Sashe 90
Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
kike buqata, tunda nazo gidan nan sau daya Ahmad ya taba zuwa bai kuma wara dawowa ba sai dai ya turo min kudi ta account dina, haba Umma yaushe kike tunanin zai so inda nake? Wallahi ni ba zan tsaya jira ba. . .� Ta juya a sukwane za ta bar falon. Hajiya Zakiya ta daga murya, “Asma tsaya ki Jl�. . ~ � Asma tajata tsaya itakuma tacigabada fadar,“Kiyi haquri kidaina kukannan indai kina son mijinki na amince ki koma amma ki dan daga komawar taki k0 gyaran jiki ne in kaiki in kuma sake miki kayan bangarenki gabadaya yadda zuciyarki za ta sassauta, ni ba na son ganin kina damun kanki nima sai inji hankalina ya tashi�. � Asma tagirgiza kai,“Wallahi Umma bazan iya tsayawaba saidai duk abinda zakimin ki iskeni da shi daga baya, amma gidana zan koma ni ma ko na haihu na ga gudan jinina don na gama shan kwayoyin planning har abada.. Batajira abinda Umman tata zatacebata fice a guje ta bar falon bata tsaya a ko’ina ba sai cikin mota ta tayi mata key taja ta bar harabar gidan. � Saudat na tsaye a harabar gidanta tana manne da Khalifa a kafadarta duk da kuwa kibar da yaron ya mulka tamkar dan turawa ga shi jajawur da shi kamar « ya hada iri da zabaya. Rakiya cd sukayi wa Dr wanda zai tafi kaduna taron .bude wani sabon kamfaninsa. Saudat na ta zuba masa shagwabar ya tafi da su shi kuwa sai dariya yake mata yana zolayarta wai ba inda zaitafi daita saitayi kiba don Khalifama yafita nauyi, in ya yi wani zillon har kusa kayar da ita yake shi ya sa kullum yana hannun mai rainonsa. ~ Saudat ta ce Allah YallaBai gorinka ya fara isa ta hakanan, kodon kaganka kai yaddakazama wani dankareran katone? Allah ka kai kilo dubu ni Wallahi ma kana kwarata�. _ Dr. Ahmad ya kece dawata irin dariya jin Sharri irinna Saudat Ahaka kuma masu gadi sukabude get motar Asma ta danno cikin gidan dukkansu sukabi motar da kallo, Dr. ya gane ta don ga sunanta nan Baro-baro a saman lambar motar Asma ta faka motar: ta bude ta fito cikin matuqar sanyin jikinta ta nufo inda ~ suke. Kallo daya Saudat tayimata taganeta, k0 kadan 'zuciyarta babu alamar fargaba k0 firgici don kuwa a yanzu tana jinta daidai da kowace kalar mace duk matsayinta k0 iliminta, kuma a yanzu ba ta bakin cikin Asma tadawo su zauna dondama batun yanxu take wa Dr maganar dawo da Asma yana cewa zai dawo da ita,ba amma sai ta yi hankali. Asma na qaraso ta rusuna ta gaishe da Dr wanda mamaki ya kashe shi, wai yau shi ne Asma ke gaidawa, lallai ruwa ya daki babban zakara, ta juya kan � Saudat ta mika mata hannu tana fadar, “Saudat bani dana inganshi�.saudat tamiqa matashi,ammayaro da iya shege yaqi zuwa sai ma ya sa kuka. Dr, yace shi yana fadar, “Kai Khalifa kuka za ka yi wa Antyn taka, ba ka kyauta ba�. Saudat ta juya tana fadar, “Ako ni nayi ciki Aunty Asma ki tafi da shi tunda Kuka zai miki Asma ta yi murmushi cike .da jin dadin karramawar Saudat a gare ta, ta ce“Ai k0 godiya nake Maman Khalifa, kyautar surbudeden 'da kamar Khalifa, aiko nayi da kanaji fa�. Murmushi ya yi tare da fadar “Kema inda vaki sa duniya a gabanki ba Asma da yanzu kin ajiye uku irinsu�. Asma ta langwaBar da kai kafin ta ce, “Ka yi haquri don Allah Ahmad, wallahi duk sharrin zuciya ne, insha Allahu hakan ba zai Kara faruwa ba, don Allah ka yafe min�. Dr. Ahmad ya kade kafada tare da cewa, “Allah yace na yafe miki Asma, ni dai har abada bazan taba sakinkiba don ina sonki, ba zan iya rabuwa da ké ba�. � Zuciyar Asma ta cika da farin ciki ta dafa kafadarsa ta sumbaci Khalifa a kumatu tana fadar, “Na gode kwarai my dear". Al’amarin rayuwa ya sauya, Asma da Saudat sun samu fahintar juna, Asma ta cire duk wani girman kai ta taya Saudat tattalin maigidan nasu, a yanzu haka Saudat ta kammala diplomarta ta ci gaba da digiri cikin kwanciyar hankali, inda ta Kara haihuwar ‘yarta mace akasa mata sunan Asma. Tammat bi hamdu lillahi,
Saikuma mun sake haduwa a wani sabon littafin Thanks all my friends
Pls my fan's prayer for me Allah ya cikamin burinada kuma Allah ya cika muku burikanku na Alkairi Ameeeeeen *BISSALAM*
Saikuma mun sake haduwa a wani sabon littafin Thanks all my friends
Pls my fan's prayer for me Allah ya cikamin burinada kuma Allah ya cika muku burikanku na Alkairi Ameeeeeen *BISSALAM*