← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 90

Sashe 65

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

aka raba biyu ana kiwo a cikinsa, sai qaton iccen bedi a tsakiyar gidan mai malalan kasa don babu sumunti. ' Bala ya tura kyauren dakinsa ya juyo yana min alama da na shiga, kamar kar na shiga har sai da ya sake yi min magana sannan na daure na sa qafa na shiga cikin dakin, ba wani mai girma ba ne sosai, yana dauke da katifar maza wadda aka lullube da bargo sai dan karamin tebur wanda aka dora wata ‘yar qaramar talabijin da bidiyo a sama. Shi ke nan abin da ke dakin, sai ‘yar hanga ta katako wadda aka sargafe kaya sannan ‘kafet din da ya mamaye dakin, wanda ya ci uwar quta. Kin san abinki da samari bazaki taba tabbatar da tsabtar saurayiba saikinga dakinsa lol (gayu a. ganku a .titi kar a ganku a masaukinki Saudat in takaice miki haka na zauna dakin nan na gyara shi tas-tas kamar ba shi ba, washegari Bala ya fita kasuwa ya yi mana siye-siye, tun daga kayan abinci har zuwa na sawa irin wanda za mu bukata. Da kayan shafa wanka, turaren wuta, sabbin labulaye, karamar radiyo, Saudat haka Bala ya dawo da kaya niqi-niki don a lokacin yana samun kudi sosai saboda tun daga Dandagoro har zuwa cikin unguwarmu babu wanda ke saida kayan koli sai shi, don haka yake samun kudi sosai. Sannu a hankali lokaci ya shiga tafiya Saudat ina ganin , soyayya, qauna da kulawa fiye da yadda ba ki zato, hatta mahaifinsa idan ya tafi kasuwa ya dawo da kunShin nama na. A haka harna samu ciki, irin mai masifar laulayin nan kamar ba na kai ba, amma daga gidanmu babu wanda ya leko ya ga ya nake, da Bala ya je ma Yaya Sani wulakanci ya yi masa, don haka ya dawo gida cike da takaici, ya fada wa mahaifinsa shi ne shi kuma ya ba shi shawara da ya je ya dauko diyar Qanwar mahaifiyarsa Laure wadda aurenta ya mutu ta ke zaune gida: � ' Bala ya amince saboda jin jikin da � nake, ban iya yi wa kaina komai bane 'haka ya tafi ya dauko min Laure, aka gyara mata dayan dakin ta zauna. Laure ita ke kula dani, duk wata dawainiya tawa ita ke min, tana gefe tana kallonmu ni da mijina duk abin da nake so shi yakemin inamai � tabbatar miki babu abin da' zai hana a kawo� shi. � Idan kuwa na ce ina son abu jikinsa har rawa yake ya je ya samo min k0 a ina, da ya shigo ya rinka tambayar Laure ya nake, ya jikina da sauqi dai k0? Na ci abinci k0 ban ci � ba? Idantaceban cibaba hakazai zauna yatusa ni agabayana rarrashi kamar zaiyi kuka har ya sai ya samu na ci, haka mahaifinsa idan ya tafi kasuwa siyo min wannan kawo min wannan, ke na ga gata da soyayya. A haka Saudat ciki ya cika wata biyar na huta da laulayi a lokacin ne kuma naje gida ni da. Bala, amma Umma k0 kallonmu ba ta yi ba ita da Yaya Sani suka watsar da mu a makar gida sai Zuwira ce wadda ta fara taflya ta tattako ta maqalqale ni na rungume ta ina jin SOyayyarta a zuciyata donni a wautata� wai gani nake ita kadai ce ke sona, ba ta guje : niba, haka na qaraci zamana na tashi muka dawo � gida ba mu ma tsaya Baba ya zoba . � Wulakancin da aka yi mana ya yi wa Bala ciwo, haka ya yi ta maimaitawa ni dai Ina jinsa ban tanka ba, don idan da zai tona tawa .zuciyar na san da ya tabbatar tafi tasa hawa da jin zafi, ni a ganina k0 don kyau da sauyawar da na yi yasa Umma bata saurare muba don ta' tabbatar Bala yana sona sutturar kanta dana naje gidan tsadarta ta kau dubu goma a lokacin kuwa dubu goma ba nan ba ce, kayan ' dubu goma sai dai dan wane da wane, amma hakan bai sa Umma ta duba qokarinsa ba ni kaina ta san ai na canza don na yi dumurdumur da ni, haske na ya Kara. fitowa na zama kamar wata. baturiya saboda kyau, ba yadda muka iya dole nena share na manta, sai dai Bala � bai .mance ba don duk lokacin da na ce masa zan' je gida sai ya ce ban 'zuwa ba yadda zan yi . a haka nazo na haihu, babu wanda yazo ta Bangarena gidanmu, sai dai Babana daya zo har gida ya ga ' jariri ya yi masa addu‘a, ya bani ‘dubu biyu da niki niqin kaya sannan ya tafi, daga shikuwa k0 kare bai ce komai ba. � Sai dai Laure ceke dawainiya da ni ita ke dora min sanwar ruwan zafi safe da yamma ’ta kwashe ta kai min kewaye ta yi wa jariri wanka, ta yi girkin abinci a gaskiya a lokacin ta yi dawainiya kodayake ta saba da wahala tunda a can