← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 90

Sashe 41

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gari da safe Saude ta tafl Bangaren Dr. Ahmad babu kowa a falon nasa don haka ta zage ta shiga aikace- aikacenta qarfe goma daidai ya sauko daga samansa yana sanye da jallabiya sabuwa ruwan toka mai hade da hularta Suna hada ido da Saude ya yi saurin qarasa saukowa daga matattakalar yana fadar, “Zo. nan Saudat." * A hankali ta dago ta kalle shi tare da gaishe shi cikin girmamawa kamar yanda ta saba. Ya amsa' a tsanake sannan ya jefo mata tambayar da ta sanya ta saurin dagowa tana kallonsa, ya qara‘gyara tsayuwarsa tare da maimaita mata tambayar. “Na ce laflya ba ki bude kyautar da nayi miki ba Ko baki iya bane?� Ya karasa maganar cike da tuhuma. ; Saude ta dukar da kanta tana kallon kafet din dakin cikin nutsuwa ta soma magana. “Kayi haquri Yallabai ba wai ban yaba ba ne kawai dai na ga kyautar ba ta cancanta dani bane shine yasa nayi' tunanin maido maka, amma ka yi hakuri Dr. Yayi wani takaitaccen murmushi tare da zama saman hannun kujera ya zauna yana kallonta a nutse kafin ya ce ‘Dama ita kyauta cancanta ce ke sawa ayita idan kuwa cancanta ce to ke kuw kin ' wuce wadda a kai miki kinfi qarfin hakan. Kuma idanma ba ki sani ba ina so yau ki sani dangantakata dake tamkar hannu da ido ne yanzu sannu a hankali zan shafe hawayen da ke kwaranya daga idanuwanki insha Allahu sai na wanzar da dariya a idanuwan dake ta zubar hawaye, kin fahimta?� Saude ta girgiza masa kai tana fadar, ‘A’a Yallabai yin hakan yana nufin zaka tsamo ni daga rijiya ka jefa ni kogi ne Yallabai ka yi tunani zan iya shiga matsala wajen Hajiya, na tabbatar idan ta samu labarin kudirin da kake nufo ni da shi zata dauki kowane irin mataki a kaina, Dr Ahmad ya kada mata kai yana fadar, 'Ko kusa Saudat babu wandu ya isu ya yi wu mutum ”abinda Allah bai masa ba haushin me Asmu za ta ji don kawai ina kokarin taimaka miki meye abin da zai tunzura ta a ciki? Ni ban ganshi ba, kuma koma akwai ba zai dame ni ba, zan yi Kokari har sai na sauke alkawarin da na dauka.� Idon Saude ya ciko da hawaye cikin muryar kuka ta ce, ‘Na san ba zai dame ka ba YallaBai amma ni zai dame ni, wata qila ma ya zamo silar barina duniyar gaba daya. � Dr. Ahmad ya ce, ‘Hakan ma ba za ta kasancewa ba Saudat ki daina ma fada.� Saude ta ce, ‘Idan ya kasance fa?� Shiru ya yi yana kallonta Saude ta yunkura ta mike hawayen da suka ciko daga idanuwanta suka samu damar zubowa cikin kuka ta ce, ‘Zan bar gidan nan dole zan bar shi, dan ina tsoron abin da zuciyata ke hangowa ina jiyewa kaina, dan idan ma wani abu ya same ni babu wanda Zai yi kukan rashina, babu ba ni da shi.... Kuka ya ci Karfinta sosai. Dr. Ahmad ya yunkura ya zagayo ta gabanta yana kallonta cikin sanyayyar muryar shi ya soma magana. ‘Duk inda ki ka nufa a fadin duniyarnan sai na nemo ki, babu inda za ki shiga ki layance min. Ina tare da ke Saudat har: sai na ga kin yi dariya sai na ga rayuwarki ta inganta kin samu farin ciki mai dorewa na yi wa kaina wannan alkawarin kuma zan cika shi ko da hakan yana nufin rasa komai na a rayuwata.� Saude ta yi saurin juyawa tana kallonsa ya daga� mata kai yana fadar, "Tabbas kisa ido kiyi kalio.� ‘Ya juya a sukwane ya fICe daga falon ya bar ta nan tana kallon qofar da ya fita. Wani irin kuka ya zo mata, tsoronta daya a duniyar nan matarsa Asma; don ta san ba lallai bane ta yi musu kyakkyawar .zargi ba, tana tsoron ta yi musu mummunan zargin da zai‘sa ta yanke mata hukunci daidai da zarginta. Saude ta Kara rushewa da kuka don har ta hango irin bala� in da za ta iya fuskanta Haka ta karasa aikinta tas ta bro Bangaren nasa, yinin yau haka ta yi sa a kwance. Da daddare kuma Hamid ya kira ta ya Kara caza mata Kwakwalwa. “Wai Saudat me ke damun ki ne shin k0 kin mance da yau saura sati uku auren ki? Na lura hankalin ki kwance yake tun yaushe nake fama da ke kina gocewa. Saudat idan harkin soma san Garba ne ki fad'a mini in fidda raina kawai, amma don me za ‘ki ta yi min yawo da hankali ki ce yau ki ce goba, idan kin san ba zaki iya fitowa daga gidan ba ki 'fad'a mini ni in zo da kaina in dauke‘ki.