← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 90

Sashe 2

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Inna laure ta kwasa a juge tana fadin na shiga uku ta isa
bakin randa ta ciko tasa da ruwa taxo ta sheqa mata gaba
gaba daya yarinyar ta firgita ta tashi tana fadar wayyo inna
kiyi haquri mai dan wake ta riqeta ke yi shiru da allah aita
kyaleki
Inna laure ta sauke wani nannauyen numfashi ta shiga zare
na mujiya
Mai dan wake ta miqe tana fadin ni na tafi amman dan allah
laure ki dinga kula kisan irin dukan da zaki dinga musu don
karkije ki daure kanki da kanki
Inna laure ta sake jan kwaron numfashi kafin tace insha
allahu zan kiyaye mai dan wake ta fice abinta
Laure ta juya ta shige dakinta ta barsu a nan
Saude ta rarrafa ta nufi dan uwan nata
Wanda ke zaune ya hada kai da gwiwa yanata faman kuka
Saude ta raba jikinsa ta kwanta ya qara janta a jikinsa
sosai
Bata jima da kwanciyaba barci ya dauketa sai faman jan
ajiyar zuciya take
Akai akai
Malam bala yayi sallama ya shigo gidan nasa hannunsa
saqale dana iklima yarinyar da bazata wuce yar shekara
goma sha daya ba
Qanwar saude ce don ita yanxu tana shekara sha biyu ne a
duniya
Malam bala ya shigo tsakar gidan tare da miqama iklima
baqar ledar dake hannunsa ta karba ta shige dakin
mahaifiyarta tana tsallen murna
Malam bala ya kalli rabiu fuskarsa ba yabo ba fallasa yace
bakin munafiki kallon uwar me kakemin? Me mugun halin
tsiya hala wani abun kukai aka dakeku ko?
Inna laure ta hankado labule ta fito kamar an bankadota ai
daman jiranka nake malam wallahi yau saika biyani kudina
in dorama yarinyarnan tallah ta boye kudin wai tace an
kwace
Na rantse da allah ban daukar asara
Malam bala yace ai daman tunda na gansu zazzaune anan
nasan wata ta'asar sukayi
Yan iskan yara masu tsinannan hali wanda sukai gadon
Halin tsiya niko yarannan dada inda zan kai
Su wallahi dana kaisu na huta da bala,in su
Tace ahto nidai kudinane sai an biyani
Babu mai doramin asara alalata ta murtala biyuce da goma
Malam bala yace toya zanyi ai dole na biyaki tunda allah ya
hadani da jarababbun yaya
Kiyi haquri idan na dawo daga kasuwa gobe saina biyaki
miqomin buta nayi alwala
Laure taja kwafa ta juya ta koma dakinta ta dauko masa
butan ya nufi bayan gida
Ta watsama rabiu harara sannan ta wuce dakinta ta samu
iklima ta zazzage baqar ledar sai diban kilishinta takeyi
Ta miqa hannu zata dauka yar tasa kuka tana tirje tirjen
qafafuwa inna laure tayi saurin ajiyewa
Ga abinkinan sarkin rigima. Ai nasandai duk cinki baki iya
cinye wannan kilishin
Yarinyar ta turo baki irin na shaqwababbun yaya taci gaba
tacin abinta
Duhun magaribane ya fara ketowa sauro suka fara duduma
a jikin rabiu ya lallaba ya kwantar da saude saman siminti
Ya lallaba ya nufi dan akurkin dakinsu ya shinfida musu yar
yagalgalallan tabarman kaba irin mai cin jikinnan
Sannan ya dawo ya lallaba ya dauketa da qar
Ya kaita dakin ya kwantar da ita ita kadai ta mamaye
tabarman don haka shi saman simintin dakin ya kwanta
babu ko filo balle abun rufa
Ga duhun dakin. Ya runtse idanunsa dukda yanada yakinin
yunwace ke kwankwasarsa bazata barshi yayi barci ba
Tunanin mahaifiyarsu ya fado masa kamar yaddah kullun
yakeyi kafin ya kwanta
Wasu hawaye suka cika masa idanu masu zafi tabbas
yasan wahalar da sukesha somon tabice
Akan wanda mahaifiyarsu tasha a gurin mahaifinsu
