu dariya ban da Baban ABU. Na ce, “Amma Mama shine baku gayawa Aunty Rabi ba mun zo mun ga danmu?” Mama ta ce, “Mace ce, ai abin bana yau bane. Ita Rabi ta sani lokacin kuna jarrabawa shi yasa ta ce ba za ta gaya muku ba murna da doki za su hanaku karatu in kun zo kwa gani, to kin ji. Yau shekarar (FA’IZA) daya tana gudunta ko ina”. Na yi shiru cikin tunani, wato sunana Yaya Aliyu ya sanyawa diyarsa da Zanirah. Na ce cikin murmushi, “Allah ya raya takwara, zuwa Lagos ya kama mu kenan”. Ni sai a lokacin idona ya kai ga huhunan goro da alawa dake jingine gefe guda wani a kan wani. Na ce, “A’a, wannan kuma fa? Auren Maryam za ayi ko Hanifa?” Baban Kaduna da Baban ABU suka kau da kai kamar basu ji ni ba. Baba Ibrahim ne ya ce, “Auren Ummi ne ya tashi gobe insha Allahu, don haka makaranta ta kare babu sauran komawa Kano”. Ummi ta zare ido cikin firgici da kaduwa. Ni kuwa sai na rungumeta ina murna ina fadin “Don Allah Mama waye angon?” Mama ta ce, “Da masoyinta mana mai sonta tun tana karama”. Babu wanda zuciyata ta kawo min sai FA’EEZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA!” Ban san sanda na ce, “Amma a rasa wanda za a bawa Ummi sai Fa’iz?” Sai bayan na fada ne na tuna cewa, UWA da UBAN da suka tsugunna suka haifi Fa’iz ne a gabana. Suna zaune ne idanuwansu cike da kauna, kuma suna son dansu kwatankwacin yadda kowanne iyaye ke son dan da suka haifa duk munin shi ko munin halinshi. Ya yin da ni nake kokarin aibata musu shi a gabansu. A sanyaye na ce, “Allah ya sanya alkhairi”. Cikin sanyin jiki na wuce daki zuciyata cike da sake-sake. Wani bangaren tausayin Ummi nake ji. A ganina sun cuce ta sun aura mata mutumin da bai cancanci a hada auren shi alkhairi ba. Sai na tuna Ummi fa na son Fa’iz, kuma so hana ganin aibu. Yadda nake son Dr. N da tabban da yake da shi, haka Ummi ke son Fa’iz da kowanne tabo mai alaka da shi da halinsa. Iyayenmu suka bini da kallon nazari ganin yadda yanayi na ya sauya gaba daya a lokaci daya. Wajejen karfe hudu na yamma masu aikin gidan ke ta kaiwa da komowa sun kasa zaune sun kasa tsaye. Suna diban katon-katon na lemuka suna jerewa a firizan dake dakunan Baskwata (boys quaters) guda biyu dake like da juna. Na dan matsa na leka, ko falon dan ‘Prince Charles’ sai haka. Kwata-kwata falon bai yi kama da sauran falukan da na saba gani ba a wurare daban-daban. Komai na falon cream colour ne in ka dauke kayan kallo bakake samfurin SONY, hatta ‘curtains’ (labulaye) cream colour ne. Haka sauran kayan alatun dake falon. A.C har biyu, ta tsaye (standing A.C) da ta manne a bango (split), sai sassanyan kamshin (Bakhour) da Yahya ya sanya a dakin ke tashi. Kujerun (leather) ne suma cream colour masu laushi. Yadda wannan dakin yake, haka na kusa da shi yake komai da komai, sai bambancin kala. Na daya dakin ruwan makuba ne (grey). “Shin Yahya Baba amarya ya yi ne?” Sai ya kyalkyale da dariya, “Mama ce za ta bari Baba ya yi amarya?” “Yo ina na sani? Na san dai ba naku bane, duk da gasu a Baskwata”. Ya kara kyalkyala dariya, “Kin manta ne gobe su Yaya Bashir da Yaya Fa’eez za su dawo? Sai dai Bashir ya kammala, Fa’iz ma’aikaci ne ganin gida kawai zai zo”. Na ce, “Hummm! Lallai. Ni za ni in kwanta, anjima in su Baba za su koma Giwa kasa a tashe ni don Allah”. Ya ce, “Insha Allah”. Na juya zuwa cikin gida zuciyata cike da sake-sake. Da mamakin kaunar da Baban Kaduna yake yiwa ‘ya’yansa (beyond comment) sunan wani ganyen shayi. Abin haushin dukkansu babu na gari, don gara ma Bashir din shi shaye-shaye kawai yake. Shi dayan munin hali har ba a magana. Sai dai duk yadda na so in yi barcin Ummi ba ta barni ba. Hakika tana cikin farin ciki da ban taba ganinta cikin irin shi a duniya ba. Murnar auren ta da masoyinta Fa’iz Allah ya cika musu burinsu. Ta yi kukan dadi, ta yi na sosai. Duka dalilin daurin aurenta da Fa’iz gobe......” Na yi murmushi na ce, “Ki yiwa Allah ki barni in yi barci, ki bari ya dawo sai ku yi tare tunda karfe daya baya amo. Ki barni da abin da ya dame ni fargabar zuwan iyayen Dr. N, don ban san irin tarbar da Hajjah za ta yi musu ba”. Ta ce, “Matsalarki ce wannan”. Karfe bakwai na magariba muka bi Baban Giwa sai Giwa, Yaya Mufty ya wuce Kano. Tun daga gate din A.B Estate gaba daya komai ya canza, an sake fasalin ginin an mayar na zamani sosai, haka cikin gidan Hajjah an canza komai sabo dal kamar gidan amarya. An sake fenti gida kamar ba a cikin garin Giwa ba kamar a Lagos ko Abuja. Irin wannan sauyin na A.B Estate na faruwa ne a duk lokacin da A.B family za su yi wani gagarumin biki. Na ce, “Uhm! Ummi ana ji da aurenku tabbas”. Ta ce, “Fadi da babbar murya”. Abin da ya bani mamaki yadda su Inna Kubra, Indo da su Kaltume da sauran kannenmu na Giwa ke min oyoyo da (AMARYA).... Ka ga amaren sai kyallin goshi suke.... ni dai murmushi kurum nake ina cewa cikin raina “Auren Ummi guda ai dole a kiramu Amare, tunda mune Amara kirazan biki”. Idona bai hasko min kowa a falon ba sai Zanirah, rungume da buleliyar ‘yarta tana shayar da ita. Yaya Aliyu na gefenta yana waya. Habawa! Da Zanirah ta cizge ‘yar a nono ta dangware masa a cinya ta yi wani tsalle muka dire a tare muka makalkale juna bayan mun shararo a guje muka shiga juyi a tsakar falon Hajjah. Wai! TAKORI ta ce, TUNA BAYA SHINE RIKO! Yaya Aliyu ya mike rike da ‘yarsa ya hau Zanirah da fada..... “Wai ke baki da hankali ne? Kashe min ‘yar za ki yi? An girma ba a san an girma ba, kuna abu kamar kananan yara? Ko su Hanifa ba za suyi wannan shirmen da kuke yi ba....” Zanirah aka kwantar da kai aka shiga lallashin maigida... “Haba Baban Fa’izah! Shekaru uku currr! Ni, Fa’iza da Ummi???” Yaya Aliyu ya yi murmushi yana ci gaba da jijjiga Fa’izar don ta koma barcinta da hayagagar mu ya katse mata, don shi dama fadan shi baya nisa. Ya koma ya zauna ya ce, “Fa’izah ya karatu? Shi kenan an kare ko?” Muka dubi juna ni da Zanirah da Ummi duka muka yi murmushi. Na mika mishi hannu ya bani diyata kuma takwarata Fa’izah. Na dauke ta na sumbace ta na kura mata ido. Allah kareem dani yarinyar take kama sosai, ko da yake dukkanmu kamar tamu daya ce. Na ce, “Ya Allah ka raya mana little Fa’izah”. Kowa ya yi murmushi ya ce, “Ameen”. Yaya Aliyu kallona kawai yake, na san ba zai wuce mamakin kyakkyawan girman da na yi ba. Na samu Yaya Aliyu a kofar gida kan fararen kujerun roba yana yiwa ‘yar shi wasa, na labarta mishi zuwan dangin manemin aurena Dr. Nazir gobe. Yaya Aliyu ya yi shiru yana mai nazarin zancena. Akwai wani yanayi a tare da shi ya kada min ‘ya’yan hanji, wani yanayi da na kasa fassarawa. Yanayi ne mai nufin “BA ZAI TABA YIWUWA BA!” Na yi zugum! Ina dubansa hannuwa a kumatu zuciya cike da taraddadi. Ya yi ta maza in ji mata ya ce, “Fa’izah kin yi babban kuskure da kika saka soyayyar Dr. Nazir a ranki, alhalin kina sane da cewa babu auren