← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 90

Sashe 22

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

falon, yana shigowa ta tsaya da aikin da take tana kallon maigidan nata bakinta na fad'ar. “Latiya dai k0 Alhaji?� Muryarshi ba dadi ya ce, “Ina yaron nan yake?� Hajiya Hanifa ta ce, “Yana dakinsa ka san ai bai farka ba yanzu.� Alhaji Bashir ya ce tado mini shi maza-maza. Jikin Hajiya Hanifa na rawa ta nufi kofar dakin Hamid din. ta kwankwasa masa yana kwance nannad‘e cikin bargo yana Sheqa barcinsa, saboda rashin baccin da ya samu jiya. Ya bude idanuwansa tare da yunkurawa ya mike, yazo ya bude kofar, Hajiya ta dube shi kafin ta ce “Ka je Abbanka na falo yana jiran ka Ya amsa da. to, sannan ya juya ya koma ciki ya nufi bandaki ya wanko bakinsa da fuskarsa sannan ya fito ya dauko jallabiyarsa ya sanya ya fito Alhaji Bashir yana tsaye inda yake har Hamid ya qaraso yana qokarin dukawa ya gaishe da mahaifin nasa, ya ji saukar wani gigitaccen mari ya ratsa . Kunnensa ya dago da sauri yana kallon sa, cikin Bacin rai Aihaji Bashlr ya soma fada“Ni zaka dauka dan iska k0 Hamid dama abinda. ka koyo kenan a qasar wajen da na tura ka. Ni zaka jawa; abin fada a cikin garin nan. To baka isaba., maza ka tattara yanaka-yanaka ka koma Kaduna, yau ba sai gobe ba ka je ka kula da kamfanina tunda aikin gwamnatin bai zama dole ba, ba zaka zauna nan ka ja mini abun kunya ba, dama shi yasa da aka ce ka je ka nemi yarinyar nan Zainab kaqi saboda ba ka gaji da barbada ba, ka yi daidai ka kyauta tashi ka ba ni wuri.� Jikin Hamid ya yi matukar yin sanyi ya miqe a sanyaye tare da fadar, “A yi h akuri." Ya juya ya koma dakinsa ya kwanta, tunani ya addabi zuciyarsa ‘ya rasa hanyar da zai bi ya taimaki yarinyar nan, ya � lusmhe idanuwansa yana jin wani abu na masa yawo. Ya san fushin mahaifinsa yana fushi da shi ya yi kwana uku, tabbas kuma dole ya tafi Kaduna tunda ran mahaifin nasa ya Baci, ya lallaBa ya mike ya cire jallabiyar da ke jikinsa ya fada bandakin da ke cikin dakinsa. Saude ta dawo daga tallan safenta ta iske Laure Zaune itada Malam Bala suna tattauna magana! Hamid, ta a jiye bokitin wainar ta 'bama Laure kudin, ta karba tana kirgawa sannan ta ,dubeta tana fadar. “Jeki ga wake can ki kai markaden alala.� Saude ta amsa da to, sannan ta wuce Malam Bala ya dubi Laure yana fadar, “Kin ga na ma mance, Malam Garba ya fada min za"a kawo kayan sa ranar yarinyar nan gobe Laure ta cc, “Ai garama a gaggauta Malam mu kawar da yaran nan mu huta.� � Iya abin da da Saude ’ta ji kenan ’ta fice tana jin tamkar za ta kifa saboda tashin hankali da fargaba. Haka ta je ta kai markadan ta dawo ta dafa alalar duk Laure na zaune tana kallonta, ta gama ta zauna ta Kirga mata a bokiti, sannan ta dauka ta tafi Hamid da ke kokarun sanya jakarsa a mota ya hango ta ya rufe motar da sauri � ya nufo ta da murmushi a fuskarsa ya ce, “Ranki shi dade barka da fitowa.� Saude ta waigo tana kallonsa kafin ta gaishe shi da dakusasshiyar muryarta. Hamid yargyara tsayuwa yana fadar. “Dama ke nake jira ki taho mu yi magana da tun dazu na Hamid ya ce ‘Kinga wannan fitowar wallahi Kaduna zan tafi yanzu yanzun nan mahaifina ya tura ni amma karki damu kwana uku kaWai zan yi in dawo saboda maganar ki, akwai wata hukumar kula da haqkin mata zanje ofiss din su a kan maganar ki Saude ta daga masa kai alamar eh ya yasa hannu cikin aljihu ya Ciro kudi masu yawa ‘yan yan naira dari biyar biyar guda ashirin ya miqa mata yana fadar ‘Ga wannan ki riqe ki yi amfani da su kafin in dawo.� Saude ta zaro idonta wadanda suka ciko da hawaye, ta girgiza masa kai alamar a’a, Hamid ya hade fuska yana kallonta ya ce “Karbi na ce mana me ye haka?