← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 90

Sashe 75

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da sallah a cikin lokaci. Bayan sallar la� asar kuma Shukura ta koma gida saboda gobe tana da lecture a school. Kwanansu uku da dawowa ya kama ranar alhamis, Saudat na kwance a falonta ita da Nabil da Nabila tana kallonsu suna home work da aka ba su daga makaranta, Momy ta shigo felon kafadarta na rataye da katuwar jaka, ‘sai rigar likitoci sagale a dayan hannun da alama dawowarta daga ofis ke nan. Duka yaran suka zabura suka nufe ta a guje suna fadar, “Oyoyo my Momy, welcome". Ita ma da fara‘a a kan fuskarta ta rungume yaran a jikinta tana shafar kawunnansu. Saudat ta yunkura ta mike ta nufi inda " ' Momy ta ke ta karbi jakar hannunta da Iafkwat dinta: ‘da mayafin jikinta ta nufi Sangarenta kai tsaye kicin ta nufa ta jero kulolin� .abinci a babban faranti tareda kwalin lemo', da ruwa masu sanyi ta nufo falon, inda ta samu� . Momy har ta yi wa kanta masauki saman tallausan ' kafet din falon, yaran duk sun zagaye ta suna ta_ shirmensu. � Saudat ta ajiye mata kayan abincin a gabanta, ta soma bude kulolin tana mata sannu da zuwa. Momy ta rike farantin tana fadar. “Barshi kawai Saudat, kije falon waje Hamid nanan ya zo zaku gaisa� . . Saudat ta washe baki tana fadar. ' ~ “Kai Momy, ashe bai mance dani ba, yau fa kwana uku . ke nan da dawowarmu daga -Dandagora, amma bai zoba shi da ya ce ‘a * washegari zai zo?� Momy ta ce “Ah to, ni kaina da na ganshi a yanzu sai da nayi mita, amma dai yace ba ya garine shi ya sa, dawowarsa kenan. Tashi ki je kar yaga an barshi shi kadai. _ � Saudat ta yunkura ta mike ta nufi kan gadonta ta jawa farin mayafinta ta yafa, ta saka takalminta flat Shoe shi ma fari A tsaye ta same shi cikin falon ya nannade hannayensa a qirji ya zuba wa qaton hoton da ke jingine a bangon daki ido, na su Nabila da Nabil ne wanda .aka yi musu a harabar wurin shakatawa da ke cikin park dukkansu sun yi matukar kyau tamkar ‘ya’yan da ke rayuwa cikin dusar qankara. Saudat ta qaraso cikin falon da ‘yar siririyan sallamarta, bakinta na dauke da murmushi. Hamid ya yi saurin waigowa yana kallon mai shigowarr tare da amsa mata sallamar Saudat ta tsaya dan nesa da shi tana fadar, “Saudatu ya tabbata kan Yaya Hamid wanda ya manta da ita tsawon kwanaki uku babu shi babu alamarsa�. . Tunda Hamid ya waigo ya ganta ya kasa koda kyafta idanunsa balle ya janye su daga kanta, girman da Saudat ta Kara da cikar jikinta shi ya fi . komai daukar hankalinsa, da kuma shigar alfarmar da ke jikinta. Ba komai bane a jikinta, illa wani tsadadden code lace dark blue mai ratsin fad-fad a jiki, dinkin riga da siket, kalar leshin ta dace da yanayin farar fatarta, don haka dinkin ya yi matukar kwantawa a jikinta. Yafi mayafin da ta yi Ya zauna kafadarta ya dace da ita, ya fito da sigarta ta nutsattsiyar budurwa. : Hamid ya lumshe idanunsa ya bude guda yana fadar, “Allah ya huci zuciyar Saudat, wai kin ga yadda kika ka koma kuwa?