← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 90

Sashe 87

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'iya tankamata ba har sai da ta gaji' don kanta ta yi shiru sannan ya soma magana kansa a qasa. � “A yi haquri don Allah Hajiya, abu ne wanda Allah ya riga ya qaddara Sai ya faru babu makawa sai ya faru, amma aurena da Sauclat wani mukaddari ne na Allah wanda ba mu isa mu guje masa ba, amma Wallahi ba don ba ni son Asma ba, duk da komai ya faru badasa hannunta ba amma ni ban riqe ta da komai ba, aurena wani mukaddari ne daga Allah, wanda,,,, � “Saurara min haka Malam, ai tun kafin a haife ka na san wannan guntun wa’azin, tunda da ma budurwar zuciyarka ta ja ka izuwa ga kisisinar: ‘yar . aikin gidanka har ka aure ta ai dole xakake fadar komai muqaddari' ne. Sai dai abin da nake bukata a yanzu .kawai ka rubuta takardar Asma ka ba ta: amma aure dakai tagama kodakuwa kaine autan maza banda rufewar ido k0 meye abin naci a tattare da kai? Yo a tauna qashi k0 a karya haKori?� � Ahmad ya mike tsaye ba tare da ya saurari umarnin hakan daga gare taba, ya zura hannu cikin aljhu ya zaro bandir din� yan dubu-dubu har guda � biyar, wato na naira dubu dari biyar kamar yadda ya ba wa Saudat ya ajiye a kan kafet yana fadar, “Ga wannan a ba ta Hajiya ta ‘yi maneji kafin na dawo, amma ni bazan saki matata ba tunda� har yanzu ina sonta�. Bai tsaya sauraren abin da zatacevaya fice abinsa ya barta tana faman kumfar baki ,,,,,,,,,, ,,,,,,,,,, ,,,,,,, Al� amarin rayuwa ke nan, a kWana a tsahi babu wuya wurin Allah, Saudat ta kwashe “Sati hud'u tana. zuwa makarantar boko da islamiyya, cikm ikon Allah kuma duk abin da aka koya mata saita dauke shi kasancewarta mai budaddiyar Kwakwakwa don hatta tukin motar da ta ke zuwa koyo cikin sati guda ’ta ' kware don haka a sati na uku ta fara hawa titi ita * daya, yanzu haka ita ke tuka kanta ta je makaranta ta , dawo gida Saudat ta Kara gogewa tai � wani fresh tamkar ba ‘YAR TALLA ba fatar" jikinta yayi wani luwai luWai har ‘yar qiba ta yi Wadda ta da yanayin jikinta, ga wata wayewa data qara samu ta musamman. , » � A yanzu haka Saudat ta ita rubutun 1Hausa, Turanci ne dai take dan daddagirawa Hausa kam ta yi matuqar iya ta, don har karanta littafan Hausa ta ke na Mambuta dabamdaban, � abin da ya Kara bude kwakwalwarta da Kara wayarmata da kai, ta qara samun experience din yadda za ta kula da kanta da shi kansa maigidan kenan Yau asabar ce ta yi daidai da cikar DR Ahmad sati hudu da tafiya kuma itace ranar isowarsa cikin ikon Allah, don haka tunda ta tashi daga islamiyya Karfe sha biyu da rabi ta dan wuce wurin gyaran jikida kunshida kitso ba ita tabar wurin ba sai qarfe hudu na yamma, don haka tana dawowa� gidan kicin ta nufa don hada abin da zata. ma maigidan kamar yaddata sanarda Mansura tana son girkamasa dambun shinkafa tareda pizza da kuma alkubus cake, potatoes chicken sai lemun‘karas tareda Creamy mango. Duk wannan zaBi nena Saudat don a yanZu itake bada umarnin komaima kondan Ayanzu. takwarene don har littafan girkin tana . Za ki dauko Barzazziyar shinkafarki ki bakace ta, ki cire garin sai ki zuba wa ‘shinkafar ruwa ki tsiyaye ruwan ki sa hannu ki matse, don ‘yan ruwan da suka yi saura su tsiyaye tsaf. Sannan ki zuba ' Barjinki a madambaci ki rufe ki batta ta turaru minti" goma zuwa sha biyar, sai ki sauke ki zuba a mara mai dan fadi ki barbaje shi sosai. * Sai ki kawo mangyad'a mai dan yawa ki zuba ki jajjaga attarugu ki zuba ki yanka albasa qanana, ki Sai .ki kawo dafaffiyar hantarki wadda kika .� yanka gutsin~gutsin ki zuba kisa garin kurkur cokali " guda sai kisa magi da gishiri da curry tare da thyme dadan garin citta da tafarnuwa sai ki juya sosai . sannan ki maida a madambaci ki rufe ki barsu su turaru minti goma zuwa sha biyar, sai ki sauke. Ki zuba a farantin maigida ki kawo dafaffen kwanki ki Bare, ki ‘masa yankan fadi, sai ki jejjera a saman abincin. Ni ma haka na ga Saudat din ta yi, sai na ga ta sa wani faranti ta rufe Sannan na ga ta dauko kwano mai fadi ta kalli Mansura. ' � “Yanzu kuma zan hada Pizza�. Ga yadda na ga ta yi. PIZZA lol Saudat na idarwa ta fice daga kicin din ta nufi babgarenta don magruba ta kawo jiki, don haka tana shiga ruwa ta watso .wa jikinta ta dauro alwala ta gabatar da salla, sannan ta nuifi gaban madubi ta ja stool ta zauna, kwalliya sosai ta yi irin wadda ba ta san ta iya ta ba, ta mike ta nufi kan gadonta ta dauki sabuwar atamfarta cikin wadanda ta kai wa ‘yar islamiyyarsu ta dinko mata. Tana cikin fesa turaren cool water ta ji wayarta ta soma rurin neman agaji, ta yi sauri ta nufi kan bed side drawer dinta ta dauki wayar, ganin sunan da ya fltO a kan madubin baro-Bare ya sa ta yi saurin shafar kore da dan' yatsanta, sannan ta kara wayar a kunnenta cikin tsananin doki ta ce, “Yallabai � har kun iso?