Sashe 94
Zumuntar Kenan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*** Mintuna masu dama suka shude kafin Fa'iz, yayi magana. 'It's not my fault' (Ba laifina bane). Akan me zanyi irin wannan mummunan 'joking' gareki har ma da IYAYENMU? 'I missed my flight', karfe goma na safe zan tashi nayi zaton na safe ne shi yasa na gayawa Walida da yaya Bashir zan taso goma na safe. A daren ranar kuma na kwana akan 'internet' ina gudanar da wasu muhimman ayyukana. Koko ince rai bata tafiya a lokacin da Ubangijinta bai kirata ba. Abu in aka ce miki da karar kwana to babu dabara. Idan kuwa rai bai zo wa'adinsa ba, ruwa da iska, mutum da aljan basu isa suyi ajalinsa ba balle abin hawa. Wani irin bacci ne mai tsananin nauyi ya kwasheni bayan nayi sallar Asuba da yake ma banyi bacci ba sai da na bada faralin Asubahi gudun kada in kwanta ya wuce ni, dana idar na ce bari in dan kishingida zuwa takwas na safe in shiga wanka in wuce Airport. Wallahi shi kenan, nayi ta baccin da ban tashi farkawa ba sai karfe goma sha daya na rana. Don haka da na tashi banji dadi ba, don na riga na fadawa Walida da Yaya Bashir na sake yin 'booking' na samu na goma na dare. Ina zuci-zucin in kira Shu’aib in gaya masa canjin da aka samu abokina Jeved yayi min waya matarshi Barya na labour in taimaka mishi inje in tsaya dasu a asibiti shi yana bisa aiki a Lusaka. Sai hakan ya janye min hankali na tafi garesu aka ce sai dai ayi mata 'CS’ ba zata iya haihuwa da kanta ba. Don haka ina wajensu har karfe takwas na dare. So ina komawa gida bayan an ciro mata yaron shi kuma Javed ya dawo, wanka kawai nayi na wuce 'Airport' karfe goma na dare muka taso zuwa Asuba muna Abuja, ban samu jirgi ba aka ce sai sha biyun rana kuma ban tsaya kiran Yaya Bashir ba kawai na biyo wani wanda muka sauka tare wanda shima Kaduna zai zo akazo daukarshi filin jirgin saman Abuja. Lokacin da na iso Maigadi ya ce duk gidan suna asibiti, lokacin ne na kira Shu'aib yazo ya sameni. Da ya ganni sai ya rungume ya fashe da kukan da ban san dalilinsa ba. Shima Malam Amadu (maigadi) kuka ya saka yana fadin. "Alhamdulillahi". A lokacin ne suke gaya min sunyi zaton ina cikin jirgin da ya fadi wanda dalilin hakan Yaya Bashir yayi hatsari, Hajjah ta samu paralysed, ke kuma kinyi dogon suma tun daren jiya har zuwa lokacin baki farfado ba, kina gadon asibiti. Muka garzayo muka taho. Na ganki cikin wani hali daya bani mamaki wai a dalilina kika shige shi. Ina tantama har yanzu... Ina shakkah... I still doubt! Fa'izah tabbatar mini, kin fadi ne don baki so na mutu......kin fadi ne don kina son mu rayu tare ko akasin haka? Am I not dreaming..?.". Hannu na kai na rufe mishi baki, 'before I start kissing him passionately'. Fatana ya yarda ni ce... ya yarda nayi nadama... Nadama irin wadda Ubangiji Yayi alkawarin karbarta. Na tuba nabi Allah na bishi... Na tuba na bi umarnin Allah! 