Sashe 74
Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tayi maganar tana nuna saude inna laure ta fadi qasa jabar kamar an tile kayan wanki tana kwalama malam bala kira malam bala ya fito daga kewaye a gigice hannunsa riqe da buta yana fadin kai laure wannan irin ihu haka ai saikisa juwa ta kwasheni in fadi babu gaira babu dalili Inna laure ta dinga nuna masa momy tana fadin malam dubamin ka gani wacece nake gani kamar maria Cikinfirgici malam bala ya siki butar ta fadi facal yayo kansu yana fadin wacce mariyar kike nufi ‘YAR TALLA- BOOK4 CHAPTER29 ZUciyar Saudat ta shiga duniyar tunani da sake- sake ganin al’amuran ta ke tamkar a cikin mafarkinta suke faruwa, kuma har yanzu ba ta fidda rai ba da za ta farka a kowane ba lokaci. Minti sha biyar ya kawo su har kofar gidan Malam Bala, inda Saude ke nuna masa hanya har suka iso, ya faka motarsa a qofar tsohon gidan. Dukkansu suka fito suka nufi gidan, Saudat na rike da hannun Nabila, Shukura na gefenta, sai Nabil a gefen Momy, Alhaji Ashiru ya zauna ya jira su a mota. Sallamar da suke ce ta janyo hankalin Inna Laure da ke quryardaki tana tattara komatsai, ta yo tsakar 'gidan tana fadar, “Marabanku; sannunku da...� Turus taja ta tsaya tare da dafe qirji cikin tsananin tashin hankali da kyarmar murya ta soma fadar. “Su wayr ku, daga ina?� Momy ta gyara tsayuwa kafin tace “Ikon Allah abin da mamaki, idan ni ba ki gane ni ba, ai ina tunanin wannan ‘yarki cr kya gane ta?� Ta yi maganar tana nuna Saudat. Inna Laure ta fadi qasa jaBar kamar an tile kayan wanki tana kwalla wa Malam Bala kira, dukkansu suka yi tsaye suna kallonta. Malam Bala ya fito daga kewaye a gigice, hannunsa rike da buta yana fadar. “Kai Laure wannan irin ihu haka ai sai ki sa juwa ta kwashe ni in fadi ba gaira ba dalili�. Inna Laure ta rinka nuna masa inda Momy ta� ke tana fadar. “Malam duba min ka gani, wace ce wannan Kamar Mariya�. ? Malam Bala ya ajiye butar ya nufo inda suke yana fadar, “Wacce Mariyar ki ke nufi?� Yana qarasowa inda suke yaja ya tsaya, suna kallon-kallo shi da Momy, alamun firgici da kaduwa sun bayyana cikin idanunsa. Dr. Mariya ta yi mmmushi kafin ta ce “Kallona da ka ke tamkar wadda ta fado daga sama, na san ba :zai rasa nasaba da ganin ba-zatar da nayi maka ba a lokacin da daga kai har matarka ku ka saki jiki da na bar muku duniyar shi yasa. ku ka wofintar da rayuwar bayin Allah, ku ka gallazamusu, kuka cuta musu don kawai ba su da kowa, amma me ya sa ku ka manta cewa, duk abin da kuke Ubangiji na nan Yana kallonku, kuma duk daren dadewa sai ya saka wa mai haqqi hakkinsa, musamman ma bayin Allah wadanda basu da alhakin kowa?