← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 90

Sashe 8

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lol kuma sance dani donjin yaddah laure da rabiu zasu kaya

Naku har kullum
Dboy
[1/12, 5:44 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[1/15, 6:40 PM] I love my mum: *YAR TALLA*

*CHAPTER 8*

Rama ya rike hannuwanta duka da ta yunkuro zata dokeshi sai ya tura hannun ta daki kanta, ya yi tayi mata dariya.
Sun shagala sosai kuma kana ganin suka san suna cikin nishadi ba su ankara ba sai dai suka jiyo muryar Laure na fadin
“Sannun ku ‘yan iska watsatstsu, taBarar ceta motsa kenan shi yasa aka shiga daka k0 jin kira ba ayi dakyau aikana qoqari gara kayi amankaka lashe abin ka, ka ga tuwanka manka kenan. Kuyi iskancin ku san ranku babu mai hana ku, ai dama barewa ba tayivgudu danta ya yi rarrafe ba gado kuki ai dama abun, kun tsotsa,ne ku yi sha’aninku kun ji.� Ta = saki labulan ta juya ta yi gaba. Rabi’u ya girgiza kai yana jin tamkar zuciyarsa
Zata fashe saboda bakin ciki, idan akwai abin da ke
daga masa hankali duniya ya dungunzuma masa lissafi to bai wuce a tuna masa abin da ya faru a * baya ba, wanda ke daga masa hankali ya dagula masa lissaii duk wata annashuwa ta shi take take Bacewa Ya jingina da bango yana kallon Saude ya jirkita ta kwanta jikinta a sanyayc. � Washe gari tunda safe Rabi’u ya yi jidar ruwansa gamida duk wasu aikace-aikace da ya san zai yi qarfe takwas daidai na safe ya sa kai ya fice abinsa b tare da ya fadawa kowa inda za shi ba.
Saude ta dauki taller wainarta ta tafi sarfiyar yau jikinta jinshi take babu dadi ko kadan da kyar ta samu ta iya saida wainar a hanya ma amai sau biyu tanayi harta samu ta iso gida da kyar, ta mikawa Inna Laure kudin tana neman faduwa, saboda juwar da ke
barazanar kayar da ita. Inna Laure ta zuba mata idanuwa cike da jin haushi kafin ta ce.
“Wannan lambon kuma na mene ne kl ke faman yi? Duk na kar ki dauki taller alalan ce k0 me?�
Saude ta girgiza mata kai alamar a’a tana nishi. Inna Laure ta ja tsaki tana fadin “To sai ki wuce ki dauka ga alalan can ta Murtala shida ce da goma
Saude ta langwaBe kai cike da jin jiki ta ce, “Ki yi hakuri don Allah Inna wallahi ban da lafiya bazan iya ba.�
Inna Laure ta waro ido waje tana fadin, “Uban me ki ka ce? Ni ki ke fadawa ba ki da lafiya Saude? To Allah yasa mutuwa ki kekina dawowa wallahi sai kin dauki tallar nan, ‘yar iska na lure kwanan nan wani tashan balagar tsuntsaye ce ke cin ki, kuma wallahi zan tatsiye miki ita tas za ki tafi ki dauka ki bani wuri k0 kuwa?�
Saude ta wuce tamkar wadda ta yi ciwon shekara goma ta dauka ta fice, tana tafiya tana hutawa k0 ta sule ba ta kai ga siyarwa ba ta zauna saman dakalin qofar wani gida tana faman kakarin amai numfashinta na fita sama-sma tun tana sanin inda
Har ya kai ta flta hayyacinta ta fadi can gefe sime.
Wani mutum da ke tahowa ta Iayin cikin shirin masallaci kasancewar yau Juma’a ce ya yo kanta a gigice ya jijjiga ta amma ba ta k0 motsi, kafin ka ceme mutane sun taru a kanta ana ta tambayar wanda ya san ta, amma babu saboda kullum dai ana ganinta
