← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 90

Sashe 14

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ta, Laure ta ce, “Bakallona zakiba cewa zakiyi bazakiba kawai sai in san kin isa.� Saude ta juya ta wuce jikinta amace, saboda ita dai ba ta taba yin wanki ba, don kayanta ma kale daya ne, duk wani wankin gidan Rabi’u ne ke yinsa. To ta inn ma za ta fara? Ba ta da zabin da ya wuce ta dora sanwar sannan ta wuce bakin magudanar ruwa ta ci gaba da cuda kayan Sai da ta yi da gaske sannan ta samu ta gama aiyukanta saboda ciwon qirjinta da ya soma taso mata ga mararta da ta kulle da bayanta, ta kwanta tana faman numfarfashi. Rayuwa ta dawowa Saude sabuwa gaba daya, al’amura sun karasa damalmale mata, duk wata .wahala da dawainiyar gidan gaba daya ita ke yin ta, ga yawan tallar datake yanzu hartafi tada tayi ta safe, ta yi ta rana, ta yi ta dare. Duk ta bi ta Kara lalacewa ta fige ta zama tamkar kwarangwal, kazantar da take ciki har tafi ta da, ga alamun girma na zuwar mata, amma kullum rayuwana Kara dagulewa take tana Kara shiga cikin matsi da kunci. Kullum a wurinta jiya ta fi yau. Tun tafiyar Rabi’u bai sake dawowa ba, ba ta kuma Kara samun labarinsa ba. Lokaci ya yi ta tafiya kusan shekara biyu kenan da tafiyarsa kullum sai ta yi kukan rashinsa wanda ba ta da kamar sa. Sai dai ta yi ta share hawayenta ta kwanta ta yi barci, qunci da wahalhalun rayuwa sun yi mata yawa har wani lokacin ta rinqa jin gara mutuwa da irin rayuwar da take ciki. Musamman abubuwan da ‘Yar Baba ke mata ya na damunta, ko'dan ta ga ta fita girma ne duk da Saude a lokacin tana da shekara sha shida, ita kuma ‘Yar Baba na da shekara sha biyar, amma tafi Saude garin jiki, saboda ita irin girman jikin nanne da ita gab-gab mai irin manyan gaBoBin nan. Don ita Saude ‘yar siririya ce sosai, kamar a hure ta 'ta fadi, sai dai tsawo kamar an ja ta. Ita kuwa ‘Yar Baba gajeriya ce mai Kiba sosai tana da manyan mazaune da wadatar na shanu, ba laifi 'ita ma kyakkyawa ce tana da dogon hanci da manyan idanuwa sai dai qaton baki ne kawai ya kware ta mai cike da haqora kamar an watsa wake a miya. ‘Yar Baba har tafi mahaifiyarta wurin‘rashin mutunci da rashin tausayi ga gadara da ' rashin kunya da tsinannan surutu, kamar aku, ga shi' Inna Laure da Malam Bala sun dauki son duniya sun dora mata, duk wani abin da suka samu yana kanta. Shi yasa ‘Yar Baba ta tashi da kwalliya ‘yar gayu ce sosai, suttura komai tsadarta za ka ganta jikin ta, matsatstsu na fitar hankali, kuma ba laifi tana yin kyau matuka, amma idan ka kalli Saude to zaka iya cewa gara jiya da yau. Yanzu haka Saude tafe take rungume da bokitin alala, tana gab kawowa kofar gidansu ta hango wata qaramar mota Joker ta yi fakin mai bakin gilas, ta qurawa motar ido a lokacin da ta ga na cikin motar, dan iya saninta ba su da wasu ‘yan uwa masu 'mashin' ma balle mota Ta Kara gyara rungumar da ta yi wa bokitinta tana kallon motar, ta zo daf da ita ne ta ga an bude an fito. ‘Yar Baba ce da wani saurayi suka fito daga gidan baya na motar hannunta na riqe da irin manyan ledojin nan na shopping. Ba ta ankara ba ta ji ta rafka tuntuBe har takalmin da ke Kafarta ya tsinke dama sun sha duniya duk sun side ga su daban-daban, wato wari da wari, wani ya fi wani. Hakan yasa tasa reza ta ragewa babban tsawo, gaba daya takalman duk sun sha faci da Leda. Ta durkusa ta dauki takalminta ta wuce cikin gidan nasu tana gyarawa, duka suka raka ta da kallo, tana jin saurayin na fadar, ‘Wannan kuma wace ce?� ‘Yar Baba tabe fuska kafin ta ce “’Yar talla ce gidanmu take tana yi wa Baba ta talla. Wani abu ne?