� � Ganin yanda ya hade fuska yasa Saude ta sa hannu ta karBa tana fadar, “Na gode.� Ya zaro wata waya cikin aljihunsa ‘yar qarama mai kyau ya mika mata. “Ga wannan ki riqe ta hannun ki zan rinka kiran ki mu yi magana.� Saude ta karBa ya juya yana fadar, “Sai na dawo.� Saude ta juya da niyar taflya su kai ido hudu da ‘Yar Baba tana tsaye tana kallon su, suna hada ido ‘Yar Baba ta ja kwafa tana kada kai ta wuce 'Hankalin Saude ya yi masifar tashi wasu zafafan hawaye suka biyo kuncinta ta ji tamkar ta zubar da kudin saboda firgita, cikin tsoro ta je tallar yau ta dawo cike da tsoron irin hukuncin da za ai mata. Haka ta shigo gidan ‘tana faman sanda kamar munafuka a tsakar gida ta samu Laure da dillaliya suna zaune. Ita iyan tana kan tabarma, ita kuwa dillaliya tana kan kujera ‘yar tsugunne. Saude ta durkusa tana gaishe da dillaliyar sannan ta mikawa Laure kudin tallar nata, ta karBa ta sake mika mata hannu. “Ba ni sauran wanda kwarton naki ya baki Jikin Saude na rawa ta ciro kudin da wayar ta mika mata, Laure ta shiga jujjuya wayar a hannunta da kudin tana taBe baki ta dubi dillaliya tana fadar. “Duba ki ga fa.� Dillaliya ta karba tana gani, ta dago tana kallon Laure tana fadar, “Amma ni sai nake ganin kamar wata banza ce ta sauko muku daga sama, kawai ki yi kwance-kwance kinada abun duniya idan ma yaudara ce ta kawo sa ke dai me ya dame ki ita ta jiyo.� Laure ta ce, “Hmm! Dillaliya kenan ba zaki gane ba yaron fa da gaske aurenta zai yi ba wai da wasa ba.� Dillaliya ta dan yi shiru kafin ta ce, “To yanzu ya ki ke ganin za a yi?� Laure ta ce, “Gaskiya na fara tsora ta da lamarin nan karfa danhakin dakaraina yazo yatsone maka ido. Shi yasa na kira ki kawai ki dauke ta ki tafi da ita AIKATAU cikin gidaje har zuwa lokacin bikinta shekara guda za a sanya ranar daurin aurenta sai ki taho da ita kawai kin ga na yi maganin takadaranci k0 ba haka ba?� Dillaliya ta ce, “AI ko kin kawo shawara Laure, Abuja ma zan tafi da ita gidan wani sabon dan Majalisa, mai tashen kudi, wata kawata ce ta yi min maganar kai masu ma’aikata gidan, don haka ta shirya gobe zan zo in dauke ta da sassafe mu tafl, duk wata kina da dubunki biyar zan rinka karBo miki na albashinta.� Dadi ya kama Laure ta ce “Allah ya kai mu Kawata, tun Asuba ma zan tasheta.� Dillaliya ta ce, “Amma kina ganin ba za mu samu matsala da mahaifinta ba?� Laure ta ja wani gajeran tsaki tana fadar, “Ke kuma da sokawa zance wuqa kike wannan qotan wake san ya shi a lissafi ai sai yanda na yi da shi.� Dillaliya ta ce “To shi kenan babu matsala ‘yar uwa. � . Duk labarinsu Saude tana jiyo su daga daki tana zaune saman simintin dakin kanta na jingine da bango, wasu irin hawaye ne masu zafin gaske kebin kuncinta. Wayyo duniya ita dai ta san ta zo duniya a rashin sa’a. Haka ta ci gaba da rera kukanta babu mai‘lallashinta. Washe gari Karfe takwas kamar yanda dillaliya ta fada ta zo cikin shirinta Laure ta tiso qeyar Saude a gaba, ta hada ta da dilla'iyar tana faman zuba mata kashedi. ‘Kl kulada aikin da za,a baki kuma banda dan hali, dan wallahi kika sake ki ka yo abin da za a koroki ki ka dawo min lokacin dawowarki bai yi ba wallahi saina shake ki kin mutu kin ji na fada miki, kuma kinsan zan iya Ta zaro naira dubu cikin kudin da Hamid ya ba ta, “wanda ta kwace, ta mikawa dillaliya tana fadar. “Ga wannan kiyi kudin mota.� Dillaliya ta karBa ta tisa Saude gaba suka tafi. Sai a lokacin wasu hawaye masu zafi suka samu damar zirarowa daga idanuwanta, tana ji tana gani suka nufa tasha cikin� yar qaramar motar nan Kurkura. Suna sauka dillaliya ta kama masu motar Abuja suka � hau, dama. saura mutum uku, aka samu wani namiji yakarasa cikon na ukun direbaya dauhanyar Abuja.
Chapter 22 · 0% Book details