� Kuka cuta musu, ku' ka gallaza musu kuka tozarta rayuwarsu daga qarshe ma ku ka tarwatsa " . min su kowa ya kama gabansa don kawai ka tsani , uawarsu a kan Iaifin daba bata ji ba ba ta gani ba; wannan shi ne sakamakon soyayyar da Kaunar da na maka? Lallai da haka shi ne ‘sakamakon . soyayya to da ba ta yi rana ba, Sai dai da yake Allah ba azzalumin bawansa bane, sai dai idan shi bawan ya zalunci' kansa, sai 'ga shi bai bar rayuwata ta tozarta ba kamar yadda kai kaso, Ya daga daraja ta a duniya, Ya kuma cika min burina tahanyar azurtanida ilimida nagartaccen miji Wanda ya fi ka komai a rayuwa, Ya kuma sake ba ni wasu ‘ya’yan, sannan daga karshe Ya hada ni da ‘yata gudan jinina, tabbas babu abin da zance da Ubangiji sai godiya. . � ' Abu daya ya kawo ni wurinkn shi ne ka sanar dani inda dana yake in kuma ba haka ba wallahi sai na zauna kotu da kai, don sai ka bani‘dana, cutarwar da kayi musu kuma wannan kai da Allah, Shi zai yi hisabi a tsakaninku, -don haka ka sanar dani inda dana yake . Tsananin firgici da kaduwa su suka girgiza � zuciyar Malam Bala � har ya ji qafafuwansa na Kokarin gaza daukarsa; ya matsa jikin bango'ya jingina'yana faman maida numfashi a wahalce" Laure da ke durqushe a kasa ta zabura ta mike tsaye cike da qarfin zuciya ta cire kallabin kanta taci damara kamar irin‘sabbin mahaukatan nan ta soma magana tana tafa hannaye“Kam babban abin da malam ya hana, mu za ki gwada wa qaryar arziki tsohuwar karuwa, kin je kin yo hayar kaya shi ne za ki zoki mana bariki? To qarya ki ke, wallahi idan kin fasa zuwa kotun kin raina Allahn da ya halicce ki, ke wanda ma ya ba ki hakuri Allah ya tsine masa, mu din nan sai dai mu ga bayanku ba dai ku ku ga bayanmu ba . Dr. Mariya 'ta yi wani qasaitaccen murmushi, ta cire gilashin da ke manne a fuskarta tana kallon Laure kafin ta ce, ‘Ai ita da ma . tabarmar kunya da hauka a ke nade ta, don haka ban kuma kasa dake ba ballantana har ki kwasa". Ta juya kan Malam Bala ta ci gaba da fadar, “Zan tafi Malam, na ba ka nan da sati guda ka nemo min inda dana yake kafin in dauki mataki, ga kuma Saude a hannuna Allah ya jefo min daga sama don haka na rungumi abuna, zan dawo rana irin ta yau don karbar dana, na barku lafiya�. Inna Laure ta yi caraf ta damke hannun Saude tana fadar, “Wallahi babu inda za ki je da ita, nan zaki barta a gidan ubanta, don mijinta yazo yace shi bai sake ta ba, dole kuma'ta koma gidan mijinta Yanzu-Yanzun nan�. Ido waje Saude ke kallonta' gabanta na. Faman bugawa da sauri da sauri, Momy kuwa dariya tayi cikin ajikafin tace “Kadadai ace shirme da� jahilcin' naki har ya fara taba kwakwalwarki? Ai k0 shi uban da ya haifi Saude bai isa ya hana in tafi da ita ba ballantana karabiti�. Kamarki ba 1nn Laure ta Kara hayayyakowa tare dA cukwikwiyo rigar Sauden Malam Bala yace “Sake ta su tafi� . Ta juya tana kallonsa a kidime tana fadar “Wallahi babu inda za ta Malam,Dan duk garinnan banga ubandaya isa yasa ta tafi da ita ba ,Na ce ki sake ta k0?� Malam Bala ya fadi a harzuke fuskarsa dauke da tsananin bacin ran da bata taba ganin irinsa ba a tare dashi A dole ta saketa din zuciyarta na barazanar tarwatsewa ta rasa inda za ta tsoma ranta ta ji sanyi, kawai sai ta durkushe a Kasa ta rusa wani irin kuka mai ta hankali. ~ � Momy da Shukura suka tasa Saude a gaba ‘suka fice batareda sunsake bitakantaba. Suna ficewa daga gidan Malam Bala yaja yan qafafuwansa ya nufi: hanyar dakinsa, bai ko kula: Laure ba, abin da ya qara firgitata ke nan Kara .kidimewa zuciyarta cike da firgicin tonon asirinta. Suna fitowa daga gidan suka shiga mota, Alhaji Ashiru ya ce, “Wai har kun yi me?