← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 90

Sashe 48

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr yayi wani tsallen murna yana fadin kai thank u very much dad ya sumbaceshi kamar wani yaro momy tace “tunda dad dinka kadai ya siyi bakin don sai ta zage ta yi magana har sai mun ce ya isa haka. Dr. ya ce, ‘Wlh A a Saura ke Momy.� Dariya suka sa masa Momy ta ce ‘Ai kyauta ta tsakanina da ita ne babu mai ji bare ya gani.� ~ Dad ya ce, ‘Ai kuma bamu yarda da wannan wayon ba mu gani a qasa.� Momy ta ce, ‘Ai tsakanin ‘ya da uwa babu mai shiga don ni yanzu na bar maka wannan da baya girma yau na dawo nan. " Dad ya ce ‘Ba komai ai dama tare muke koya kaya kace my son?� Dr. ya ce ‘Ai k0 dai Dad fada mata mu dai mu gani a qasa ; Hajiya ta ce, ‘Hummm! Kan ku ake ji "Ta janyo hannun Saude tana saka mata wani zobe tare da abun hannunsa, sannan ta bude sarkar ta sanya mata da kanta ta cire mayafinta tasa mata yan kunnanyen Masu shegen kyau. * Dr ya kaure da tafi� yana fadar ‘Kai Mamy gaskiya baki ya siyu." Dad ya ce, ‘Sai ku taso muje mu yi lunch Gaba daya ba musu duka suka mike hannun momy sarqe dana Saudat, Dad kuwa yana dafe da kafadar Dr suka nuf1 dinning area A tare suka ci suka sha ana ta barkwanci basu suka bar gidan ba sai bayan sallar Magariba. Zuwa Saudat. gidansu Dr. Ahmad yau ya Kara mata darasi a rayuwa iyayensa sun nuna mata qauna tamkar zasu goya ta abin daya karayar mata da zuciya wanda ya sa ta kuka mai cin zuciya � Dr Ahmad da ke tuqi ya dago ya kalle ta kadan sai a lokacin ya lura da kukan da take ya maida kan shi saman. titi muryarshi a sanyaye ya ce, “Kukan me ki ke kuma?� Tamkar bazata tankamasaba, saidatayi dakyar ta iya tsayar da kukan nata kafin ta ce, ‘Dole ne inyi kuka Yallabai ta yanda kai , wa iyayenka qarya don kawai ka cimma wata manufa ta � ka, ni dama na sani tun fakro ka tsane ni kana san ka ‘kore ni amma ka rasa hanyar da zaka bi kar Hajiya ta bata ranta, amma ni da ka bi ta ni ba sai kabi ta wannan hanyar ba ta nuna kana sona ba, don hanya ce ta tarwatsa rayuwata wallahi, idan daga nan ka sauke ni ba za ka qara ganina a gidanka ba har abadan � abada" � Ta qarasa maganar tare da qara rushewa da wani sabon kukan � Dr ya taka birki tare da sauka daga saman Iitin ya . koma gefe ya_faka motar ya kunna fitilar dake cikin Motar ya jirkito yana kallonta gaba daya ya tattara duk _ wata nutsuwarsa a kanta, cikin sanyin muryarsa ya kira Sunanta. “Saude kenan wallahi tallahi tunda nake ban taba tunanin tarwatsa rayuwarki ba kullum fatana shine in ga rayuwarki ta inganta dubi idanuwana Saudat kalleni don Allah.� Ya fada. tare da riKo hannunta wanda ya tilasta mata kallon nasa. Tayi saurin sauke idanuwanta saboda wani irin kwarjinin dayi mata ga alamun damuwa nan bayyane kwayar idanunsa Dr yaci gaba da fadin “Ki kalle ni sosai Saudat idan har kin san abin da ake nufi da. so to zuciyata na dauke da dumbin soyayyarki da qaunarki', kuma duk abin da ki ka ji ina fada da gaske nake a shirye nake da auren ki a kowane Yanayi.� Saude ta yi saurin dagowa a razane tana kallon shi, tsabar rudu da kadauwar da ta yi ya yi bala’in firgitar da ita, a nutse yake kallonta ba tare da ya sake magana ba cak kukan Saude ya tsaya ta soma magana tana kallon tsabar idanuwansa, cike da kaduwa ga muryar har ta soma: disashewa saboda kukan da ta yi cikin sarqakKiyar murya ta soma fadar. “Dan Allah don Annabi ka rufa mini asiri kar ka Sake furta wannan kalmar wadda za ta. zamo makamin rugujewar rayuwata wallahi ka fi qarfina ta kowace fuska, kai ba sa an aurena bane karkama klsake fada" don Allah don Annabi." Dr. ya lumshe idanuwansa ya harde a tsanakke ya soma magana ‘Ba kya sona kenan Saude Juyo ki kalle ni ki fada mini ba kya sona, fadi kawai Saude ta ji tamkar yana buga lugudan tashin hankali a zuciyarta ta runtse idanuwanta tana jin tamkar zuciyarta za ta yi bindiga. Dr. ya sassauta murya tamkar mai shirin‘fashewa da kuka ya ce ‘Saudat wallahi ina son ki, so kuma irin na gaskiya wanda babu wasa a cikinsa, kuma wallahi a shirye nake da na fuskanci kowace 'irin jarabawa ce a kanki, ki amince min don Allah inamai tabbar miki ba za ki yi nadamar damqa mini zuciyarki ba. � Shi yasa na fara kai ki wurin� iyayena kafin in furta abin da ke zuciyata,� duk da ba su san wace ce ke ba, amma abun zai zo da sauki don gari na wayewa gobe zan mai da ke Katsina idan kuma kin amince na nemi auren ki � Cikin kuka Saude ta ce ‘Ta yaya zan mince in je fa rayuwata cikin matsala? Wace ce ni da zan iya kishi da matarka? ‘Yar wace ce ni a qasar nan da zan so miji kamar ka? Yallabai kafi karfina kai ba sa an aurena ba ne wallahi.