� Daga can ta ji ya karya murya yana fadar.“Wayyo tamyau, don Allah ki gafarce ni, na iso, amma ba zan samu isowa ba yau, za mu yi meeting a majalissa� ' Ai Saudat ba ta san lokacin da ta datse kiran . ba, saboda takaici ta wullar da wayar a kan gado cike da Bacin rai, don ganinta idan ya yi mata haka bai mata adalci ba. Ta ja tsaki tare da mikewa da niyyar ta cire kayanta, ta ji an turo kofa tare da sallama. Ai bata san lokacin da ta wuntsira ta nufe shi ba, shi kuwa ya bude hannayensa ta fada cikin jikinsa. “Madam kin yi kyau, kin Kara girma, wallahi kamar musanya min ke aka yi�. Ta sa dariyar farin ciki, “Mu je YallaBai ka ci abincin da na shirya maka sai ka yi wanka ka huta�. Bai musa mata ba ya miketa riko hannunsa tamkar wani qaramin yaro ,suka fice, har dinning area, ta ja mass. kujera ya zauna sannan ita ma ta zauna. Duk abin da ta girka sai da ta zuba ta tura masa, babu abin da bai ci ya yi santiba Wayarsa dake kan tebur ta soma‘ruri ya mika hannu ya dauka, ganin sunan Momy ya sa shi saurin dauka ya kara a kunne, “Hello Momy ina wuni, eh ga ta ma�. Ya kara wa Saudat wayar a kunne, muryar Momy dinta ce ta ji tana fadar, “Hello Saudat, albishirinki? Yau na ga yayanki Rabi u, an ganshi yanzu haka yana zaune a falona� Ai Saudat ba ta san lokacin da ta fasa wata uwar Kara ba, ta saki wayar cikin tsabar kaduwa ta soma fadar, “YallaBai an ga Yaya Rabi’u, wayyo Allah na bari in dauko mayafina mu tafi Dr. ya waro ido, “Muje ina Saudat? Ba ki san k0 Karfe nawa ba ne yanzu? Takwas saura fa". Saudat ta marairaice masa, “Don Allah ka zo mu je, wallahi ba zan iya runtsawa ba yau in ban ganshi ba, k0 ka sa direba don Allah ya kai ni�. Dr. ya dan yi kasaKe yana kallonta, yadda duk ta firgice lokaci guda a take kuma sai ya ji tausayinta ya kama shi, tabbas ta yi kewar yayan nata, za ta iya ma shiga kowane irin hali. Ya sauke kansa daga kallonta ya mike ya suri wayoyinsa da ke kan teburin, ya ce, “Dauko mayafinki kizo muje�. Sai kuma tausayinsa ya kama ta, k0 awa 'daya bai yi da dawowa daga wata tafiyar ba, sai dai ba yadda za ta yi, tana son ganin yayan nata a yanzu fiye da komai. Ta juya ta dauko mayafinta kalar atamfar ta dauko wayarta da jakar takalman kafarta ta tattara kudaden da Dr. ya ba ta wanda ko dubu hamsin ba ta taBa a cikinsu ba ta zuba a jakar, sannan ta fito. Yana nan tsaye inda ta bar shi yana jiranta. Yana ganin ta flto ya yi gaba ta biyo shi a baya, sabuwar motarsa ya shiga. � Saudat ta dube shi, “Ba direba zai kai mu ba Yallabai?� Ya ce, “A’a mu je kawai na tuqa mu, zamu fi sauri�, , ' Ba ta sake tankawa ba ta zagaya kujerar da ke gcfen direba ta bude ta zauna, ta samu ya kwantar mata da kujera, don haka ta kwanta sosai, shi kuma ya yi wa motar key suka fice daga gidan suka hau hanyar Katsina, inda suke sauraren karatun alkur’ani mai girm wanda Dr. ya kunna musu a motar, hakan yasa kowane ya nutsu yana saurare sai ‘yar maganar da ba a rasa ba. Ba karamin gudu ne Dr. Ahmad , yake sharawa ba a kan titi, don Karfe goma da minti talatin ta yi musu a cikin Katsina a gidan su Saudat. Tun kafin ya ida tsayawa Saudat ta Balle murfin Kofar ta fito a guje, ta nufi cikin gidan tana Kwalla wa Yaya Rabi’u kira. Tana shigowa ' falon tana wurwurga idanu, can hango shi cikin doguwar kujera yana shan fan-milk, Saudat ta fasa wata uwar Kara ta kwatsa a guje ta fada jikinsa ta kankume shi tana ihun dariya. , * Shi kansa dariyar yake yana ambaton sunanta � tare da Kokarin dago ta don ganin yadda ta koma amma taKi sakinsa, su Nabil da Nabila ma ‘suka rufa mata baya suka rungume ta suna murnar ganinta. � . Momy dai dariya kawai ta ke musu zuciyarta dauke da matuqar farin ciki da shaukin ganin sanyin idaniyar nata 'Dr ya yi sallama ya shigo falon rike da jakar Saudat da wayarta ya durkusa agaban Momy yana gaishe ta cike da girmamawa, Saudat ta zame daga jikin yayan nata tana kallonsa, kuka ta ke sosai shi kansa sai da kwallar ta zubo masa cikin karfin hali ya soma share mata hawayen yana fadar, “Ya isa haka Saudat, ba kuka za
Chapter 87 · 0% Book details