� Saurayin ya girgiza kai kafin ya ce “A’a, haka kawai amma dai gaskiya kazama ce, wallahi bakijiba data wuceni harzuciyata saida ta tashi. " Daidai nan Saude ta shige cikin gidan tana jin zuciyarta na mata wani irin kunci. Tana shiga cikin gidan ta ajiye bokitin tallarta, ta miqama Laure kudin cinikinta sannan ta dauki abincin dake ajiye bakin murhu babu k0 murfi sai kudaje ne ke bi yabe yaBe. Saude ta dauka ta nufi bakin qofar dakinsu ta zauna ta soma cin dumaman tuwon. ‘Yar Baba ta shigo niki~niki da ledoji Inna Laure da ke zaune gefen tabarma ta washe baki tana fadar. “Oyoyo! Ga ‘yata, taho nan zauna, zo zauna mu ga me aka farauto mana ‘Yar Baba ta cire takalmanta masu mugun tsini ta ajiye ledojin saman tabarmar, ta cire dan karamin mayafinta mai kamar matacin koko, saboda shara~ sharansa ta zauna, gaban rigar nan an yanke shi sosai, maman nan nata ya yo waje kadan ne kawai ke cikin rigar, Inna Laure na kallonta k0 a jikinta ita ta ledojin ma kawai take. Babu abin da ke cikin ledojin sai kayan makulashe kala- kala, su sweet, cingam, biskit, choculate da sauran tarkace, daya ledar kuma wasu hadaddun kayan shafawa ne irin na manyan mata. Bakin Laure ya Ki rufuwa‘ta dubi ,‘Yar Baba taha fadar, “Wannan kuma ina ki ka same shi ‘Yar Baba, dan wane ne a garin nan?� ‘Yar Babe ta tabe baki tana taunar cingam kafin tace, “Wallahi ban san k0 dan waye ba, nima jiya na hadu da shi na dawo daga makaranta.� Laure ta rafka guda kafin ta ce, “Da kyau ‘yata tauraruwa cikin taurari, mai farin jini, shi yasa. kullum nake Kara son ki dan anan dai haihuwa ta yi rana, Ki dai tsaya ki nutsu ki dage ki shake mana wuyan duk wanda ki Kikeso in ja shi in zaga birni in ratsa Kauye nasa ai masa daurin huhun goro ‘Yar Baba ta sa dariya tana fadar, “Kai shi yasa nake son ki Laure.� � Ta mike tsaye tana fadar, “Hmm! Gaskiya wani abu na ci min tuwo a Kwarya, gaskiya Laure yarinyar can tana zubar mini da aji a gaban samarina.� Laure ta zaro ido “Wace yarinyar?� ‘Yar Baba ta yamutsa fuska kafin ta ce, ‘Yo wace ce in ban da waccan Sauden banzar kullum tana cikin Kazanta wallahi da ta wuce ki har wani wari za kijitanayi. Agaskiya nibazan iyaba indaitaga ina zance ta koma ta samu dakali ta zauna sai na gama, wallahi take ake yi mana daukar matalauta.� Laure ta ce, “Ai waccan mai kama da igiyar shanyar ni kaina abun na damuna da ta tunkaro ki harwani Karni-Karni za ki ji tana yi ita k0 warin jikinta ba ta ji.� ‘Yar Baba ta ja tsaki ta wuce daki tana faman juya mazaune kamar mai rawar taBa-kaka. Wani irin abu ya yiwa Saude tsaye a zuciya, wai harsu sunada bakinda ’zasu kiratada kazama, alhalin sunfi kowa sanin kayanta a duniya kala uku ne sumana Laure ne data gaji da gurza tasakar mata, duk sun sha gamin baki. Daidai da man shafawa bata da shi a gidan, to balle sabulun wanka k0 na wanki, sai idan ita ce ta gaji da yawo da kazantar ta ta siyo omo na goma cikin kudin tallarta idan ta dawo tayi wanki tadiba aciki tayi wanka. Idan ba zata manta ba rabon da fatar jikinta ta ga man shafawa tun kayan kwalliyar da Yayanta ya siyo mata shekaru uku kenan da suka wuce da ‘yan kwanaki. Ta mayar da ‘yar kwallar da ta ciko mata ido ta ci gaba da cin tuwon da ta keji tamkar dutse saboda yanda yake mata tsaye a qahon zuciya. Da rana Saude tana zaune saman bencin cikin tasha ta tasa bokitin alalarta a gaba tana kallon jama’a na ta kai wa da kawowa, can ta hango Garba Gurgu yana nufowa inda take yana faman tsangala kafa da shanyayyan hannunsa guda can gaban qirjin shi a makale yana kadawa irin na wanda ya shanye Saude ta Kara hade fuska dan a duniya idan akwai wanda ta tsana, to bai wuce Garba Gurgu ba, ga shi dattijo dan a Kalla ya kai shekara sittin, ga shegen iyayi kamar wani qarami. Yaro Garba ya qaraso har inda Saude take zaune yana ' faman watso hakora kamar an zana ABCD. Saude ta daukc kanta ta ci gaba da kallon wani waje. Garba ya cangala ya zauna saman dutsen da ke gaban ta. “sannu da hutawa Hajiya Saude ya kasuwar?� Saude ta jiyo muryar nan kamar an kunna injin markade saboda girmanta, ta dago idanuwanta tana Lol i relly feel unhappy for rabiu [1/17, 7:54 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [1/19, 5:11 PM] I love my mum: *YAR TALLA*
Chapter 14 · 0% Book details