� � � � Saudat ta yi murmushi har da sunkuyawa ta zauna tana fuskantar katon teburin da aka qawata da kayan ciye-ciye dana sanyaya makoshi. ~ ~ � ' � Hamid ya durqusa a gabanta yana kallonta da idanunsa dake fallasa asirin zuciyarsa, ya kira sunanta . “Saudat, wallahi ina sonki, irin son da ba zai . misaltu ba, daidai da daqika guda ban taBa ' mancewa da keba a rayuwata, kina nan makale a zuciyata wallahi ranar da kuka zo gidanmu a ranar na bar Katsina na tafi Abuja, isowa ta ke nan wallahi. Saudat zuciyata ta gaza hakuri sai da nazo ki yarda da ni don Allah kyakkyawata". Dariya ceta kwace wa Saudat saboda ganin yadda duk Hamid din ya bi ya rude kamar wani zautaccce, shi ma ‘yar dariyar ya yi yana sosa qeya alamar ya danji kunya shi ma. A daidai nan ne kuma Dr. Ahmad ya sawo kai cikin falon da� yar siririyar sallamarsa, waddai ta makale amakoshi. * ' Saudat ta dago kanta a dan razane ta dubi ' inda yake Wani razanannen kallo ya watsa mata ta cikin siririn farin gilashin da ke manne a fuskarsa, Lokaci guda ya dauke kansa tamkar allah bai ajiye � Awajen ba, haka ya gifta su ya shige falon cikin gidan. Saudat ta sauke wani gwauron numfashi tare da maida hankalinta inda Hamid yake Murmushi ya sakar mata tareda fadar, . “Wannan shi ne abokin takarar tawa kenan?� Saudat ta sunkuyar da idanunta qasa tana dan wasa da bakin gyalenta don har ga Allah Hamid yana da muhimmanci a rayuwarta, duk da ta sani sarai ba za ta iya hada soyayyar Dr. Ahmad da ta kowa a zuciyarta ba. Hamid ya yunkura ya mike hannayensa zube a cikin aljihunsa yana kallonta da fararen idanunsa. Saudat ta yi qasa da idanunta ta kasa hada ido da Hamid din sai kawau ta tsinci kanta da jin matukar nauyinsa. Hamid ya yi wani malalacin murmushi Wanda ya tsaya iya labbansa kawai, muryarsa na dan sarqewa ya ce “Tsananin son da nake miki Saudat, da dumbin qaunarki da ke zuciyata ba zai ingiza ni ga take gaskiya ba. Saudat na yi miki rantsuwa da Allah ke ce kadai macen da na tabaa so a rayuwata, kuma haryau bana tunanin da akwai kwatankwacinki. A ranar da kuka zo gidanmu kuka ganni a ranar aka daura aurena da Kausar ‘yar qanin mahaifina 'Amma nasa qafa na bar Katsina zuwa Abuja� ban� sonta, banida muhallin da zan iya :ajiyeta a a zuciyata, tunda na. tafi sai jiya na dawo. A yanzu haka mahaifina ya yi fushi , , don haka mahaifiyata ta ba ni shawara na tafi Kaduna Wurin matata, wannan ne � kadai abin dazai Shirya tsakanina da mahaifina. Yanxu� haka tafiyar tawa ce zuwa Kadunan shine na kasa daurewa har sai na tsaya na ganki sannan na wuce. Saudat ba zan shiga haqqinki ba, idar har kin ji zaki iya aurena a yadda nake a � yanxu na ba ki sati daya ki yi shawara duk abin da � kika ”yanke zan dawo sai ki sanar dani�. �' Ba tareda ya tsaya sauraran abin da zata cebaa ya zaro ambulan daga cikin aljihunsa ya dora mata a hannu sannan , ya juya ya fice abinsa. Saudat ta mike jikinta a kasale ta � nufi qofar shiga babban falon gidan. Ba ta ankara ba sai dai ta ji sun yi karo yana qokarin fitowa ita tana qokarin shiga, ta yi saurin ja da baya tare da dafe goshi, kallo daya yayi mata ya Juya ya dauke kai da sauri ya raBa ta zai wuce. . Saudat ta yi saurin rufa masa baya tana ' kiransa baida alamar tsaya ba balle harya .sauraré ta hakan ya sa ta Kara da gudu~gudu ta , sha .gabansa. 