Sashe 42
Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
ba, illah dai kawai na tausayawa rayuwarki da ke qoKarin rugujewa, ke yarinya ce Saudat ba za ki gane waye da namiji ba sai ran da ya buga miki irin nasa tambarin, ranar ne zaki fahimci irin wautar da ki kai a baya. Ni ba zan takura ki ba in ce dole sai yanda nake so za ki yi rayuwa ba, a baya wauta na yi da rashin bincike wanda yasa na dauka zuciyarki shararriya ce babu wani datti a cikinta, ashe ban sani ba tuni kin shigar da soyayyar da take nema ta makantar da ke ta kai ki ta baro ki.� Ya dan yi shiru yana kallonta yana girgiza kai, sannan ya mika mata wayarta. “Ungo ga wayarki.� Hankalin Saude ya qara masifar tashi ba ta san lokacin da idonta ya kawo kwalla ba, sai dai ta ji zubar su saman kuncinta. Dr. ya waro ido cike da mamaki kafin ya ce ‘Kukan me za ki kuma Saudat ai na dauka firgicin ki‘na raba ki da masoyin ki ne da na yi kuma sai na ce na bar ki da shi, to me ye kuma abin kuka?� Saudat ta sa hannu tana share hawayenta, wanda sukaqi tsayawa ta soma magana cikin kuka. “Ka yi hakuri wallahi ba da wani namiji nake magana ba Hamid ne.� Nan ta kwashe labari ta ba shi tun daga sakon da ya aiko Dillaliya da shi har zuwa wayar da suka yi. ~ Dr. ya ja numfashi kafin ya ce ‘Saude kenan, a dan labarin da ki ka ba ni na fahimci kina son Hamid shin haka ne?� Saude ta ji tamkar ya dora mata Dala da Gwauron Dutse aka, ta rasa abin da za tace masa ma. Dr. ya sake cewa, ‘Da ke nake magana fa Saudat kin mini shiru Da kyar ta iya dagowa ta kalle shi, ya yi mata masifar kwarjinin da ba za ta iya kallon idanuwan shi ta fadi abin da ke zuciyarta ba. Murya: shi a sanyaye ya sake maimaita mata tambayar a karo na uku, ba ta san yanda a kai ba sai dai ta samu kanta tana mai girgiza masa kai, alamar a’a. Shin meye dalilin saude na cewa batason hamid mu tara donjin yaddah zataci gaba da kayawa [1/27, 10:11 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [1/28, 12:05 PM] I love my mum: *YAR TALLA*