tana wucewa babu wanda zai ce ga daga unguwar da take tahowa, tun kafin a tafi masallaci har aka dawo sallar Juma’a, amma ba a samu wanda ya san unguwar su Saude ba.
Yamma liqis Rabi’u ya dawo daga wurin aikinsa ya yi dumu-dumu da yashi da suminti kana ganinsa kaga mai aikin Kasa, ya yi sallama ya shiga gidan. Laure da ke zaune a bakin rijiya ta dago tna kallonsa ya giftata zai wuce ta zabura ta mike ta cimimiyo rigarsa tana fadin
"Daga gidan uban wa ka ke dan iska tun safe ina gararin neman ka rumfa-rumfa ban gan ka ba daga ina kake?�
“Daga wurin aiki.� Ya ba ta amsa kai tsaye
Laure ta maimaita, ‘Aiki. Aiki fa ka ce? Eh lallai Wuyanka ya yi kwari wato harka san ka kakkare
Ka tafi wurin aiki, tabbas lallai wata rana sai ka
Shaqeni shi kenan jeka jeka kawai." Ta fada tana . murmushi
Rabi’u ya wuce dakin su kai tsaye ya cire rigar ya kwanta saboda gajiyardaya kwaso ga shi abinda ba ka sababa. A take bacci barawo ya sace shi, kiran salla ne ya farkar dashi
Ya tashi a gigice saboda rashin ganin Saude ya fita tsakar gidan amma batanan abinda batataBa ba yanufi kofar dakin laure ya duka daga bakin qofar muryarshi da alamun rudani yace, “Inna ko $aude tadawo?�
Laure ta watsa masa wani kallo kafin tace,“Ban saniba tana indata dawo da baka gantaba Ko kudice dazan Goyata?�
Gaban Rabi’u ya yi mummunar fad'uwa hankalinsa yayi masifar tashi.To inatake?
“Shin ba zaka tafi kanemota baneba zakatsaya kallon jama’a ne?� Muryar mahaifinsu ta katse masa dogon tunanin dayake ciki
Ya yunkura ya mike jikinsa asanyaye yafice.'shin ta inama zai fara neman nata ne? Wayyo Allah Ya Ubangiji kada kajarabeni da abinda bazan iya daukabaYaAllah kasa duk inda Saude take tana hannu nagari.
Abinda yake fada kenan azuciyarsa,yayanka yayi hanyar rewa
Tasha dukda yanada yaqinin zuwa yanxu an rufe tashar amman babu yaddah zaiyi yanashan kwanar layin nasu ya
Ci karo da jama’a wani na rungume da Saude wai za,a kaita gidan mai unguwa.
Hankalin Rabi'u ya yi masifar tashi ya tsare su yanavfadin qanwarsa ce su kai masa ‘yan tambayoyin da za su yi masa sannan suka ba shi ita ya nufo gida hankali tashe tun a hanya yake ta faman rusar kuka don shi duk a tunaninsa mutuwa ta yl.
, Yana shiga gidan ke Laure ta zabauro masa wai ina kayan tallarta, ita ta sana’aarta take ma. Wani_abu ya zowa Rabi’u iya wuya yanda ko kadan mahaifinsu bai damu da halin da Sauden ke ciki ba. Ya shimfideta a tsakar gida jikinsa na rawa ya nufi rijiya ya janyo ruwa ya shiga Sheqa mata, cikin ikon Allah ta farfado m har tana magana, ko motsin kirki ba ta yi, saidai sambatun datake tyi iri irin wanda ya zare hankali
Rabi’u yana kuka ya nufi dakin mahaifin nasu ya durqusa gabansa yana fadin, “Don Allah Baba ka ba ni kudi in kai ta asibiti ta farfado, amma ba ta motsi kada ta mutu.�
Malam Bala ya ce ‘Rabi� u ta mutu mana, ai ranta ba a hannuna yake ba, ban da ikon sanyawa ta rayu haka kuma banda ikon hanata kaxo sai wani rawar jiki kake akan ciwon d bai taka kara ya karyba
