← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 90

Sashe 53

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saude ta sulale qasa tana wani gunji mai kama da. gurnani ji ta ke numfashinta na sama‘sama kamar zai dauke, ta rushe da Wani irin kuka mai daga hankali, ta zabura ta yo waje tamkar marar hankali ta tSallake mutanen dake waje da gudunta. Tana jin mahaifinta na Kwalla mara kira, amma ba ta tsaya ba Dr wanda ya gaji da zama a motar ya fito ya jingina da motar yana lallatsa wayarsa ya ganta ta fito a guje,hankalinsa ya yi � masifar tashi ya nufe ta yana KoKarin rike ta, ta durkushe a gabansa tana wani irin gunjin kuka. Dr ya rikice cikin tsananin rudani ya rike ta yana fadar, “Me ya faru ne Saudat? Waye ya rasu ne? ki fada min." Saude ta Kara rushewa da wani kukan ba � tare data :saurara ba ta shiga qokarin fadar, “Na mutu... .“mutu , na lalace. yallaBai * an d‘aura min aure da Garba . “Innalillahi wa" inna ilaihi raji �"un Abin� da Dr Ahmad ya iya fada kenan tare da juyawa ya kifa kansa saman motar gabad'aya ya ma rasa a wace duniya yake Malam bala ya qaraso da hazarinsa yana fadar keko wannan diya allah ya wadaran halinki yanxu sbd dibar albarka shine zaki kwaso a guje kina ihu kamar wata tabin iska shin ba,a gaya miki yanxu muryarki al,aura baceba iyee? Sauce najin abinda ya fada ta sake rushewa da kuka tana fadar wayyo allah na shiga uku na lalace malam bala ya dauki sallallami kafin yace anya saude da hakalinki kuwa yanxu budewar idon taki taki har takai kiyo waje kina kururuwa? To maza tashi ki shiga ciki mutuniyar banza mara mutunci zaki tashi ki wuce ko saina jefeki Saude ta tashi da sauri ganin yana niyyar jefeta da wani hogen daya rarumo ta fada cikin gida tana kuka sai a lokacin Dr ya dago idanuwansa da suka kada sukai jajir cikin dasashshiyar murya yace kayi haquri baba don allah inason magana dakai Malam bala yace Ohoo daman kaine mai hure mata kunnen? , . Dr. ya girgiza masa .kai, yana jin zuciyarsa tamkar zata ballo ta fito ya ce,� “K0 daya ni dai ne wanda ta ke aiki a ' gidana, inda aka kai ta aiki" Malam Bala ya ce “Auho, to bismillsh mu shiga daga soro ai ban fahinta ba, mu shiga in kira maka innar tasu ku gaisa'Ba musu Dr. ya bi shi~suka shiga cikin soron gidan, sannan Malam Bala ya shiga cikin gidan ya sa Inna Lami qanwarsa uwa, daya uba daya ya ce ta kira masa Laure ta taho kuma da tabarma Yana tsaye ta shiga ta fito masa da tabarma tare da fadar, “Lauren tana zuwa" � � Malam Bala ya, juya ya dawo ya � shimfida masa tabarma suka zauna, Dr, ya dubi Malam Bala suka gaisa sosai cikin girmamawa Sannan Dr ya qara gabatar da kansa Baba nine wanda Saude ke aiki a gidana, na maido ta. ne saboda wani muhimmin abu wanda maganar aurenta da ta sanar ds ni a «yanzu ya tarwatsa komai amma Baba kayi haquri da abin da zan fada maka a yanzu kai _ masa kyakkyawan kalla da kuma, kyakkyawar � . fahimta Baba kai ka haifi Saudat ka fi kowa sonta, kafi kowa sanin ciwonta, kuma amana ce a gare ku abin tambaya a gobe kiyama idan ku ka cutar da ita ku ka wofintar da rayuwarta wallahi sai Allah ya kama ku a kan hakan duk dakuwa kukukahaife ta. ' Baba, Saudat tana da masu sonta da aure a nan garin, da kuma ni kaina, sannan Saudat yarinya ce qarama Baba bai kamata ku_ tankWare rayuwarta ku zaba mata mijin da bai cancanta da ita ba don kawai saboda, wani dalili naku ka yi haquri Baba na san kuna da hakkin zaba mata mijin da ya yi muku, amma Baba� zaba " mata mijin da ya� dace da rayuwarta don Allah don Annabi Baba ka dubu girman Allah ka yi wa rayuwar yarinyar nan adalci ' Tunda Malam Bala ya sadda kansa bai dago ba, komai yake tunani oho! Inna Lame � wadda take labe a tsaye hannunta dafe da kofa . tana sauraren duk bayanan Dr. tace, “To muna godiya Alaramma, Allah ya biya. Sai a tashi a tafi umma ta gaida assha, kuma abin da . :ka yiwa "yarmu Allah ya sa ayi wa taka, mun . kai diya aiki ka hure mata kunne ka lalatata ka maida mana, ka iske kuma za a yi mata aure kana Kokarin hanawa kai shaida, saboda dandin bai iske ka ba? To ta fada mana komai, kuma ba abin da za muce maka sai mu ce ka je Allah Ubangiji ya yi mana sakayya". Dr Ahmad wanda ya ji maganganun tamkar: saukar markade, ya dago da sauri yana kallonta cike da mamakin maganganunta ya Kasa cewa komai, su Malam Bala ne ya Daga kai yana fad'a, “Ya Isa haka Laure, koma cikin gida don Allah� Inna Laure ta ce, “Ka