← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 90

Sashe 36

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

1page is missing Gaban Ahmad ya yi wata mummunar faduwa cikin sanyin jiki yace, “Lafiya kuwa me ke damun kine? Tamkar ba zata tanka masa ba saboda yanda kukan yake. neman Kin tsayawa, sai da ya sake� maimaita mata tambayar, sannan ta samu ta tsaida , kukan cikin shakakkiyar muryar da ta gaji da kukan Tace “YallaBai me yasa rayuwa take zuwa da abubuwa marasa dadine irin haka? YallaBai me yasa rayuwata kullum ba na ganin haske sai duhu a cikinta? Me yasa rayuwa ta kullum take neman rugujewa ne saboda wahala?� YallaBai shin ..... � Kuka ya ci Karfinta ta kifa kanta a kan cinyarta ta ci gaba da raira abin ta. Wani irin tausayin ta ya mamaye zuciyar Dr. Ahmad, ya durqusa gabanta a hankali har tana jiyo kamshin turaren da ke fatar shi. Muryarsa a sanyaye ya kira sunanta ‘Saudat Wanda ya sa ta dago kanta da sauri don bata taBa zaton ya san sunan ta ba, kuma yau ne karo na farko da ya taBa kiran sunan nata. Ya ci gaba da magana, ‘Saudat k0 me rayuwa ta ' bada hakuri aka a karba, ki karBa' duk abin da rayuwa ta zo miki da shi ki rungume shi, sai ki ga Ubangiji ya taimake ki a duk inda ki ke, yawan kuka ba zai kare ki da komai ba sai ma ya haifar miki da . wani ciwon. Kalle ni Saudat.� Ya fada da siririyar » murya, ta dago da jajayen idanuwanta tana kallon , shi, ya mika lallausan hannun shi yana goge mata hawayen: “Ki daina zubar da hawayen ki irin haka, alhalin ba ki tanadi mai share miki shi ba.� Saude ta� yi saurin janye fuskarta cike da jin kunya da nauyi, ya dan razana tare da fadar “Oh am sorry Ya mike ya ciro hankicif daga cikin aljihunsa ya mika mata. Ta karba ta soma share hawayen ta gama ta miKa masa ya karBa ya mayar aljihu, sannan ya ce “Tashi mu je ciki, kin ci abinci kuwa?� Shiru ta yi don rabonta da abinci tun jiya don haka ba musu ta mike, suka nufi falon kai tsaye Suna shiga ta nemi gefen kafet ta zauna bai tanka ‘ba Ya wuce kai tsaye wurin firij din da ake aje kayan gwan'gwani ya bude ya ciro wani qaton cake tare da ~ lemo guda da fresh milk ta kwali, sai chips a wani Qaramin plate wanda ya ji dafaffen kwai da madara ' ga shi ya dauki sanyi. Ya nufo inda Saude take zaune ya ajiye mata a gabanta, sannan ya ja gefe ya zauna saman kafet din yana' fuskantarta, da hannu ya yi mata nuni da ta ci, ba musu ta sa hannu ta dauki milk din ta fasa, ta bade cake din ta rinqa hadawa tana ci. Cake din * ya yi mata wani masifar dadi don sai ta ce tunda take � ba ta taba cin abu mai dadinsa ba ita kanta ta yi mamakin wanda ta cinye, don chips din kasa cin shi ta yi don ba ta saba cin irin shi ba. Ta daga madarar ta shanye tas, don sai da ta ji babu wuri a cikinta, duk abin da take yana zaune yana kallonta tana gamawa ta mike da niyar tattara kayan, ya daga mata hannu. “Bar shi kawai za a tattara.� Kallon shi kawai ta yi sai dai ta gaza magana. Don haka shi ya katse shirun ta hanyar fadar, “Kije kawai ki huta', kin'ga kin sha kuka kada kan ki ya yi ciwo, kin ji?� ' Saude ta amsa da to a hankali, sannan ta juya zata tafi hartakai bakinkofa tajiyakira sunanta ta' waigo tana kallonsa. Tamkar wanda aka matse bakinsa aka ce dole sai ya fadi abin da yake son fada ~ ya ce, “Please kar ki sake yin kukan nan don Allah.� Saude ta daga masa kai alamar to, ya ce, “Kin yi alkawari?� Da kai kawai ta amsa masa, sannan ta . juya ta fice A yanzu mamaki yake ba ta ba ta taba tunanin yana da tausayi da jin Kai irin haka ba, ashe dama yana da kyawawan halaye irin haka ya Boye su, Allah Sarki, ko da yake ai rayuwarta abin tausayi ce ga duk wani mutum mai imani. _ ' . Ta zauna bakin gadonta ta janyo Wayarta miss � call biyar ta gani, ta san kuma duk aikin Hamid ne, � Allah Sarki soyayya. Ta ajiye wayar karkashin Kanta ta kwanta. Hirar ta da shi jiya cikin dare ta dawo mata tamkar yanzu ‘suka yin ta, ta yi wani ”murmushi tare da yin wani juyi . Da safe misalin Karfa takwas ta nufi Gangaren Dr Ahmad da mamakinta yau kwance ta same shi cikin falon Kasa, saman doguwar kujera da News paper a hannunsa yana dubawa, yana sanye da wando three quater wanda ya wuce gwiwarsa sai bakar singileti a jikinsa. Saude ta durkusa tare da � ”gaishe shi.