← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 90

Sashe 40

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Me nake gani haka Dr? ‘Yar aikin ce ke cin abinci a food flask dinka, kam babban ....... � Ya watsa mata wani kallo lokacin da ya kashe wayar ya ce “To k0 rai ya yi baki ne? Ai dai anawa take ci ba a baki ba k0? Ya yi mata tambayar cike da � isa da gadara. _ � Asma ta qara shaqa kafin ta ce ‘Hmm! Dr. kenan amma dai .ka san wannan ba qaramin kaskanci bane da zubdawa kai girma ka yi bak0? A. Zo a iske yar aikin ka na cin abinci a kwanan ka, ‘yar aikin ma ‘yar Kauye, jaka dakikiya, wadda talauci ya yi masu daurin ..... Dr. yayi saurin daga mata hannu ‘ya isa haka Asma, kin sanni sarai ban san cin fuska don Allah tunda ban aika miki da katin gayyata ba ki bar nan, banasan ciwon kai.� ' Takaici ya kashe Asma, ta matsa daf da shi tare da sassauta mur'ya ta ce ‘Yanzu Dr saboda ‘yar aikin ka ka ke cimin fuska haka?� � Ya ce ‘Amma kin sani Sarai ba a gaya mini yanda zan yi ko?� Haushi ya kama ta ta juya a zafafe ta bar masa falon, ya taBe baki ya juya wurin Saude wadda � lomar abinci ta yi wa tsaye a maqogaro tun dazu ta gaza hadiyewa, saboda tsabar firgici da tsoratar da ta Dr. ya zauna bakin kujerar dake fuskantar ta yana fadar. “Ki nutsu ki ci abincin ki sosai ga likita nan zuwa.� Hawayen da suka taru a kwarin idanuwan ta suka gangaro cikin kuka ta ce, ‘Wayyo Allah na ka ja mini Allah kadai ya san abin da za ta yi mini yau na banu na lalace! � Dr. yace ‘Kuka kuma Saudat? Yanzu nan har an yi abin kuka? Lallai ashe kina da kukan jini nan gaba. � Saude ta Kara rushewa da kuka, ‘Wallahi gida zan tafi� Dariya ta kama Dr. ya ce, ‘Ashe matsoraciya ceke lallai Saudat na tabbata da Asma ta ji haushin ki da k0 sama da qasa za ta hade anan ba za ta kyale ki ba, ta riga ta san halina ne sarai don haka ba ta damu da ke ba ta kaina za ta dauki matakin don haka ki ma kwantar da hankalin ki ki ci abincin ki � Saude ta ture abincin tare da fadar, ‘Na qoshi.� “Me? Ai wannan ne baki isa ba k0 ki dauka ki cinyc shi ko yanzun nan in kira ta ince kin cetazo ta kwashe kwanukan kin gama.� Saudc ta yi saurin waro ido waje tare da janyo abincin da saurinta ta ci gaba da ci, ya yi dariya a , zuciyarsa sosai ya ce matsoraciya. Tun kafin ta gama cin abincin likitan yazo ya duba ta sosai tare da rubuta mata wasu magunguna, ya kira direba yasa ya je ya siyo mata su, ya dinga lallashinta yana rokon ta a kan ta rinka shan magungunan, sannan ya ba ta ta tafi Cikin tsoro ta shiga sashin nasu don gani take Asma na nan na jiranta. ' . Tana shiga sashinta ta maida qofa ta rufe ta ajiye magungunan ta haye kan gado ta janyo wayarta da .taketa faman ruri tun dazu ta ci gaba da wayarta. Washe gari da yamma tana zaune a bangaren Dr. tana aiki, zuciyarta sai faman sake-saken neman mafita take saboda wayar da su kai da Hamid jiya da daddare Dr. ya sauko daga samansa yana sanye. da qananan kaya irin na hutawar turawa, ya tsaya daga gefen kujera yana kallon Saude wadda ke durkushe tana 'goge goge � . Jikinta ya ba ta tamkar ana kallonta, don haka ta yi ‘saurin waiwayawa, tsaye ta gan shi a gabanta ya harde hannuwansa a kirji tamkarmai nazarin wani abu. Saude ta yi saurin durkushewa tana masa sannu da fltowa, bai amsa mata. ’ba� sai ma ya sake gyara tsayuwarsa. “Me yasa baki san hutawa?� Saude ta dan kalle shi kadan kafin ta ce ‘Ai aikina ne shi yasa.� Dr. yadan dauke kai kafin yace, ‘Ai kin kusa barinsa, saki wannan aikin ma taho mu fita mu sha iska.� Bai jira abin da za ta ce ba ya yi gaba abinsa, Saude ta raka shi da idanuwanta. To me yake nufi da ita? Ba dai korarta za su yi ba? Da sauri ta zabura ta bi bayansa. . Hadaddan wurinn shakatawa ne wanda aka kashewa dubban nerori wurin Kawata shi, don an zuba abubuwan ban sha’awa da debe kewa. Saude ta . koma jikin wani dodon roba, tana kallon Dr. wanda ke wasa da dan biri, can ya dago ya yafito ta da hannu alamar ta zo duk da tsoron da ya cika mata zuciya haka ta dake ta tafi inda yake, ta tsaya daga gefe tana kallon su, ba ta ankara ba ta ji ya fizgo hannunta ya hada da na birin, yana wa birin magana cikin harshen turanci. Mutuwar tsaye ta yi don tana bala’in tsoron sa sosai, don ma yana dan Karami, sai ta ga ya ’fadi' Kasa alarnar gaisuwa. Dr. ya yi dariya yana kallonta ya ce “Ana gaishe kifa?