Nasiharta gareshi itace ta dawo masa tamkar yanxu take
masa su tace
Rabiu don allah don annabi ko bayan raina. Ka kula da
rayuwar qanwarka karkabar rayuwarta ta gurbata a duk
halin da kuka tsinci kanku a ciki kaga ita mace ce dole tana
buqatar taimakon wani wanda zai jibanci lamarinta
Nasan kaima kana buqatar taimako amman a duk yanda
rayuwa taxo rabiu yinta ake
Nasan kodani ko bani dole ku rayu bakuda mataimaki sai
allah.
Rabiu kuyitayimin addu,a in rayu kodan saboda ku. Nima
inason in rayu sbd ku
Baisan sanda kuka ya kwace masa ba saida yaji saude
jikinsa tana jijjigashi.
Tace yaya kuka kake?
Yayi saurin hadiye kukan tare da goge hawayensa
Ya lalubo hannunta ya riqe kafin yace ba kuka nakeba
dariyace nake na tadaki ko?
Tace a,a yaya yinwa nakeji cikina sai cixona yakeyi tun safe
banci komaiba na tafi tallah har yanxu
Ya salam ya fada a fili sbd rashin sanin abinyi
Saude ta kwantar da kanta a kan cinyarshi tace kaji cikina
sai kuka yake ko yaya?
Bai tanka mataba ta qara girgizashi cikin muryar kuka tace
yaya abinci zanci
Rabiu ya kwantar da murya yace dakinyi haquri kin kwanta
kinga da safe ba saiki karya ba
Tace wlh bazan iya barciba yace to lallaba ki kwanta ina
xuwa
Ta zame daga jikin nasa sai shi kuma ya miqe ya fita
Duk suna kwakkwance a tsakar gida cikin gidan sauro sbd
lokacin zafine
Sai radio ce keta faman babatunta a banza
Rabiu ya lallaba sadab sadab ya isa har inda suke ya dauko
langar fura ya lallabo ya shigo
Dakin ya zauna yana fadin tashi saude ga fura na samo
miki kisha
Ta tashi da hanzarinta ya lalubo bakinta ya kafa mata
langar furar tasha iya shanta sannan shima yasha kadan ya
rage sauran ya lallaba ya tafi don mayarwa
Yana qoqarin ajewa kenan iklima ta farka tana fadin laure
zansha fura
Rabiu yai saurin durkusawa a wurin jikinsa nata faman bari
Inna laure ta tashi tana haska fitila da niyyar dauko langar
furar
Taga mutum a durkushe wuri guda
Ta fasa wani uban ihu wayyo allah malam baraw barawo
Malam ya tashi a firgice ya rarimo adda yana ina yana ina ?
Kafin ya fito daga ciikin gidan sauron rabiu ya kwasa a guje
yayi dakinsu yana famar rawar jiki
Malam ya fito yana ina barawon yake laure?
Tana rawar murya tace nan nan na ganshi duqe wlh
Malam bala yaja tsaki to idan nan kika ganshi yana ina ?
A,a ka. Haska mana ya dauko touc light ya tafi yana
haskawa har zuwa zaure ya dawo yana fadin kedinnan
Wallahi kinada matsala. Yanxu haka inuwa wani tsuntsun
kika gani kinxo kin rikita mutane da wani barawo
Laure tace malam nifa mutun na gani anan duqe
Yace to idan da mutum kika gani da ban ganshiba ko laya
yayi ya bata? Don allah ki koma ki kwanta kinji
Laure tace niko malam wlh bazan iya rintsawa ba don da
idona naga mutum nan tsugunne
Malam bala ya shige gidan sauransa yana fadin ai saikiyita
zama ke kadai
Sai a lokacin hankalin rabiu ya kwanta ya saki wata ajiyar
zuciya ya lallaba ya kwanta abinsa
Bai jima da kwanciya ba bacci barawo ya sacesa
Qarshe shida na safe laure ta hankado kofar dakin nasu ta
gansu sai sharar barcinsu kawai sukeyi wani takaici ya
kamata ta juya ta debo ruwa cikin kwanon sha ta daga
labulen ta sheqa musu a firgice duk suka tashi sukai wuqi
wuqi kamar ya,yan zakaru
Inna laure ta taba baki cikin masifa tace
Hmmmmm
Ya labarin
[1/7, 5:49 PM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/8, 4:40 PM] I love my mum: *YAR TALLA*

*CHAPTER 3*
Chapter 2 · 0% Book details