'Don Allah ka tsaya ka saurareni Ta yi magar tamkar zata rusheda kuka. Dr. Ahmad yasa ya tsaya a gabanta yas‘hannayensa a aljihu tare da kafa mata ido. Saude ta langwabar da kai ' “Don Allah kar ka horar dain da fushinka, wallahi ba zan iya jurewa ba� . . Dr Ahmad ya watsa mata harara kafin yace“Idan har ni ban horar da zuciyarki da fushina ba, ai ke kya tarwatsa tawa zuciyar da masifar kishinki kauce ki bani hanya in wuce : Ya qarasa maganar tare da sa hannu yana ture ta daga gabansa Saudat ta Kara tokare hanyar cikin muryar ' son fashewa da kuka ta ce “Haba don Allah yallaBai, Yaya Hamid ne fa ba wani ba�. Dr. Ahmad ya qara watsa mata. wani kallo, “Okey, Yaya Hamid ne shi da yake ba namiji baneba k0? K0 kuma shi din ba sonki yake ba ko? Da Allah matsa bani wuri malama na wuce�. Wani irin qululu ya tokare zuciyarta ganin yadda ta ke rarrashinsa yana qars botsarewa. ta juya da hanzarinta tana sharar kwalla ta shiga ciki. Dr Ahmad yabita da idanunsa dukda � zafin da zuciyarsa keyi bai hana shi jin tausayinta ba, sai dai shi kansa bai san kalar zuciyar shiba da kishi yakan sa ya kasa sarrafa kansa ba yadda ya ' iya haka ya juya ya fice daga falon YAR. TALLAH CHAPTER30 Saudat'na Shiga falon taga Momy zaune hannunta rike da waya da alamar. magana ta gama tana shirin giftata. ta wuce, Momy ta rika , hannunta. saudat ta waigo da sauri tana kallonta, 'don haka ta dawo ta raBa ta zauna zuciyarta babu "dadi. , ~ Momy ta kira sunanta, “Saudat dan rigimar nan naki ba zai miki haqurin ki fara karatu ba, naga alamar rigimamme ne na gaske, don haka nayi tunanin a tsaida magana kawai in yaso ko a gidanki kya yi karatunki idan kina da rabo har gaba da sakandire sai ki wuce a gidanki don haka yanzu zabi yana wurin ki shin tsakanin Hamid da shi Ahmad din waye kike jin kina so a cikinsu� Saudat ta dago a sanyaye ta dubi Momy kafin ta ce, “Duk ina sonsu�. Momy tayi wata tatacciyar dariya ta ce, “To idan kina sonsu duka Saudat wa ki ke son aura A ciki kuma?� Saudat ta yi shiru zuciyarta naci gaba da ' harbawa, ta. sani sarai soyayyarta a yanzu tanaga � wurin Dr.� Ahmad, to amma ta juya wa Hamid baya � ' anya ta yi wa soyayyar da ya yi mata adalci? To shi kuma Dr din fa? � � � Momy ta katse mata tunanin da cewa . “Ki yi tunani da kyau Saudat, duka mutanen biyu duk suna qaunarki amma ni a nawa gamin Ahmad shi ne wanda ya cancanta ki aura, amma ki yi tunani da zuciyarki". Saudat ta dago kai tana kallon Momy zuciyarta na faman harbawa ta ce “Momy na zabi Dr din in har ke ma ya yi miki Momy ta dora hannu saman kafadarta ta dafa ta tana fadar, “Hakan shi yafi cancanta Saudat, tashi kije Allah ya yi miki albarka". Saudat ta amsa da, “Amin�. Sannan ta
Chapter 75 · 0% Book details