← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 90

Sashe 13

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya janyo wani qaton faskare laure ta riqe tana fadar. a a dan Allah ka yi hakuri Malam kar ka kashe shi.� ° Malam ya goce yana fadar, ‘Wallahi yau sai dai akwashi gawa'rsa cikin gidannan inyaso nima a kashe ni.� Ya nausa cikin dakin ya hau Rabi’u da duka kamar Wani zautacce, bakin ciki, mamaki da tsantsar tashin hankali su suka hana Rabi'u komai saidai kare kansa da yake, sai da yaga Malam makasar sa yake: nema sannan ya mike ya yi waje Hayaniyar su ce ta tayar da Saude daga baccin da take, ta tashi sai zazzare idanuwa take, don ita ba ta San abindake faruwaba,taga dai Malam nata faman shan kwalla yana dukan Rabi’u ta tashi itama cike da . tashin hankali kafin ta motsa � Rabi’u ya ruga malam ya bi shi har , “Sai na kashe ka la’anan nan Allah, Allah ya isa tsakanina da kai, wallahi kar in sake ganin ka cikin *gidan nan, kai cikin garin nan ma idan ka bari muka hadu sai na halaka ka munafukin Allah.� Ya juyo ya dawo gidan ya tattara masa ‘yan zummokaransa ya fito kofar gida ya watso su yana fadar, “Ka san inda dare ya yi maka, ka ji na fada maka, Allah ya yi wadaran ka, yasa ka hadu da mummunan hatsarin da za a kasa gane ka, Allah ya wulaqanta ka yanda kai min Allah ya yi maka wanda . ya fi shi, dan iska. Insha Allahu sai ka wulakanta, Allah ya daga maka hakali ya hana nutsuwa a duk inda ka ke� Laure ta fito tana fadar, “Don Allah Malam ka shigo gida haka nan tun'da dai ka kore shi ka ga har � mutane sun fara taruwa.� ' Malam Bala ya dawo gidan ya ci gaba da 'zazzaga masifa tamkar wanda ba ya cikin hankalin shi, Saude dai na kallon su kuka kawai take tamkar ranta zai fita, ga jinin da ya bata mata jiki wanda har a lokacin bai daina zuba ba Ta lallaba ta mike ta saka hijabinta ta fito wajen tana neman Rabi’u can ta hango shi zaune saman dakalin Kofar gidan Malam Akilu mai Rauhanai ya hada kan shi da gwiwa da ‘yan kullin tsummokaransa a gaban shi. Wani sabon kuka ya Kara kwacewa Saude ta nufi inda yake tana kiran sunan shi, Rabi’u ya yi saurin dagowa yana kallonta fuskar shi sharbe-sharbe da hawaYe, ya yi mata nuni da hannu ta Karaso inda yake. ' Saude ta karasa ta durkusa gaban shi ta fashe da 'wani irin kuka mai ban tausayi, tausayin kansu ya kara kama Rabi’u ya samu da kyar ya iya tsaida nasa kukan, muryar shi a dakushe ya soma magana ba tare da hawayen sun daina zuba daga idanuwan shi ba. “Saude kin ga yanda Allah ya yi damu kuma k0? , Ki yi hakuni na san Ubang‘iji na sane da mu ba mancewa ya yi da mu ba, kuma shi ya san yanda zai yi da mu, tashin hankalina Saude a yanzu daya ne ' yanda zan tafi in bar ki ban san a wane hali zan barki ba wace irin rayuwa ce za ki fuskanta bayan bana nan, ban sani ba.� Yasa hannu yana goge hawayensa kafin ya ce, ‘Dole zan tafi', dole zan bar garin nan Saude ki yi hakuri ki rungumi rayuwa a duk yanda ta zo miki kar ki yarda ki sabawa Ubangiji a duk halin da kika tsinci kanki ciki, na dadi k0 kishiyar hakan. Na � san insha Allahu Ubangiji ba zai bar rayuwarki ta lalace ba." � Yasa'hannu cikin aljihunsa ya ciro wasu kudi ‘yan, dari biyar~biyar da alama kudin aikinsa ne ya raba biyu ya miqa mata rabi yana fadar, “Ga. wannanki riqe a hannunki kiyi amfani dasu insha Allahu zaki rinqa samun aikena a duk inda na shiga a fadin duniyar nan.� Ya ajiye mata kudin saman jikinta ya mike yana fadar, “Allah ya hada fuskokin mu da alheri." Saude ta yi saurin miqewa ta riqe shi tana wani irin gunjin kuka mai daga hankali. “Don Allah kada ka tafi ka bar ni Yaya wallahi mutuwa zan yi idan ka tafi Wayyo Yayana!� Ta qara fashewa da wani gunjin kukan. Rabi’u ya dafa ta yana kallon idanuwanta kafin ya ce, “Ki yi haquri Saude ni kaina ba dan na so ba zan tafi inbarkiba,da zaiyiwu da dole dake zantafi, amma ba yanda zan yi ne tunda ke macece amma na yi miki alkawarin duk inda make a duniya ina tare da.... Ya kasa fadar abin da yake son fada saboda kukan da ya kwace masa shi ma. Ya zame hannayenta daga jikinsa yana fadar, “In har kina sona da gaske Saude kada ki sake cewa komai ki juya ki koma gida ni na tafl sai wata rana.