Sashe 44
Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dr Ahmad ya ajiye wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya ce “Ki je zan neme ki.� Saude ta share hawayenta ta mike a sanyaye tafi Dr. Ahmad ya bi ta da rinannun idanuwansa wanda sukai jawur. Saude tana shiga dakinta ta fada kan gadonta ta fashe da wani irin kuka mai sauti, ita kanta ba za ta iya misalta tashin hankalin da take ciki ba, zuciyarta na wurin Hamid ta san dole ya neme ta tunda ta sanar da shi yau za ta bar gidan, shin idan ya kira ta bai same ta ‘ba wane irin zargi zai mata? Kila ma ya rabu da ita. Wayyo ni Allah na! Ta Kara rushewa da wani sabon kukan. Yinin ranar haka ta yi shi babu wata walwala a tare da ita. . Da yamma liqis Dr. Ahmad ya aiko aka kira ta, don haka ta wanke fuska ta murza mai da hoda, duk wai don karya gane kukan data sha, sannan ta fice. Da sallamarta ta shiga falon nasa, yana zaune saman daya daga cikin kujerun falon, ya harde tamkar wani basaraken Balarabe, shigar ta manyan kayan ta yi masa masifar kyau ta Kara fitowa da cikar kamalarsa da kwarjininsa. Saude ta durqusa dan nesa da shi kadan kafin ta ce, ‘Sannu dahutawa YallaBai.� Dr. Ahmad ya dan zuba mata idanuWansa kafin yace, ‘Me ya samu idanuwan ki Saudat, kuka ki ka rinka yi tun tafiyar ki k0?" Da sauri ta girgiza masa kai alamar a, a ‘Hmmm! Saudat kenan me yaSa kike san boye mini damuwarki alhalin duk wani motsin ki sai zuciyata ta fassara mini shi Ya girgiza kai tare da fadar ‘Tashi mu je ki min rakiya cikin gari.� , _ Da hanzarinta ta yi saurin daga kai tana kallonsa Dr ya mike; tare da fadar kar ki ce komai biyo ni kawai. Saude ta mike. jikinta a sanyaye tana shirin fashewa da kuka yana kallonta bai kula taba ya yi gaba abin sa. � Saude ta bi shi tana matsar kwallarta ita dai so yake kawai ya jaza mata tashin hankalin da ba za ta iya dauka ba kawai. Suna fitowa harabar gidan ta samu masu tsaron lafiyarsa wadanda suke a lungu da sake na gidan sun nufo sa, wasu kuma sun nifi wurin motocinsa wadanda yake fita da su Dr. Ahmad ya daga masu hannu kawai ya nufi wata shareriyar Jeep mai qofa takwas fara mai bakin gilas, daya daga cikin masu gadin nasa ya take da gudu ya bude masa kofar baya ' Dr Ahmad ya juya yana kallon Saude wadda ke tanya tamkar� yar kaciya, ya yi mata nuni da hannu alamar ta shiga ta ji tamkar ya dora mata dukkanin tashin hankalin duniya ta ja ta tsaya cikin tsananin kidima Dr Ahmad ya dan matsa daf da ita muryarsa Kasa kasa ya ce ‘Za ki shiga k0 k0 sai na dauke ki na shiga dake da kaina?� . Ganin yanda ya matso ta ya tabbalar mata zai iya yin abin da ya fada din don haka ta janyo dauriyar duk duniyar nan ta dorawa kanta, ta taka a sanyaye ta � shiga motar, tana zama shi ma‘ya shigo aka maido masu kofar aka kulle Saude ta ji ta yi mutuwar zaune idan ta ce bata cikin tsananin rudu da kaduwa ta san ta yaudari kanta. Ta lumshe idanuwanta tana sauraren bugun zuciyarta ta san ita yau tata ta Kare ba abin da zai hana Asma na samun labari tasa bindiga ta. Harbeta Shiru babu wanda ya yi magana a cikinsu. Sai Dr. Ahmad neya dan mika hannun shi ya latsa gefen motar, sai ga wasu hadaddun labulaye sun zagaye motar , ya mika hannu ya bude na’ura mai KwaKwalwa (Computer) din da ke gabansa wadda ke jikin motar ya kunna, sannu a hankali ta kama tamkar talabijin din bango. Ya koma ya jingina ya ci gaba da latselatsensa ba tare da ya kalli inda take zaune ba, kowa da abin da yake sakawa a zuciyarsa. Ba ta san sun iso ba sai dai ta ji an bude masu qofar, Dr. ya rufe computer din ba tare da ya kalle ta ba ya ce ‘Fito mu je. � Bai tsaya ba ya sa kai ya fito don haka ita ma ta ziro qafafuwanta ta fito tana kallon harabar wurin da suka shigo. wurin gyaran jiki ne wanda ya amsa sunansa a cikin garin Abuja daga sama an yi rubum da manyan .. baki a jikin wani karfe ANNURI beauty QUEEN rubUTun ya bada hasken � Dr Ahmad ya yi gaba Saude na biye dashi har suka iso cikin masu take masa baya daya yayi saurin isa ya bude musu qatuwar kofar ta gilas tareda gaishe suka shiga qaton wurin mai kamar an gina shi da' zallan gilasai Da kyar Saude ke dosana kafarta� dan gudun kar ta fasa gilas din Suna shiga ciki su kabi wata qofa mai kama da ofis,� Dr. ya tsaya gaban wata mata cikin Harshen turanci su kai magana sannan ta miqa masa wata yar lakarda ya yi wani