← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 90

Sashe 34

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Wani sanyin dadi ya bugi zuciyar hamid lokacin da siririyar muryarta ta daki kunnensa muryar da har ya fiddah rai da sake jinta a duniya cikin doki dajin dadi yake magana Amin wa,alai kumussalam ya habibati saudat nasan zuwa yanxu saqona yaxo gareki hakane? Murmushin dake fuskarta ya qara qawatuwa kafin tace hakane yaya hamid dillaliya ta kawomin dazu ashe baka mance daniba yaya hamid? Hamid yace wat? Haba sudat ai idan har zan iya mancewa dake to wlh zan iya mancewa da kaina saudat soyayyata gareki ta gaskia ce kuma ta ginu ne tun daga lokacin dana fara ganinki kuma inhar ba daina numfashi nayi ba sudat bazan taba barinki ba sainaga kin taka wani matsayi a rayuwa na miki wannan alqawarin Cikin farin ciki dajin dadi saude tace na gode yaya hamid Yayi wani murmushi wanda har saida ta jiyo sautinsa yace gaskia saudat dina ta fara girma haka bakinki ya bude ? Murmushi kawai tayi bata tankaba hamid yace saudat nasha wahala lokacin dana dawo na iske bakyanan wlh saida nayi tamkar zan haukace kamin in samu insan inda aka kaiki amman bansan ko waccce anguwa bace ba a cikin abuja saida na biyo ta hannun wannan matar yanxu ya kike ganin za,ayi don muna cikin matsala fa Saudat an fada miki ansa ranar aurenki? Saude tace eh an fada mini Toya kike gani abuja zanzo in sameki ko ko ya za,ai ? Cikin kidima saude tace ina? Ka rufamin asiri masu gidan bazasu bariba Saidai kawai ka bari inna samu dama kawai na gudo Hamid yace to yaushe ?donni nanda sati daya jirginmu zai tashi zuwa qasa mai tsarki aikin hajji birina kafin satin duk yaddah za,ai ayi kawai a daura mana aure don wlh saudat ina tsoron in rasaki Saude taja‘numfashi kafin ta ce, “Insha Allahu Yaya Hamid duk yanda zan yi kafin satin zan yi ba za ka rasa ni ba da yardar Allah.� ' Dadi Ya kama Hamid nan ya ci gaba da jan ta da hira, su kan Su ba su san sun ci lokaci ba sai da suka jiyo ana kiran sallar Magariba.� Hamid ya ce “Lah! Saudat kin ga kin shagaltar dani mun ci lokaci har haka, bari in je in yi sallah zan kira ki zuwa dare kin ji sweaty na?� Dariya kawai ta yi shi kuma ya kashe wayar, wani sanyin dadi ya cika masa zuciya. Ta murgina ta sake mirginawa cike da shaukin soyayya kusan sai nace ban taba ganinta cikin irin wannan farin cikin ba � � “� Washe gari Saude na cikin shirin tafiya aikinta, ta ji karar wayarta, ta matsa inda ta Boye ta ta dauka ta kara a kunne tare da rairo sallama Hamid ya amsa tare da gaishe ta, ta amsa ba sai dai ta maido masa da gaisuwar ya amsa suka gaisa sosai, can ya nisa kafin ya ce“Kin san me wai ashe jiya yayanki yazo gidanku, ban sani ba sai daga baya na samu labari?� Cikin zakuwa Saude ta ce, ‘Kai don Allah Yaya hamid yanzu yana ina don Allah?� ~ Hamid ya ce“Nima abin da yasa na baro Kaduna ke nan cikin daren na zo Katsina, amma sai na samu wai matar gidanku ta sa mahaifinku ya yi masa korar kare, suka dinga watso masa kaya waje cikin daren ya bar Katsina, amma ya barma maqotanku saqo baki Saudat ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya ji take tamkar ta shake kanta saboda baqin ciki Hamid ya ce, “Ai kuma nifa ba wai na fada miki ba ne don ki tayar da hankalin ki ba, ki yi hakuri tunda ya dawo yanzu wata rana ma , zai sake dawowa, don wallahi tallahi na yarda da Kaunar da ke tsakanin ku na san in har yana da rayuwa ba zai mance da rayuwarki ba Saudat ki yi haquri don Allah kin ji?" Haka dai ya yi ta lallashinta sannan ya kashe wayarsa. Saudc ta qara fashewa da kuka mai cin zuciya dama she Yaya Rabi’u yana raye? Ashe ‘dama bai mance da niba? Shin kowace irin rayuwa yake yi a Lol labari dai nata tafiya cikin kwanciyar hankali kuma ta wani barin sai nake ganin kamar Dr Ahmad nason ya fada tarkon sofa idan ya fara son saude ya kuke ganin zata kaya tsakanin asmau da sauden hamid da saude da kuma garba gurgu da saude kai akwai rikici fa mu tara donjin ci gaban wannan qaya taccen labarin idan naga comment sosai zanci gaba anjima idan kuma kukaqi to sai gobe kenan naku har kullum Admin Dboy🤔 [1/25, 9:29 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [1/25, 10:39 AM] A A Dboy: *YAR TALLA*
Chapter 34 · 0% Book details