Sashe 69
Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
na. ma rasa a ' duniyar� da nake ranar maganar kuka ma babu ita, don idanuwana sun kekashe ga shi 'ba damar in tafi gidanmu don na san Umma ba ma saurarena za ta yi ba Abin Allah sai ga shi yana zuwa wurin Baba ya hau shi da fada har yana kumfar baki ya ce ba da yawunsa ba, bai amince da wannan auren ba. Bala ya yi juyin duniyar Baba ya haqi yaddah, a dole ya haqura don ba yaddai zai yi. Sai dai zamana da Bala babu abin da ya canza don sai ma ya dauki gaba da ni, yadda ki ka san ni .na hana auren k0 gaishe shi na yi ba ya amsawa, duk na bi na gigice na rame ga ciki ya fara girma amma rayuwa sai a hankali, ni da Rabi’u muna fuskantar quncin rayuwa. A haka har cikina yazo ya tsufa na haife Ki a wannan karon Ummana ta zo ita da Yaya * Sani, hakan ya tabbatar min da sun fara saukowa da ni. Ummana ta ba ni kyautar kaya niqi-niki, shi kuma Yaya Sani ya yi min kyautat kudi dubu biyar a nan ne na samu labarin ya samu Aiki a cikin birni a babban banki first bank har ya yi auransa a can na yi masa murna sosai. Sun dade sannan suka tafi, amma na lura sun dan fahinci halin da nake a ciki, domin Bala bai siya wa jaririya k0 hankici ba Babu kaya a jikinta cikin zanina na qudundune ta, data ce ina kayanta ‘nace Bala ya; tafi ya ’siyo yanzun nan. Ta hau fada haihuwa tun jiya amma ace ba a tanadi kayanda za a sawa yaro ba, babu k0 sabon dan goyo saboda sakarci? Ta Ciro riga guda cikin kayan da ta kawo min mai tsada ta saka wa jaririyar Ranar suna kuwa Saudat na sha kuka har na gode wa Allah, don Bala bai yanka rago ba abincin suna ma masara kawai ya bari tiya biyar ya kama gabansa, . har yamma babu labarinsa. Na ci kuka har na gode wa Allah don nasan abin gori ne a gari a ce ba a yanka wa yarinya rago ba. Haka na ciri dubu uku da dari biyar cikin kudin da Yaya Sani ya ba ni na bada aka siyo min madaidaicin dan taure aka yanka, sai a� lokacin mahaifin Bala yasan ba a yi yanka ba, ya yi fada har ya gode wa Allah ya Ciro kudi daga cikin aljihunsa ya bada aka siyo tikekiyar tunkiya aka hada aka yanka da yamman nan likis gab da magruba. Bala bai dawo gida ba sai qarfe sha dayan dare mahaifinsa ya yi masa tatas har � yace zai iya tsine masa a kaina. Shi dai hakuri _kawai ya ba da ya shigo gidan ya qare min tanadi da wulaqanci. . Da safe kuwa sai cewa ya yi abin yanka biyu ya yi min yawa ni da wa ban san yadda aka yi ba, ashe ya sabe tunkiyar ya fice da shi ya kai wa Laure. Ya barni da dan tauren Ke Saudat na ga bakin cikin rayuwa don a lokacin ji na yi tamkar in hadiyi zuciya in mutu k0 daidai da rana daya Bala bai taBa .. cewa a kawo ki ya ganki ha, inda na samu sauki ma mahaifinsa don ya nuna maki so kamar ya had‘iye ki, duk da kina' Jaririya amma » da ke yake zama a kofar gida sai idan kin yi ?fitsari ko kuka yace akawoki abaki kisha minti goma kuma zai sake aikowa a kawo ki * ga yayanki Rabi’u wanda zance tamkar shi aka * haifa mawa don da Baba ya aiko a“dauke ki zai biku idan za adawo dake tare dashi haka idan za a sake fita, wannan ne ya dan rage min � radadin da ke damuna. Ga shi Umma na min aike yanzu akai� akai tana aiko Zuwaira kanwata wadda a lokacin ta fara zama budurwa, shekararta goma tana aiko min ita da� yan abubuwan bukata k0 _ ‘yan kudi don a lokacin Umma tana samun "kudi sosai wurin Yaya Sani ya tsare musu .komai � . Kwatsam mahafin Bala Allah yamai rasuwa mutuwar‘da ta daga min hankali a lokacin kina da wata 'biyu, na ji mutuwar Baba fiye da~ yadda na ji ta mahaifina aka zo aka yi sadakar uku kowa ya watse. Ranar da aka yi arba’in Saudat, ~a washegari aka daura wa Bala aure da Laure, a . ranar‘kuma aka yi mata jere ta tare. Bani da labari sai dai na ga jama’a na ta shigowa ana jejjera kaya ban tambaya ba har suka gama suka tafi da daddare na ji gudar ‘yan kawo amarya a lokacin zuciyata ta tabbatar. min da abin da nake zargi na shige dakina na yi kuka ~ har na ji babu dadi, na share hawayena na ci gaba da hidimomina a cikin gidan Ummana da ta samu labari aiken kudi ta yi min masu yawa ta ce in ja jari in rinka sana’a saboda zama hakan ba zai min ba. Kin ji uwa mai