dan rubuce rubuce ya miqa. mata itasa hannu, � sannan ta mike ta yi masa nuni da wani kujerar dake gefe da dan tebur dinta guda a gabanta; wanda aka dora News paper a sama, ta kawo masa lemu da cake sannan taja hannun Saude. . “Come and enter my frnd Saude ta ce ikon Allah ai ke kika san shi Tasa hannunta cikin na Saude suka shiga cikin wani qaton wuri nena gaske wanda aka zubama duk wani" injin � k0 wata na’ura ta gyaran jiki ‘Matar ta kira wata babbar mace Bahaushiya wadda ba zata wuce shekara arba in ba ta nuna mata Saude su Sukai kai magana cikin harshen turanci da matar ta mikawa Saude‘hannu da murmushi a fuskarta tana fadar. “You are welcome my sis. ' Saude ta yi sukuti tana kallonsu cike da takaicin turancin banzan da suke mata. K0 matar ta lura ne? Oho ta canja harshe zuwa Hausa. “Sannu da zuwa ‘yar uwa mu je k0?� Ba musu Saude ta bi ta suka nufl Bangaren gyaran gashi, ta zauna a kai mata gyaran gashi sosai sannan suka wuce Bangaren gyaran jiki, inda a kai mata dilka da halwa lokaci guda, daga nan a kai mata gyaran qafa da na akaifa. Tun kafin a qarasa dama Saude ta gama tsurewa da tsabar kyan da ta gani kwance a jikinta, ita kanta ba ta taBa sanin haka ta hadu ba sai yau, don k0 Indiya sai haka, saboda idan baka san ta ba aka ce maka Ba’indiyace ba yanda za ai kai musu. ' Ita kanta ta san sun ci lokaci, don k0 da ba ta duba agogo ba ta san dare ya ja sosai. Ana gamawa suka fltO inda Dr. Ahmad ke zaune rike da jarida yana dubawa suna Karasowa ya ajiye jaridar ya mike yana kallonta tamkar wadda ta fado daga sama, lokaci guda kuma ya lumshe idanuwansa ya bude ya juya ya koma wurin ‘yar Baturiyar nan wadda ke ta latse-latse cikin computer ya mika mata A.T.M dinsa tasa ta cire kudin sannan suka flto daga wurin. Ita dai Saude kallonsa kawai take, amma tambayoyi ne cike fal da cikinta, wanda ta tabbatar ba * ta da mai amsa mata su sai shi kadai. Suna mota wanda suka shiga kamar dazu direba ya ja su suka fice daga » harabar wurin Saude ta lalubo duk wani karfin halinta kafin ta iya bude baki ta kira sunansa. “YallaBaii� ,. Dr. Ahmad ya dago da idanuwansa daga saman wayarsa yana kallonta kan ya ce, ‘Ya dai Sande?" “� Ta dan sha Jinin jikinta kafin ta ce ‘Ina so in dan � yi wata� yar tambaya.� ce Dr ya dauke kansa daga kanta kafin yace, ‘Tun » kafin ki yi tambayar na san abin da za ki tambaya don haka ki yi haquri ki hadiye zan ba ki amsa da kaina � idan lokaci ya yi.-� Za ta sake magana ya daga mata hannu, hakan yasa ta ja bakinta ta tsuke a dole, ta bar zuciyarta na faman� dukan tara-tara. Suna isowa gidan ta .kwasa da sauri da niyar ta riga shi shiga gidan, Dr. ya yi saurin tsayar da ita ta hanyar kiran sunanta, ta ja ta tsaya cak � Da kansa ya Karaso har inda take ya daidaita tsayuwarsa a gabanta kafin ya soma magana, ‘Ki shirya gobe da safe za mu fita.� Saude ta yi saurin dago da fuskarta tana kalloh shi shi ma ya zuba mata idanuwan nasa wanda babu alamar fargaba a cikinsu,idanuwanta suka kawo kwalla cikin muryar kuka ta soma magana. “Ni wallahi ,ba zan je ba na gane so kawai ka ke ka jaza min bala’in da ba zan iya dauka ba na rantse da . Allah babu inda zani .... � Ta Kara rushewa da kuka. “Don Allah don Annabi ka taimake ni kar ka jaza min bala‘in matarka don Allah...� Dr. Ahmad ya yi wani murmushi wanda ya tsaya iya laBbansa kawai kafin ya ce, ‘Ashe kina da baki haka? Da kyau. To ki dai shirya� fita gobe koma me ye zai faru ai kina iya daukarsa idan kuma ba ki zoba to ki tabbatar ni da kaina zan shigo in dauke ki kin san kuma zan iya, don haka sai da safe.� . Ya juya ya yi gaba ya bar ta tana masa rakiya da kallon da ke cike da mamakinta karara, don a yanzu hawayen ma sun daina zuba. Mamaki da fargaba suka kashe ta, ita kanta ba ta san tsawon lokacin da ta dauka a tsaye ba, don sai da ta yi da gaske sannan ta iya jan qafafuwanta ta yi gaba. Tunane-tunane da damuwa yau su suka hana Saude barci da wuri, shekarunta sun yi Karancin da za ta iya yankewa kanta hukunci, da ta gaji da tunanin sai ta kifa kanta samaun filo ta shiga kuka mai sauti, sai da ta yi mai isarta sannan ta yi shiru don kanta, babu wanda ya lallashe ta, sai ajiyar zuciyar da take ajewa akai akai. A' haka barci barawo ya sure ta ba tare da ta sani ba. ' Tun da garin Allah ya waye Saude ke zaune saman gadonta ta zuba uban tagumi da