Don nasan baxai wuce bugun iskaba da masassara
Ka je ka kira Malam Maidala yaxo ya yi mata rukiya ga naira hamsin ka siyo panado ka bata ta sha.� Ya wurga masa kudin.
“Tashi ka tafi.�
Rabi’u ya mike yana jujjuya kudin a hannunsa wani sabon kuka ya Kara kwace masa ya sa kai ya fita, kamar yanda ya ce haka ya je ya kira Malamin yazo ya dubeta shida kan'shi yace ba iskabane zafin zazza6i ne, don haka a kai ta asibiti. Ya dawo ya sanar da mahaifin nasu, a lokaicn har ya kwanta. _
Don haka a fusace ya tashi yana fadar, Wai menene zaka dame ni da zarya shin wai nina dora mata ciwon ne k0 k0 me?�
Rabi� u yace, “Kayi hakuri Baba, Malam ya ce ciwonta na asibiti ne zazzaBi ne mai zafl.�
Yace ‘To shine har saika tadani ina baccina, tunda yafada maka zazzabine kaje katsinko ganyen dalbejiya kai mata surace mana, haba ban san matsawa wallahi.�
Rabi’u ya mike jiki a sanyaye hawaye na faman zarya a kuncinsa, tsanar mahaifin nasu ta qara mamaye masa zuciya gaba daya. A lokacin karfe sha daya na dare ne haka ya shiga dakin ya dauki Saude a kafada ya tafi chemist da ita.
A lokacin Bala mai allura� na' qoqarin rufe , chemist din nasa Rabi’u ya dube shi, ‘Don Allah
Malam Bala marar lafiya na kawo na ga kana kokarin tashi.�
Mal. Bala ya waigo yana kallonsa kafin ya ce, “Ashshal Waye ba shi da lafiyar?�
Ya ce ‘Wallahi Saude ce tun dazu zazzabi ya
kamata hadda su suma, yanzu haka k0 motsi bata ”yi
Bala mai chemist yace, “Ashsha! Ai kasan ni ban san sunansu na gaskiya ba, ‘Yar Baba k0 “Yar Tallar wacce cikinsu?�
Rabi’u ya' dan ja fasali kafin ya ce ‘Yar tallar dai�
Bala mai allura ya ce ‘Ikon Allah, saukota na ganta.� Rabi’u ya sauko ta yana nuna masa har a lokacin sambatun ta kawai take.
Bala mai chemist ya ce “Ai wannan zafin zazzbine wallahi maleria, wato zazzaBin cizon sauro, gaskiya Rabi’u ku gaggauta kai ta asibiti don Wannan ciwon bana zama bane hadari ne babba dole ana buKatar likitoci. kamar biyu zuwa uku a kanta.�.
Hankalin Rabi’u ya Kara masifar tashi ga shi bai ajiye ba, bai ba wani ajiya ba, nairarsa dari biyar ta aikin yau, ita kadai yasan ya mallaka sai hamsin dinda Baba ya ba shi. Ya dubi Bala mai allura yana fadar.
“Don Allah Malam idan da akwai taimakon da zakamin ka taimaka min ai mata kafin zuwa safe na
ga abin da Allah zai yi, amma wallahi yanzu ban da halin tafiya asibiti �
Bala mai allura ya ce‘Ai babu wani taimakon da zan iyayi yanzu anan nafada maka hatsarine a wurina na duba ta cikin wannan yanayi da take ciki.�
Rabi’u ya kifa kansa a ka Saude yasa wani irin kuka mai ban tausayi, ya zai yi da rayuwarsa tunda baidashi baidawada zai taimakamasa yana kallo rayuwar ‘yar uwarsa za ta salwanta, saboda kawai ba shi da shi... Kuka yake sosai.
Sosai kamar ransa zai fita

I will be back in no time

Via Dboy👍🏻
[1/15, 6:40 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/17, 7:43 AM] A A Dboy: *YAR TALLA*

*CHAPTER 9*
Chapter 8 · 0% Book details