bar ni da wannan� babbab shaidanin mai munafurcin kashe aure ya maida mana diya karuwa, kuma saboda rashin imani ya biyo ta har gida ya ce kar a yi mata aure� tunda bai gaji da lalatar ba. Malam ka kalli Saude sosai na rantse maka da Allah cikine daita�. ldanuwan Malam suka yo warwaje * saboda tsabar dukan da maganar tata tai masa a Kirjinsa. Cikin rudu ya mike yana fadar“Laure ki shiga gida haka wuce ki tafi� Ganin maganganun nata sun yi tasiri a zuciyar Malam yasa ta juya tana matsar kwalla a munafurce ta gefe tana kallonsa � Malam ya dubi Dr. Ahmad zuciyarsa na huci yace “Malam mun gode kwarai amma don Allah ina rokonka ka tashi ka tafi don Allah�. . Dr ya danne mamakin da ya cika masa zuciya, cikin qarfin hali ya bude baki da niyyar yin magana. Malam ya daga masa hannu cikin tsananin fushi ya ce. “Babu abin da za ka fada don Allah don Annabi ka tashi ka fita ko na samu zuciyata ta sassauta�. � Dr. ya mike tsaye cikin halin jarumtaka, don gabadaya zuciyarsa' rugurguza ‘ta ,ke tamkar za ta Balle Kirjinsa ta fito fili. Ya danne abin da ke yunkuro masa kafin ya iya Karfin halin fadar “Ka yi hakuri Baba, wallahi tallahi na rantse maka da Allah ban aikata abin da kuke zargina da aikatawa,ba kuma na amince zan tafi amma don Allah ka bani minti biyu in magana da Saudat a gabanka Malam ya zabum masa “Kai Malam ka ga ka bar nan tun muna shaida juna, don wallahi Saude ba za ta sake fitowa ba sai idan za,a tafi da ita dakinta, ka ji na gaya maka". Dr Ahmad yaji tamkar anwatsa masa tafasassan ruwan zafi mai qona zuciya. Ya lumshe idanuwansa yana jin tamkar mala’ikan mutuwa ya taho ya zare masa ransa koya� huta, ya bude idanuwansa da kyar ‘wadanda suka ida rikicewa ba ka ganinkomai � cikin shi sai tsananin ja tamkar garwashin wuta. Ya zura hannunsa cikin aljihu ya zaro ' gabadayan canjin da suka yi masa saura, yasan bazasu haura dubu hamsin ba, ya ajiye a kasa ' tare da fadar kayi hakuri a bata wannan canjin insha l Allahu ko tana gidanta ne zan yi mata aike� Ya juya ya fice yana kokarin dauke kWallar da ke neman~zuraro masa . Malam ya duka ya dauki kwalin yana . faman juyawa a hannunsa, Laure da ke labe tana jiran ta ji yadda zasu qare ta zabura ta yo ' c'iki'n soron ta yi caraf da kudin tana fadar yauwa "‘KaWo su nan Malam". � Shi hatta ma ba shi tsoro ya sakar mata ~ ya tsaya yana kallonta, ta soke a zani tana . fadar “Allah ya ga tsimurmular da muke muna ta fama da Tv Stand ba kayan kallo yanZu k0 ka ga wad‘annan sai a siyo ma ‘yar baba irin wannan talabijin din wadda ake lika wa jikin bango da � kafet din tsakiyar daki su kadai ne dama ba a siya ba� . Malam Bala ya ce“Haba Laure, yarinyar nan ita aka ba wa kudin nan, kuma kina sane daga katifa da zanin gado da labule babu abin da aka sai mata, yanzu wadannan ba ' sai a Kara a sai wani abun ba?� Inna Laure ta ce, “Haba Malam ka sani fa sarai irin mutumin da ‘yarbaba ta aura, dan masu da shi fa dan gidan hali, ne za su rike; mana ita da mutunci? Ita ko Saude Garba ne fa ka sanni na sanka, kar ce ta san kar to mu wahalar da :kanmu na me? Dakunan fa naji ‘yan jere na fadar daki daya ne ya ware mata mai girma, to me za mu zuba a cikin daki daya? Ai da ma Dan gado ne da katifa toga katifar nan ko zuwa gaba ai: idan Allah ya hore ai sai mu yi mata gadon k0 ya ka ce Malam�?" � Malam Bala ya ce, “Shikenan aje a yi k0 ma . � me za a yi. ni dai na rabu da yaran nan lafiya nan da awa daya za a wuce da su gidan Yaya Maje�. . � Laure ta amsa da, “An gama Malam ’Sannan ta juya ta nufl cikin gidan ta bar shi yana kwashe tabarma. Tunda Dr Ahmad ya fita ya fada , motarsa ya kifa kansa saman sitiyarin motar bai sake dagowa ba,» duniyar gabadaya «ta shiga juya masa, ya rinka jin tamkar ana sa guduma ana sassaka masa kirji Ya dauki tsawon lokaci a kife tamkar matacce jijiyoyin kansa suka tattashi rado rado abunka ga jar fata, kamar an zana su, wani irin ciwonkai mai zafi ya sauko masa, ya. dagO� kansa da Kyar wanda ya ke jin ya yi masa bala’in nauyi ya mika hannunsa a kwabar jikin .motar ya dauko biro da takarda ya yi wani dan rubutu layi biyu ba tare da ya flta ba, ya kira yaro cikin dasasshiyar muryarsa ya ce, “Ka san Saude?" � "� .Yaron yace, “Yar talla, wadda ku ka zo yanzu tare? Dr». ya ce, ‘Ita don Allah karBi ka kai mata, ka tabbatar ka ba ta hannunka da nata, kar fa ka ba wa kowa kaji?� ' Yaron ya amsa da, “To".
Chapter 53 · 0% Book details