'He is the one I love today and always... Burina Allah Ya barmu tare har zuwa karshen rayuwar mu. Mu rayu tare idan wa'adi yazo mu cika tare. Ina rokon Allah Ya cika min wannan buri... Yasa na rayu tare da FA'IZ rayuwa mai tsaho da nagarta... Sauran al'amuran da suka biyo baya (unexpressable) ne. Wata sabuwar duniya ce kuma wata rayuwa ta daban da biro ba zai iya bayyanawa ba. Wadda daga ni har shi bamu taba tsintar kanmu a ciki ba sai 'kintace' wato (Imaginations) tun lokacin da muka fara kamuwa da son junanmu. Muke kissimata cikin mafarki da ido biyu, muke kintacen ta da 'how deep it will be, how passionate, and how romantic! It's indeed the pleasurable one, EVER! Cikin wannan duniyar ne wadda bata kintatuwa 'no matter how efficient the description of a WRITER' wato duk kwarewar mai rubutu baki iya rubuta ta ba, muka kwashe awanni biyu, ban gaji ba, bai gaji ba, ZUCIYA da GANGAR JIKI kadai ke aiki a tare. Har sai da suka samu 'healing' na ciwon da ya kassara su, yayi 'overwhelming' Abubakar shekara da shekaru, ya kayar da Fa'izatu watanni uku. Ubangiji da Ya halicce mu, Shi kadai Yasan adadinsa a zuciyoyinmu. Dr. Alkasim Bello, kwararren likita a A&E na asibitin da muke, ya kwankwasa kofar Nurse na biye dashi. Bai shigo ba sai da Fa'iz ya yi mishi izinin shigowa. Amma hakan bai sa ya rabani da barin jikinsa ba. Murmushi Dr. Alkasim ya yi, "Darling didn't die, Fa'izah will not die...". Maganarshi ta bamu dariya dukkanmu. Yayi rubutu a (file) dina ya rufe ya dubi Fa'iz fuska fal fara'a. "Kana iya daukar amarya ku tafi Mr. Fa'iz, She's o.k, is a normal shock. Allah Ya kara dankon kauna". Babu kowa a (reception) din cikin 'yan gidanmu tabbacin duk sun tafi gida. Mukullin motar Baba yana hannunsa, don haka shi ke janmu zuwa Malali. Tafiya sosai mikakkiya, don asibitin yana unguwar Rimi ne. Ina gefensa yana tukin cikin sukuni da kwarewa. Na lalace a kallonsa tamkar wani furen fulawa don kyau. Ubangijin da ya halicce shi ya suranta shi, ya kyautata halittarsa da haiba da kamala. Idan na dube shi kallo daya kaga nitsatstsen mumini mai kiyaye iyakokin Ubangijinsa. Wanda kuma ya dama, ya kutsa cikin ilmin zamani mai tsada da daraja. A goshinsa tabon Sujjadah ne, ya taru yayi baki sidik cikin nuna babu ranar Allah da zata fito ta fadi bai russuna ga Ubangijinsa ba, Ma'abocin wata iri tsafta bayyananniya da ko cikin faratansa ya nuna. Komai nashi garai-garai kuma tsaf-tsaf kamar a lashe. Babu abinda nake yi cikin zuciyata sai tasbihi ga Ubangiji na da Ya mallaka min wannan ‘giant-handsome’ a matsayin miji a gareni mai so na da kaunata ba. Idan bance nafi sauran mata sa'a ba to hakika ina cikin sahun masu sa'ar ta kowanne bangare a rayuwa. Sautin Sheikh Mahmoud Khaleel Al-khusairi ke tashi a rediyon motar cikin Suratul-Ankabut. Watakila jikinsa ne ya bashi kallonsa nake yi kamar zan cinyeshi, ya juyo a gicciye ya saci kallona. Murmushi yayi, wanda ya fadada shi har fararen hakoransa suka fito. "Da yanzu wata na nan da lullubi aka, ta fara takaba". Na galla masa harara wadda ta fito ne hakikatan daga zuciyata, na dauke kai na mayar gefen titi. "Na matsu mu isa gida, (am running at a speedly level) amma motar bata sauri. Na matsu inji dalilin da yasa makiyinka yake kokomawa mutuwarka, har ya sume dominta". Juyowa nayi na kalleshi na 'yan sakanni, na sake maida kaina a titi cikin jin zafin maganganunsa. Na sadda kaina kasa, sai hawaye suka fito, suna diga akan tafukana. Sanyin