� Ya dauki jakar kayansa ya juya yana tafiya yana sharar hawayen da ke zuba daga idanuwanshi kamar an kunna famfo, Saude ta duka a gun tana wani irin gunjin kuka tun iya karfinta. Rabi’u na jin ta amma bai waiwayo ba saboda yanda yake jin zuciyarshi na Barazanar tarwatsewa gaba dayanta ga shi a lokacin ba jama’a da yawa a waje saboda safiya ce sosai. Tunda Saude ta duka ba ta sake tashi a gun ba, tun tana kukanta iya karfinta har muryarta ta disashe. ~ Rana ta soma mutane suka fara fitowa daga gidajensu duk wanda zai wuce sai ya yi mata magana, amma ba ta tashi ba, tana duke cikin Kasa tana' kuka, ba ta ankara ba sai dai taji saukar duka ta ko ina� tana dagowa ta ga Inna Laure, ta mike ta � kwasa da gudu ta nufi hanyar gida, ita kuma ta raka ta da jifa. ' Tana shiga cikin gidan ma nan ma Malam ya dora mata da na shi dukan yana zaginta tare da yi mata mugun baki. Inna Laure ta shigo babu alamun ' tausayawa� a fuskarta ita ma ta hau zaginta tana fadin * “’Yar iskar ai ba yau suka fara ba, ai dole ta zauna tana~ta aikinkuka karabata da jin dadinta munafuka.� Ta hankade labule ta shiga daki ta dauko mata wasu tsummokaran kayan ‘Yar Baba wadanda ta gama da su ta watso mata tare da wando da tsumman dunzugu, ta gwada mata yanda za ta sanya sannan ta � dora mata tallar wainar. Haka Saude ta dauki tallar ta tice daga gidan tana matsar kwallah. Haka ta je tallar ta dawo ba taci komai ba, sai kukan da take ta faman yi. Haka ma da rana ta dauki alala ta sake tafiya, ruwa kawai ta iya sha a wurin ranar yau, duk inda ta gifta sai ta ga tamkar za ta ga Yayanta amma k0 mai kama da shi bata gani ba haka ta karaci yawon tallar ta ta dawo da yamma likis. Ta samu Inna Laure da dillaliya suna tsakar gida saman kujera ‘yar tsugunne taya ni gulma suna hirarsu har da shewa. Tana shigowa Laure ta nuna ta da baki tana fadar. “Kin gan ta nan fa dillalliya, wan: ai aikatau ga wannan ai tallar cc kawai ta dacc da ita.� Dillaliya ta ce, “Haba dai a ganin ki dai, amma in da ni ce da wannan wallahi Abuja zan tura ta kawai." Saude ta qula ta gaishe da dillaliyar sannan ta mikawa Inna Laure cinikinta ta mike ta wucc dakinta. Tana jin Inna Laure na fadar, “Hmm! Dillaliya kenan ai ni duk wanda ya ci tuwo da ni miya ya sha, to shi kuwa k0 miyar ma bai sha ba don in fada miki dama cike nake da shi don har na fara tunanin in zuba masa shinkafar Bera a abinci ‘ya ci kawai, sai dai a wayi gari ya yi mushe. Ai in fada miki ina tashi. da Asuba na 'ga yarinyar jinin ya zo mata, ai a take dabara ta fado mini, ni kaina sai da na shiga daki na yi ta dariyar qeta yanda na ga Malam na sharar ‘yar kwalla.� I Duka suka sa shewa suka tafa. Can Saude ta jiyo diilaliya na fadin “Ke wai ba zaki saro gyada ki soya mata ta rinqa zama kofar gida ba na ga sabuwa ta fara shigowa wallahi ciniki za ta yi ta rinKa zama nan kofar gida da daddare.� Laure ta ce “Ai k0 kin kawo shawara bari gobe Talata inje ‘Yar Kutungu da kaina in siyo mai kyau in zo in soya mata Ai shi yasa nake son ki kawata Akwai ki da bada shawara mai kyau. Saude ta lallaBa ta kwanta tana jin zuciyarta na tuquki wasu zafafan hawaye suka rinka biyowa kuncinta ba ta da mai lallashin ta yau dakin ya yi matA bakikkirin, saboda rashin rabin jikinta, Yayanta a cikinsa Sai yanzu ne ta gane marainiya ce ita marar gata, yanzu ta yarda da maganar Yayanta da yake ce mata bata da. gata a. duniya, ba su da kowa sai Allah. Ashe da gaskiyarsa. Ta sake rushewa da wani sabon kukan lokacin da ta tuna da lokacin da ya dawo daga aiki jiya ya kawo mata kayan kwalliya. * Ta tuna da irin yanda yake lallashinta idan ya ga ta shiga damuwa duk ~ yanda zaiyi sai ya yi ya tsaida hawayen nata, ga shi yanzu baya nan. Tabbas ta rasa gata a duniya ta rasa jigon rayuwarta. don tana ji a jikinta da wuya. idan za � tasake ganinsa tunda shi kan shi baisan inda za shi ba yanzu, wala ya mutu k0 ya yi rai. Shin k0 yana a wane hali yanzun ma? “Wai k0 ba da ke nake ba ne Saude kina ji ina ta faman kiran ki?� Saude ta jiyo muryar Laure, don haka ta zabura ta mike ta goge hawayenta ta yo tsakar gidan a lokacin dillaliya ta tafi Laure ta watsa mata harara kafin ta ce, “’Yar iska duk uban me kike ina kiran ki kin yi min shiru?� Saude ta yi shiru tana kallon yatsun qafarta hawayen da suka taru a idanuwanta suna diga qasa, Laure ta ja tsaki tana fadin. “Ke dai kya kai su in kaya ne wuce ki ki dora mini sanwar tuwo, idan kin dora ki zo ga kayan wankina can na jika ki wanke mini su.� Saude ta yi saurin dagowa ta kalle
Chapter 13 · 0% Book details