gidansu wankau ta ke na kudi da surfani. A kwana a tashi har na yaye Rabi� u, ban Kara zuwa gida ba, a ganina tunda sun Kini ni ma na manta da ~su kin ji wauta fa, ' haka rayuwa ta ci gaba da tafiya tamkar bani da � iyaye a garin, saboda Bala ya bar min Laure ita ke min komai na hidimar gidana iyakata ni dai inwanka nida dana mutafi wurin maigida. ~ , Ashe abindaban saniba Laure tana nan tana jin haushinmu kamar ya kashe ta ni k0 sakaran ban taBa sani ba, don ban yi zaton za ta iya jin haushinmu ba, saboda yadda nake ' � kyautata mata ni da maigidana. . Lokaci na tafiya ban sake haihuwa ba a tsawon shekara bakwai a lokacin ne kuma mahaifina ya rasu, to a nan ne na dan yi hankali na dauki dana muka tafi gidanmu na zauna a can har sai da aka yi sadakar uku duk yadda Ummana ke shasshare ni sai data tanka min duk da ba wata maganar arziki ba ce muka yi, anagama sadaka na tattara na koma gidana, to a nan fa labari ya sauya don ban sani ba ashe na bar baya da qura, haka kawai na ga Laure na min wani kallo-kallo, ga shi shi kuma uban gayyar ya hau shasshare ni da na yi masa magana sai ya hau ni da fad'a dana yi laifl da ban yi ba duk daya wai an yi wa tuwo Barin miya. Abin duniya duk ya dame ni ya ishe ni, ga shi ba ni da wanda zan fada wa matsala ta, a haka dai na yi ta hakuri ga shi a lokacin ban san na samu cikinki ba, sai da laulayi ya matsa min, amma Bala ko a jikinsa ya watsar da mu ba-ya kula mu ni da dana balle abin da ke cikina. Rayuwa duk ta dagule min, na zauna na zama wata kalar tausayi, kin san halin da mace ke shiga idan miji ya juya mata baya abin ba dadi, sai dai in qule daki in yi jugum. Ban� taBa mantawa da ran Wata laraba ba ina zaune a daki shiru ' Laure bata ,kawo mana abinci ba ga shi k0 abun karyawar � da ta yi mana da safe, ban samu cinsa ba nan na’bar wa Rabi’u ya yi ta wasada shi ’har wurin uku na rana babu abinci babu dalilinsa� A dole na takarqare na mike na fice shiga kicin din, sai dai abin da na gani sai da ya so tarwatsa min zuciya, na na tsaya turus ina kallon Laure wadda ta zabga uban goho ta takarkare tana ta faman barbada magani a kwanon miyar Bala, ban tanka mata ba har sai ' da ta gama barbade-barbadenta tas! Ta kawo cokali ta jujjuya miyar ta maida ta rufe, ta mike tana boye maganin a habar zaninta. Muka yi ido hudu, a take jikinta ya hau rawa � tana faman karkarwa can kuma ta ja tsaki ta rabA ta wuce ta barni tsaye da. mamaki a zuciya. ; Can na girgiza kai na dauki kwanon miyar na fito na zubar ’da ita, da ma miyar danyar kubewa ce na dawo na zauna da' kaina na takarkare na sake dora wata miyar' ta busasshiyar kucewa na yi na gama na debi * nawa na ajiye masa nasa da kyar na samu na ; tuttura abincin ama zuciyata tamkar za ta tarwatse. Bayan la’asar Bala ya dawo. daga kasuwa tun kafin in fito kuma ta riga ni fitowa ta tare shi ta shimfida masa tabarma jikinta na rawa ta tafi ta kawo masa abincinsa da ruwan randa masu sanyi cikin kwanon sha. A lokacin ni kuma na fito na tsaya daga bakin qofa ina kallon ikon Allah, Bala ya ja kwanon miya ke nan ya bude suka yi ido hudu da miyar busassiyar kubewa ya yi sa‘uriin dago kai yana kallon Laure. “Wannan miyar kuma fa? Ba ni na ba da danyar' kuBewa ba nace a kawo miki ba, k0 ba a kawo ba?� Laure ta karya kai cike da kisisima kafin tace, “To ai ‘yan ba ni na iya yau :su suka ' dauki miyar suka zubar suka shirya tasu ta musamman�. Bala ya yi saurin dago kai yana kallona. , “Ban gane kin zubar da miya ba, kan wane dalili?" Jikina ya yi matukar yin sanyi ganinyadda ya zaburo min na daure na durqusa � gabansa muryata a sanyaye :nace kayi Mai gida bari nayi ban sani ba Shi ya� sa na sake maka wata, amma ina neman wata alfarma a taimaka a maido girkin gidan nan wurina�. . . Bala ya zaburo, “Ke gafara can rufe min baki, ki dai ce wani mugun halin kika tsiro da shi, kuma wallahi ba zan dauka ba, ba ma zan laminta ba, tsabar almubazarannci kawai ki dauki abinci ki zubar saboda ba ke ke nemowa ba k0?� Zuciyata ta kara ganin yadda Bala ya hau ya ke ta zuga min masifa haka, idona ya kawo kwalla na mike cikin kuka ina fadar, “Allah ya ba ka hakuri Na juya na shige dakina na barsu. Ban san abin da suka kitSa ba, da zai fita ya . hankado labulen
Chapter 65 · 0% Book details