na'urar motar yayi min yawa domin har raba ke naso daga kofofin A.Cn. Ga sanyin da jikina yayi da kalamansa, suka hadu suka haifar min da zazzabi-zazzabi, na soma jin kaina a sama, ban bari mun hada ido ba, don bana so yaga hawayena. Ya karya kan motar ya shiga layinmu, wannan karon yana tafiya ne cikin (slow-motion). Tamkar baya so mu karasa gidan. "I'm hungry, yaya za'ayi kenan? Gashi nayi alkawarin bazan sake cewa ki dafe min wani abu ba, 'above all' kema din baki da cikakkiyar lafiya, kin jigata kin wujijjiga da mutuwar maigida ba zaki iya girkin ba ko na janye alkawarin nawa. ‘I still wonder’ dalilinki na damuwa da mutuwata maimakon kiyi farin ciki na baki duniyar ki sha sharafinki...". Wannan karon ma shiru nayi, banyi magana ba, hawayen ne dai suka ninka na baya. "Insha sharafina, ko in shiga uku na?" Zancen zuci nake, ban san cewa ya subuto fili ya shiga kunnensa ba. Yi yayi kamar bai ji ni ba, ko da gasken ne bai ji ni ba bazan iya sani ba. Domin cewa yayi. "Kina jina? Na ce don mene kika damu da mutuwa ta?" Har tsakar kaina naji shock, cikin kwanyar kaina naji kunya, wata irin kunya da ban taba jin irinta a rayuwata ba. Wadda ta haifar min da dabarbarcewa. Ya sake maimaita tambayarsa. Wannan karon, tambayar tasa tana dauke da 'intonation' na ba da umarni kuma da gaske amsata yake bida, ko rai ya baci. CIkin karkarwar murya da in-ina na ce. "Uhm... uhm abincin yana... yana gida, na riga na dafa... ba sai ka sayo ba!". Dariya yayi mai hade da kallo daga can kasan ido. "Shi kluma cefanen fa?" Nima sai abin ya bani dariya, ganin ya saki daga daure fuskar da yayi. "Tambayar da nayi miki daban take da amsar da kika bani Fa'eezah!. 'Anyway' jikina ya bani kinyi kewana, idanuwanki sun nuna, kwayar idonki ta fada, kazalika kasusuwan da suka yiwa cikakken wuyanki ado, suka kuma maida dara-daran idanunki lungu. Don haka ne na zamo 'curious' wajen son jin dalili? Dalilin da ya sumar dake don NA MUTU! Alhalin sanin kowa ne mutum yana murna ne da mutuwar makiyinshi...". Na katse shi cikin kosawa, "Indai cefane ne ai Shu'aib ya kawo, Ya'u ya sanya su a (kitchen) da (store) da firinji, don Allah ka rabu dani haka!". Sai hawaye. Dai-dai sanda ya sanya hancin motar cikin gate din gidanmu. Buzu ya bude bakin shi yaki rufuwa don murnar isowar Ubangidan shi lafiya. Ya sanya motar a ma'adanarta, ya kashe fitilunta amma ita motar bai kasheta ba. Na murda mabudin motar don in fita, ko motsi ya ki yi. Na juyo a hankali na dube shi, da idanun bidar dalili. Har yanzun murmushi yake, ya ce. "Cefanen? Guda nawa ne?" Na ce cikin kauda kai, "To bude min kofar mana tukunna muje ciki kaga yawan cefanen da idanunka?" [26/02 8:44 AM] Sumayya Takori: Rausayar da kai yayi, a cikin kallona, ya lumshe idanunsa ya bude. "Yaya akayi kika sauya haka? 'What a sudden and awkward change! I need an explanation if you want to go out". Idanuna suka wani irin lumshe da kansu, na debo karfin zuciya na bude su tangararau akanshi. "Allah Ya hana bincike, kaga Allah Yaya Fa'iz yunwa nake ji... ka bude min kofa". "Allah Ya hana bincike, amma ke kika yi?" Na fiddo ido na ce, "Binciken me nayi maka?" Murmushi yayi (again), "Za ki