� Ba tare da ya dago kansa daga karatun da yake ba ya amsa mata gaisuwar. Saude ta mike ta soma aikinta kamar yanda ta saba, sai da ta kammala tsaf sannan ta soma turare falon da turaren wuta, kamar wadda aka cewa dago kanki, karaf su kai ido hudu, ‘gaba daya idanuwansa da hankalinsaya tattara su a ‘kanta.~ � ’Saude ta ji ta yi wata masifaffiyar tsarguwa, cikin basarwa irin ta gogaggun maza ya� yi mata alamar kira dakansa, jikin Saude ya Kara yin sanyi ita dai ta fara tsorata da irin kallon da yake mata, ba yanda ta iya haka ta ajiye bonar din ta nufl : ' inda yake ta dan durkusa kusa kadan tare da fadar, _ “Ga ni� Yalla Bai.�. Idonsa na' kanta kamar mai san karantar wani abu cikin idanuwanta ya ce“Ya kamata a tsaya da aikin nan haka a kawo mana abun karyawa k0 ke ba ki soma jin yunwa ba ne?� Yadda ya yi maganar cikin "salon nuna tausayinsa a kanta shi ya ba ta mamaki Saudat ta sunkuyar da kanta qasa� tana kallon yatsun hannunta, sannan ta amsa, da to muryarta a sanyaye, bai tanka. mata ba har ta mike ta fice daga falon, ya koma ya kwanta ya dora hannun shi guda a kan shi ya lumshe idanuwansa komai yake tunani? Oho. Saude ta karBo break din ta kawo da sallamarta ta ajiye masa. tiren kayan abincin a gabansa tare da fadar, ‘Ga abincin. � Dr. Ahmad ya yunkura ya tashi zaune ya sauko daga kan kujerar ya zauna a gabanta tare da harde qafafuwa tamkar wani karamin yaro ya ce, “Zubo mana. � Saude ta yi saurin kallonsa tana san tambayarsa shi da wa amma kwarjinsa ya hana, don haka ta sunkuyar da kanta. Ta dauko ' plate biyu za ta zuba Dr. ya sa hannu ya janye dayan yana fadar, ‘Plate guda za ki zuba mana.� Ba ta musa ba ta dauki saving spoon ta , debo soyayyar agada (Plaintain) tare da alalar nama da kwai sai soyayyar da nama cikin dankali ta zuba su kowane gefe da gefe a tsakiyat plate dim sai ta zuba wata hadaddiyar miya kadan sannan ta tura plate din a gabansa ta rufe kulolin, sannan ta dauki kofi guda biyu ta zuba kunun madara da gero tasa ‘cokula ta miqa masa. Dr. Ahmad ya zuba mata manyan idanuWansa da dan murmushi a fuskarsa ya ce, “Sannu.� Ba ta amsa ba saboda yanda ta ji nauyin yanda ya mata sannun, kamar ba yallaBan da ta sani ba. . Da kan shi ya matso da plate din a gabanta shi ma ya matso tare da miqa mata kofl guda na kunun Gaban Saude ya yi wata mummunar faduwa ta yi saurin matsawa tana girgiza masa kai alamar a’a. Dr. ya hade fuska tare da fadar. “Karbi mana meye haka?� Yanda ya yi maganar cikin tsawa ya sa ta saurin mika hannu ta karBa. Ya ce “To sa hannu mu ci maza.� Ta yi saurin kallonsa idonta 'ya ciko da kwalla ta gaza yin magana, Dr. Ahmad ya girgiza kai cikin damuwa ya ce “Abincin ne ba zaki ci ba shi ne za ki yi kuka?� Ta yi saurin girgiza masa kai,alamar a� a Ya kada kai cike da damuwa ya mike ya koma kan kujera ya kwanta ya lumshe idanuwansa ba tare daya yi magana ba. ~ Wani irin abu yayi wa Saude tSaye a zuciya, shin wai ita me ya maida ta ne? Yanzu abincin ma da zai ci sai ya wahalar da rayuwarta a kansa, abin da yake mata ya soma ba ta tsoro. Ji take tamkar ta mike ta bar masa falon, in ya ci ma k0 bai ci ba ruwansa. Bude idanuwansa da' ya yi shi ya katse mata tunanin take cikin sanyayyar muryarsa ya ce “Na takura ki k0? Ki yi hakuri kina iya tafiya kawai. � � Gaban Saude ya yi wata irin masifar .faduwa cikin muryar kuka ta ce“Ka yi haquri dan Allah � Ya dauke kansa kafinn ya ce “Aini banyi fushi ba.� � . . Damuwar da ta gani qarara a fuskarsa ne ta Narkar da zuciyarta, ita kanta tana mamakin kannta -. yanda hankalinta ke tashi idan suna tare bata san lokacin da bakinta ya bude ba sai dai ta ji tana � fadar “Ka yi hakuri yanzu ai zan ci.� A hankali ya dago yana kallonta, ta ta" sunkuyar da idanuwanta kasa, wani takaitaccen murmushi ya yi tare da saukowa daga kan kujerar ya: zauna gefenta. Da kan shi ya dauko kofi din kunun ya mika mata, ta sa hannu ta karBa cike da jin nauyi ta soma sha, dadin kunun ya ratsa mata kwanya ashe haka yake da dandano a baki, tun tanajin nauyi har ta dake ta ci sosai tana cire hannunta yana cire nasa.� a Ta dan zuba masa idanuwanta, ya daga mata gira, alamar ya aka yi? Shiru tayi “ta kwashe kayan ta dawo ta gyara wurin da sukaci abincin sannan ta qarasa inda yake zaune yanacikin karant jaridarsa, ta dan durkusa. _ “Zan tafi Yallabai ko akwai wani abin da~ ka ke so?� ' Dr. Ahmad ya dago da kansa ya kalle ta a nutse~ kafin ya ce, “Me yasa za.ki tafi nan ba falo ba ne? Me yasa
Chapter 36 · 0% Book details