� 'Saudat ta ja numfashi ba ta taba tunanin ya iya bude wuta haka ba, ta ma rasa ta indaza ta fara, don . haka ta kwantar da murya ta ba shi hakuri tare da yin . masa alkawarin duk rintsi gobe za ta gudu ta bare � Abujar. » , Abun duniya duk ya ishi Saude tunaninta daya yanzu hanyar da za ta bi ta bar. gidan ga YallaBai yana nema ya taso ta gaba tsoronta daya ma yanzu kar ya ruguza mata al’amuran ta, wannan tunanin ne ya hana Saude barci da wuri sai kusan biyu da wani abu na dare ta kwanta, don sai da ta harhada kayanta tsab na barin garin. . Sallar Asuba ma da kyar ta iya yin ta saboda baccin da yaci qarfinta. A kan sallayar ma wani sabon baccin ya sake dauke ta. Ba ita ta farka ba sai qarfe sha daya da mintina. Ita kanta ta yi mamakin tsawon lokacin da ta dauka tana bacci, don haka ta mike da hanzarinta za ta shiga bandaki ta ji kukan wayarta, don haka ta dawo ta dauka. ' Tun kafin ta qarasa sallamar ya katse ta ta hanyar fadar, ‘To yaya kin taho k0 kuwa yanzun ma ba ki samu damar ba? . Saude ta sauke numfashi tare da fadar, ‘Nina fada maka Yaya Hamid insha Allahu yau zan bar gidan nan duk rintsi, saboda ni kaina nafi ka kaguwa dana bar gidan nan don Allah ka kwantar da hankalin ka insha Allahu babu abin da zai faru.� Ya ce, ‘Hmm! Saudat kenan na lura ba ki san irin son da nake miki ba shi yasa har kike fadar kar in damu wallahi yanzu kasancewa ta da ke ne kawai zai ba ni farin ciki a rayuwata, don Allah Saudat kada ki ci gaba da nisanta kan ki dani please; � Tausayinsa ya kama ta ita kanta ta soma jin irin yanda yakeji yanzu don haka cikin sanyin murya ta ce, “Kayi hakuri Yaya Hamid ni kaina. ina jin yanda kake ji a yanzu, kuma nan da wasu ‘yan awanni zan maka kyakkyawan albishir.� . Hamid ya ce Allah yasa ki gaggauta kin ji?� ’lnsha Allahu.� Ta ce cikin sanyin murya, sannan ta. kashe wayar ta mike da nufin maida ta wurinta, zuciyarta ta yi. wata mummunar bugawa. A tsaye yake jikin qofar ya harde hannuwansa a kirji ya tura mata idanuwansa da ke sanye cikin farin gilas gaba daya ya tattara duk wata nutsuwarsa a kan Saudat ta ji.tamkar ta kurma ihu saboda tsaba: tsor da kaduwa duk ta dabarbarce,. , Dr. Ahmad ya take a hankali har zuwa gabanta ya mika: mata hannu, “Ba ni wayar.� Ba musu ta miqa� masa wayar hannunta na rawa. Ya ce, ‘miqo min har da waccan da na baki.� Jikinta na faman bari ta juya ta dauko masa, ya karba kawai ya juya ya fiCe abinsa ba tare da ya ce da ita komai ba Saude ta fada saman gadon jagwab kamar an zuba kayan wanki har wata zufa ke tsatstsafo mata, ta daura hannu a kai .Wayyo Allah na! Ya Ubangiji gani gare� ka , Asma. ta fado kamar an an jefo ta, ' ' Saude ta Zabura ta miqe a tsorace tana kallonta, Ta tsaya tana watsa mata wani malalacin kallo. Saude ta durqushe a gun, tsantsar firgici ta bayyana a fuskarta bakinta sai kyarma yake wurin fadin ‘In...ina... ina wuni Asma ta tabe baki tare da jan wani dogon tsaki, ta shiga zagaye dakin tamkar mai neman wani abu ta kai ta kawo ta kai ta kawo, ta dinga binciken ta sai data gaji sannanta juyatafice batare datace uffan ‘ba. Saude ta yi suman tsaye, me keson faruwa ne da ita ne? Ta yi masifar firgita, ita dai ta san ta shiga . tsaka mai ‘wuya, don da za a auna ta a lokacin babu abin da zai hana a tabbatar da hawan jininta, kukan ma ya gagare ta sai muzurai kawai take yi. ' Wasa-wasa lokaci ya soma tafiya tana nan zaune, � tabbas idan ta yi wasa lokaci zai qure mata, don gangar jikinta ce kawai zaune a gun amma zuciyarta na wurin Dr. Ahmad. Qokon ta daya Allah yasa ya yanke mata hukuncin da za ta iya dauka. Wasa-wasa ta lurawankin hula zai iyakaita dare,don hakata yanke shawarar tashi ta je ta ba shi hakuri, ba yanda ta iya haka ta lalalBa ta mike: jikinta amace ta nufi Gangaren nasa. Sallamar da take shirin yi ta makale a makogoranta, tsaye yake goye da hannayensa a baya wadanda ke rike da wayoyin da ya karba wajenta, duk da bayansa take saboda ya bada baya, amma hakan bai hana ta fahaimci yana cikin yanayi marar dadi ba, tsoronta ya qaru matuka tana fargabar ya yi mata mummunan zargi. Jin shigowarta yasa Dr. juyawa a hankali yana kallonta da jajayen idanuwansa ba tare da ya ce mata kala ba. Saude ta durkusa a gabansa muryarta a sanyayc ta ce ‘Don Allah ka yi hakuri Yalla6ai wallahi ba... Dr. ya yi saurin daga mata hannu alamar ta dakata, ya yi taku daya zuwa uku ya matso gabanta cikin razananniyar muryarsa wadda ke fita a hankali ya fara magana. “In yi hakuri laifin me ki ka yi min? Kina tunanin raina ya baci ne don na kama ki kina kula maza?� Ya girgiza kai. “K0 daya Saudat ko a jikina, ko da kuwa duk mazan duniyar nan samarinn ki neba zai rage ni da � komai
Chapter 41 · 0% Book details