� Dr ya ce‘Ni ba wannan na tambayeki ba Saudat ' shi aure sa a da sa a ne? Wa ya fada miki? Ai shi aure cancanta ce kawai, Kuma da ki ke maganar kishi da Asma, wace ce ita, ta isa ta hana abin da Allah ya� Qaddara. Saude nina ganki kuma nace ina so kuma mutum ko aljan bai isa ya. hana ni sonki ba har sai idan kece kika ce ba kya sona, kuma insha Allahu na san ba za ki fada ba, haka ne?� Ya yi maganar tare da matsar yatsun hannunta wadanda ke cikin hannunsa, Saude ta runtse idonta tana jin wani abu na yi mata kai komo a zuciya. To k0 shi ne son? Ta tambayi kanta. Dr. ya girgiza ta tare da fadar, ‘Bude idon ki Saudat ki kalli masoyin ki ki furta abin da ke � zuciyarki, shin kina sona za ki aure ni?� Shiru ya ratsa wurin ta kasa cewa uffan. Dr. cikin sarkewar murya ya ce, ‘Don Allah ki yi magana ki ce wani abu, please Saudat. � Kunya da nauyinsa suka dabaibaye ta ta samu ta duke da qyar kafin ta iya magana cikin wata likitacciyar murya ta ce, ‘To ka sake ni in fada.� � Da sauri ya saki hannun nata yana fadar, ‘Na saki fadi." Saudat ta dan yi jim tana tunanin abin da zai iya Zuwa ya dawo anan gaba don haka cikin raunanniyar muryana ta soma magana. “Yallabai ni ba sonka ne ba na yi ba, asali ma kai abun alfahari ne ga duk macen da ta same ka ballantana makaskanciya mai tsananin rauni. YallaBai zuciyata ce cike, da fargabar abin da zai iya zuwa ya dawo, wallahi ina tsoron tashin hankali ban son abin da zai sanya rayuwa ta damuwa ko ya yake.� Cikin farin ciki Dr. ya ce, ‘Haba Saudat ai matukar ina “ciki Kin gama zubar da hawayenki a kan damuwa, sai dai k0 hawayen soyayya wanda farin ciki ke sawa a � zubar dasu saboda shauki irin na soyayya.� Kuka da dariya suka kwacewa Saude Iokaci guda, ‘tasa tafin hannu ta rufe fuskarta, Dr. ya yi murmushi . tare da Juyawa ya yi wa motar key yasa mota hanya suka cigaba da tafiya » tare da waninsu ya sake magana ba. Horn din da ta ji yana wa maigadi shi ya tabbatar ~ mata sun iso Cinna hancin motar cikin gate din gidan ya yi daidai da bugawar zuciyar Sanue dif zuciyar ta ** tsaya da aiki a take. Ina ga k0 Asma ce za ta fito, Saude ta ji muryar Dr na fada wanda ba ta ma fahimtar me yake fada ba saboda tsabar rudu da kaduwa da take ciki. Saude ta runtse idanuwanta ganin Asma ta nufo motar tasu, Dr ya ji tamkar ya juya sai dai babu dama don kuwa tuni masu gadi sun riga sun rufe gate kuma k0 kafin su sake budewa ya tabbatar ta iso. . Don haka ya yi dabarar bude motar ba tare da ya gyara fakin ba ya fito yasa key ya kulle motar ya nufe ta tun kafin ta Karaso yana fadar “Saukar yaushe My dear.� ,, Turus ya ja ya tsaya saboda k0 kallon shi ba ta yiba ta wuce shi ta nufi wurin motar, gaban Dr ya yi wata masifaffiyar faduwa ba wai don yana tsoron Asma ba, a a saboda Saudat don ya lura ta yi matukar � 'firgita da ganin Asmar matuqa don haka Jikinsa a � sanyaye yabi bayan ta Tana qarasawa gaban motar ta ja ta tsaya ta miqawa Dr. hannu, ‘Bani key da motar." Ta fada cike da gadara. Dr. ya ja ya tsaya a gabanta cikin nuna halin ko’in kula ya ce, ‘Ba zan bayar ba kina da ajiya a ciki ne?� Cike da mamaki Asma ke kallonsa kafin ta iya bude baki ta ce, ‘ba zaka bayar ba ni ka ke fadawa haka Ahmad? Hmmm! Da kyau ba zan yi mamaki ba tunda ka dauki ‘yar iska kun flta kun gama yawan iskancinku kun dawo ai dole za ka sawa mota key tunda Allah ya toni asirinku. . Amma ka sani daga rana irin ta yau ka gama marmarin fita da kowace. karuwa don sai na sa ka yi nadamar da baza ta taBa qarewa ba wallahi, dan ba irin Asma ake wa irin wannan tozarcin da wulakantar ' ba a cikin gidanta, mayaudari, munafuki kawai.� Tana maganar tana kwance dankwalin kanta. Ta hau daura damara a qugunta tamkar mai shirin shiga filin dambe ta durkusa ta kwashi duwarwatsun da aka baza a harabar gidan ta hau jefa su a gilas din motar tana fadar. “Wallahi yau sai dai k0 ni ko ke a gidan nan ‘yar iska wallahi sai na yi ajalin ki, karuwar banza." Dr. da ke tsaye ya yi saurin rike ta yana fadar,
Chapter 48 · 0% Book details