� “Momy ta ce, “Mun tafi kawai Alhaji�. Ya dan waro ido kafin ya ce “Amma na za ta za ku yi min magana da shi ko da fitowa ce ya yi mu gaisa, k0 ba ku samu mahaifin nata bane?� Momy ta kwantar da kanta a kan makarin kujerar kafin ta ce “Manta da su kawai‘Alhaji, muje ai sai da mutunci ake zumunci�. Bai ce komai ba ya yi wa motar key, Momy ta ce, “Saudat ta nuna musu gidan iyayen Hamid. Saudat ta’amsa da to jikinta a sanyaye, zuciyarta cike da kasala. A Kofar gidan su Hamid maigadi ya sanar musu iyayen nasa sun yi tafiya zuwa Zaria, sai dai Hamid din shi kadai, Momy ta ce ya yi musu magana da shi. Maigadin ya juya ya nufi cikin gidan, bai jima ba ya dawo ya sanar da su yana zuwa. Suna nan zaunc cikin mota daga� gate din gidan, yana sanye da wani farin yadi mai sheki ya daura wa wuyan hannunsa wata tsadaddiyar agogo baka, mai kyan gaske ya dora farin gilashi saman dogon hancinsa da makullin mota a hannunsa, da alama fita zai yi. Kai tsaye wurin motar tasu ya nufo idonsa a kan Momy tun kafin ya ida Karasowa � yana isowa ya rusuna ya gaida Daddy, sannan ya gaishe ta yana fadin, “Doctar kece a gidanmu?� ~ ‘Dr Mariya ta fadada fara'arta kafin ta ce “Aiko nice da kaina Malam Hamid, ai dole ne ma � inzo ko dan qaunar da ka nuna wa Saudat ya zame min wajibi inzo in yi maka godiya, kuma in maka albishir da cewa Saudat yata ce nice mahaifiyarta nina haife ta da cikina" Hamid ya waro idanuwa waje yana fadar, “Yarki kuma DR? Kina nufin dama kece mahaifiyarta�?� , Momy ta amsa da, “Tabbas nina haife ta da dan uwanta Rabi u�. ~ Wani irin dukulallen farin ciki daki zuciyar Hamid. ya daga hannunsa sama yanA yiwa Allah godiya. Saudat kuwa kallonsa kawai ta ke a . zuciyarta tana jinjina ma soyayyar da bawannan »ke mata � � Momy� ta ce “Za mu tafi Malam Hamid, da fatan zumunci mai Karfi? zai shiga tsakaninmu� « Hamid ya amsa da “insha ,Allah"� Amma idansa na kan Saudat wadda ke ta faman haske shi � da lallausan murmushi � Yace “Mamy ki bani adireshinku insha Allahu dana dawo daga tafiya zanzo Babu musu Momy ta ba shi dan qaramin card din da ke cikin jakarta wanda ke dauke da adireshin gidan da lambar gidan, sannan Dady ya ja motar suka tafi Saudat na daga masa hannu har suka Bace wa ganinsa. Wani irin abu ya caki zuciyar Hamid, ya sa dan yatsansa ya lakace ‘yar guntuwar kwallar da ta taso masa, shi da ya sani Allah ya jarabce shi da soyayyar Saudat, irin son da ba zai iya misaltuwa ba, wai yau Saudat dinsa ce ta zama haka? Rayuwa kenan. Ana kiran sallar azahar suka iso gida, don haka Alhaji Ashiru na sauke su ya wuce masallaci don ya bada farali, su kuma suka shige gidan, Momy ta wuce bangarenta su ma suka nufi nasu Bangaren don gabatar