� Kallonsu kawai take bata � iya yin magana ba, birin ya mike yana ta faman zazzagaya ta yana tsalle-tsallen murna. ' , Dr. ya janyo hannunta suka nufi wani.� qaton lilo na roba mai matattakala ya dan kalle ta da murmushi a fuskarsa ya ce “In hau za ki jujjuya ni�?� ‘Duk da haushin riKon da ya yi mata ya kama ta sai da ta yi dariya saboda yanda ya yi maganar. Ya ce, ‘Okoy, dariya ma na baki to bari in dora ki in jujjuya ki.� Tun kafin ta yi wani yunkuri ta ji ya sure ta ok ya dora saman lilon. Saude ta fasa wata uwar kara saboda razana, don ita gaba daya ma lilon tsoron shi take yi, dariya ta bawa Dr. sosai na kauyancin nata, don haka yana dariya yana jujjuyawa da ita, mutuwar zaune ta yi ta . runtse idanuwanta tana sauraren ikon Allah, shi kuwa dariya kawai yake mata, yana zolayarta ganin ba shi .da niyar daina juya ta yasa ta bude idanuwanta tana shirin kuka, ta hau rokonsa. ‘Don Allah don Annabi ka sauko da ni.� Dr. ya tsaya da lilan ya matsa yana fadar, ‘To sauko tunda ba kya so.� Saude ta waro idanuwa don ta san ko da kudi aka bata bazata iya saukowa ba, ya yi murmushi tare da mika mata hannunsa ta rike sannan ya sauko da ita, yana mata dariya yace matsoraciya duba ki ga aku na .kallon ki. � Saude ta yi saurin juyawa, caraf ya riKo hannunta ya ja ta da saurinsa. Haushi ya kama ta yanda ya maida ita kamar Karamar yarinya. Saman wasu kujerun roba ya zaunar da ita shi ma ya zauna, suka sa zagayayyan tebur din a tsakiya. Saude ta bi abin . da aka dora' saman tebur din da kallo, wanda a kai � � rafin din shi gwanin burgewa. Dr. ya miKa hannu ya dauko ya mika mata ta tsaya tana kallon shi ya miqa mata tare da fadar. “Karba mana.� Ta mika hannu ta karba,tana kokarin bude rafin leda din. Dr. ya yi saurin tsaida ita yana fadar, ‘tsaya tsaya waya fada miki idan aka bawa mutum gift budewa yake'a take bakauyiya ai bari ake sai an tafl.� Yana maganar cike da zolaya. . Saude ta zumBuro baki" jin ya kira ta da bakauyiya, dariya ta kama shi ya ce, ‘A’a ‘yanmata ashe kin iya fushi irin haka?� Ta dauke kanta ba tare da tace Kala ba. Ya ce, ' ‘Wai fushin ki keyi da gaske am so sorry, tuba nake -kaina bisa wuyana.� Dariya ta kubce mata yanda ya yi maganar a ladafce sai kace ba YallaBai din da ta sani ba, ganin dariyarta yasa ya mikc yana fadar “Taso muje kin ji ana ta kiran sallah a_ masallaci.� � Saudeta tashi ta mika masa gift din da ya bata, ‘ya dan zuba mata idanuwansa babu alamun wasa a fuskarsa ya ce ‘Da shi za ki tafi kyauta ce daga gare� ni.� Yana gama fada ya juya ya yi. gaba abinsa, ba tare da ya saurare abin da za tace ba. Tsabar mamaki da kaduwa su suka hana Saude furta komai, har sai da ya kusa bacewa ganinta saunan ta iya wage murya tana fadar, “Na gode kwarai.� Hannu kawai ya daga mata ba tare da ya juyo ba ya Bace abinsa, ita ma ta yi gaba cike da zullumin abin da aka nannade haka. Tana .shiga dakinta ta fada kan gadonta ta yi zaman dirshan ta shiga bude kyautar, ta ciro wani kyakkyawan kwali mai kyan gaske da zanen waya waya a jikinsa. Saude ta bi hoton wayar da kallo kai da gani ka san ta yi tsadar gaske, a zuciyarta ta furta ‘Allahumma arzuquni" tasa hannunta ta bude kwalin. Gabanta ya yi wata mummunar faduwa ta yi � masifar firgita ganin sabuwar wayar kwance cikin kwallin, ta ciro ta tana jujjuyawa, touch screen mai shegen kyau, wadda ta san ko da kudl aka hada ta ba za ta iya kunnata ba. Saude ta riqe wayar tare da dafe kai, yau na shiga uku ni Saude, wai me ke shirin faruwa da nine? Wasu irin hawaye suka ziraro daga idanuwanta ta lura mutumin nan so yake ya jaza mata bala’in da ba zata iya dauka ba, yanzu tsautsayi yasa Hajiya ta samu labari ya kenan? Motsin taflyar da ta ji ne ya sa ta zabura ta maida wayar cikin kwalinta ta tura a qarkashin filonta, tana faman‘muzurai. Aunty ce ta shigo da sallamarta suka gaisa sannan ta ajiye mata wata leda Saude ta mika hannu ta janyo ledar tana duddubawa. Sabulan wanka ne dana wanki tare da kayan shafawa da mayuka, ta ajiye� leadar gefe ta koma ta kwanta tana fatan gari ya waye ta je ta maida masa wayarsa, don ba zata yarda ba ya jaza mata tashin hankali da bala’in da ba za ta iya dauka. Ba Dole nema ta runtse ido ta fada masa� ya fita daga rayuwarta ita dai ba kowan kowa bace hakan kuma ba yana nufin ba ta san mutuncin kanta bane da wannan tunanin bacci barawo ya sace ta. Washe
Chapter 40 · 0% Book details