dadi. � Yaya Sani kuma ya zo garin da kansa yasa aka yi min sabbin kayan daki masu kyau da tsada, wanda ko na amaryar ba zasu kama kafar nawa ba don da ma kin san ba a yi min kayan dakiba, dan uwa mai dadi Nan fa kishi ya Balle Laure da habaice� habaice har tana fadar, wai Yaya Sani sun� Samu labarin tsafi yake a birbi, kin jifa! Ba ka da damar da arziqi zai sameka yanzu ance yankan kaikake, nidaibankula ta ba hidima ta da yarana kawai nake Ga shi har a lokacin Bala bai damu da ni ba balle ‘ya’yana sai ma ta kai ta kawo ba ni da girki a cikin gidan, kullum ita ke sanwa, . kuma ita ke kwana da miji, suka bi suka hade min kai abincin da zan ci ma aka daina ba ni, da na yi wa Bala magana ya hau ni da fada wai bai riKe ni ba, idan ba zab iya ba ga hanya nan shi ba zai iya ba, ai yana da labarin idan an ba .ni abinci zubarwa nake wai ni mai dan uwa, mai kudi, to in zauna dan uwan yaci da ni. Haka ya qaraci Kankancinsa ya yi tafiyarsa. . Na shiga rudani ga ‘yan kudin da ke hannuna duk na cinyesu a ranar haka muka wuni, washegari ne da na ga yunwa na neman kashe mu a dole na mike na sabi ‘yata na goya na kamo Rabi’u na kullo dakina na leka ~ _nafada wa Laure zan je gida don Allah idan ‘Bala'ya dawo ta fada masa, na ba ta makullin dakin. , Ta amsa a daKile n muka tafi, ina tafe juwa tamkar za ta kayar dani DanivSaboda yunwa, ga Rabi’u na ta kukan zaici abinci duk da kuwa da girmansa don'. yana dan shekara takwas a lokacin Kai tsaye gidan Umma muka nufa a yanayinta ya tabbatar min da ta ji dadin zuwan namu,n2a kuma yardar wa kaina ta yafe min ' laifina a yanzu sai dai da alama tana min kallon tausayi. ' ' A gidan mun ci mun sha, kamar cikinmu zai Bule. Muka yi sa� a Umma ta gyara kaji guda shidda na zauna na soya mata su ta dibar mana kusan rabi da kwalayen lemuka masu "yawa da ledar kayan marmari, haka muka dawo gida niqi-niqi da naira dubu ta abin 'hawa. Muka dawo gida wajajen magriba ban 'samu kowa a tsakar gidan ba,� � na leqa dakin Laure na karBi makullina na bude muka shiga na ajiye niKi-niqin ledojin naje na dauro alwala na dawo nayi sallah sannan na zauna na baje kayan Ina cicciro wadanda zasu lalace. Da wuri Na ji an hankad'o labule na tsaya ina kallonsa, ya shigo dakin yana faman muzurai, na gayar da shi amma bai amsa ba, don haka ni 1 page is missing Ya runtse idonsa yana maimaita innalillahi Wa’inna ‘ilaihi raji’un, ya bude ,su _sun kada sun yi jajawur muryarsa na rawa ya � soma fadar, “Da ma an dade ana gaya min halinki amma ban taba yarda ba, sai yau da na ga zahiri ba zan ce miki komai ba Mariya ki je ke da Allah, ba zan ce miki komai ba�. Ya juya ya fice tamkar zai fafi a Kasa tunda na sadda kaina qas'a ban iya dagowa ba, zuciyata ce ke ta faman kai kawo tamkar za ta fasa kirjina ta fito fili, babu abin da nake maimaitawa sai innalillahi daga qarshe kuma sai na kife kaina a qasa na sa wani irin kuka mai ban tausayi. Rabi’u da ke .zaune kusa dani ya sa hannu ' “Mama ki tashi ki yi shiru . � Da dai ya ga ban da niyyar yin shirun shi ma sai ya kifa kansa a kaina yasa nasa kukan. , Tsawon lokaci muna a haka babu mai tada wani sai da'na gaji don kaina na ji kaina ya fara bugawa alamar ciwon kai ne zai sauko min, na lallaba na mike na kinkimi dana na dora kan gado, ni ma na kwanta a gefen Keko kina ta sharar baccinki muka rinka. sauke ajiyar � Zuciya a tare har bacci Barawo ya sure Rabi’u amma ni idona babu alamar bacci a cikinsa yadda naga rana haka na ga dare. � Washe gari haka na tashi jiki ba kuzari' zuciyata ta yi min masifar nauyi koba a auna ni ba ina da tabbacin jinina ya hau saboda yadda kaina ke wani irin masifar ciwo ga juwa ga nauyin kirji duk dai alamun mai hawan jini. Ga lamarin ba sauqi don sai‘na ce ma gara jiya da yau don bala’in na yau ya fi na jiya tashin hankalin yanzu ya linka na yau dan na fuskanci wulakanci da cin mutunci da muzanta � a lokacin nan don bar sai da na gwammace dama ba a halicce ni a duniya ba. : ~ Ga ciWo ya zoya tiso ni gaba kamar zan mutu daga ni sai dana Rabi’u muke jinyar, shi “ke yi min komai daidai da shiga kewaye sai na dafa shi, ya kai ni har bakin qofa, amma� Bala bai taba yi min