← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 90

Sashe 54

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sannan ya juya ya nufi gidan a guje. Dr. Ahmad ya maida murfin motar ya rufe ya yi mata key, ya ja sannu a hankali ya bar unguwar. Saude wadda tunda ta shigo gidan ta fada dakinta wanda aka maida shi na zuba tsummokara ta zube a Kasa ba tare da ta damu dadattin dayayiba, tashiga rusarkukamai � tada hankali ji ta ke gabadaya ta tsani rayuwar. Yaron ya shigo tsakar gidan inda jama'a ke ta hidimarsu ya tambaya, “Ina! Saude?� Inna Lami ta nuna masa dakinta, yaron ya nufi dakin, ya iske� ta kwance Kasa~ tana sharBar kuka, ya ce “Ga shi inji mai mota a waje ya ce na kawo miki�. Saude da ke kife tana kuka a dago da kanta a hanzarce tana kallon yaron ta karBi takardar hannunta na kyarma tana qokarin warwarewa kamar tasan abin da aka rubuta ta zuba wa kyakkyawan rubutun ido wanda ta ke jin tamkar shi ne ta ke gani, yaron ya juya ya tafi ya barta tana kallon rubutun da ba zata iya karantawa ba, illar jahilci�. Ta fada ta qara durkushewa ‘ta dukunkune takardar ta sake Ta qara fashewa da wani sabon kuka mai ban tausayi.. Yaya Rabi’u ya fado mata a zuciya, ta tuna rayuwarta da shi, da irin yadda yake rudewa idan ya ga hawayenta ya yi ta rarrashinta, rayuwa ke nan, ga ta yau tana kuka ba ta da wanda zai ce ki yi shiru balle har ya rarrasheta. Yau ta yi' kuka kamar ikon Allah idanuwanta suka kumbura suka yi luhu-luhu, ga bangaren kanta da ya dauki ciwo a dole ta saurara da kukan saboda yadda ta ke jin kan nata kamar zai rabe biyu. Ta tashi zaune ta jingina da bango ta � rafsa uban tagumi tana tunani mai tarwatsa zuciya, Inna Lami ta tah0 dakin ta turo mata robar tuwo wanda aka yaba wa miyar taushe ta ' ce, “Ga shi nan idan kin gaji da kukan ki dauka ki ci da sauri, don yanzu za a wuce da ku gidan uban wanka�. Ta wurgo mata bakar leda, “Ga wannan atamfar uban wanka ceda takalma ‘yan Maradi da abaya wanda za ki saka a tafi, maza don ba ke za a tsaya jira ba�. Tana gama fada ta juya ta yi gaba abinta ta bar Saude na bin ledar da tuwon da kallo, a yanzu idanuwanta sun KeKashe babu abin da suke sai zogi da radadi mai ciwo k0 motsin kirkibatayiba, har Inna. Lami tadawota ~ dauki sallallami, “Wai Saude ya ki keso da mune, kefa kawai akejira,karma kici tuwon kanki kidaukikayan kisaka mushine � matsalarmu� Ta yi tsaki ta juya abinta. Saude ta Ki motsawa daga inda ta ke don yadda ta ke ji. zuciyarta k0 kashe ta za su yi ba za'ta saka kayan ba, har yanzu ji take kamar a mafarki ne komai ke faruwa. Ba ta fidda rai ba da za ta farka a kowane lokaci ta ganta a gidan Dr. Ahmad don haka ta soma linke takardarda Dr. Daya aiko mata ta daure a haBar riga tamau. ' Inna Lami ta dawo ta tsaya daga bakin Kofa cike da masifa ta ce “To sai ki fito tunda ba zaki sauya kayan ba, wlh ko,a tsirara ne sai mun kai ki, ehe�. . Sayde ta yi maza tana faman muzurai, tana faman kaiwa da kawo wa, idonta ya sauka inda su ‘Yarbaba suke tsaye da .qawayenta, sun sha anko ana ta shewa. Yar baba ta watsa mata harara tare dajan dogan tsaki Saude ta sunkuyar dakanta bataredata kula ta ba, Inna Lami ta ce ‘Taho nan, ‘Yar baba mu je ai muku nasiha gaba daya Ta sa hannu ta rike ta Saude na biye da � susuka shigadakin da Lauretake. Badai wata'nasiharkirki bace duk habaici ne ta ke yaba wa Saude, ta yi abinta ta gama sannan lnna Lami tatisasu gaba har~ wurin Malam Bala shima nasiha ce dakuma 'jankunne kada waddatasake talullubo zaninta wai da sunan yaji balle wani abu wai shi jaWarci, duk wadda ta sake ta kashe aurenta, to saidai tasan indazata nufa sannan yayi musu ,. fatan alkhairi daga nan aka dauke su da motoci ’zuwa gidan uban wanka, shi ma'ya yi musu nasihar tasa. Ana gama sallar magaruba � .motocin kai amarya suka zo, qananan motoci ~ masu shegen kyau guda biyar, mijin ‘Yarbaba yaturo dasu na daukar amarya. Shi kuwa Garba gurgu a kori kura ce kwara guda daita za a dauki amaryar adauki ‘yan gidansu don haka mutane duk suka kwashe suka nufl motocin� daukar ‘Yarbaba da. Kyar .. aka samu wasu mutum biyu dattijai wadanda za su raka Sauden. Haka aka kwashe aka tafi da amaren, Saude ta lumshe idanuwanta kukan ma ya Ki yiyuwa, idanuwan sun qafe sai radadi suke, zuciyarta sai faman bugawa ta ke da sauri da sauri tamkar za ta tarwatse. � Direba ya ja wani dogon birki kiyyyy! Ya tsaya a kofar gidan, ginin kasa wanda aka shafe da farar kasa, tsohuwa ta riko hannunta. “Fito mu je ‘yar nan ki shiga da qafar dama, da kuma bismillah�. Saude daina � jin maganganun nasu tamkar amSa kuwwa a kunnenta,ne fuskarta na . rufe da hijabi suka shiga cikin gidan mai dogon zaure wanda doguwar kwata ta raba biyu. Suka isa tsakar gidan ‘yan tsaffin na fadar, “Gafaranku dai masu gida�. Babu wadda ta kula su daga cikin matan gidan sai� yan yara ne ke ta tsallen murna, an kawo musu amarya su suka nuna musu dakin nata aka shiga da ita, cikin dakin wanda duk cikin gidan shi kadai ne ya ci arzikin aka filasce shi da siminti, aka goga masa ‘yar farar Qasa ciki da bai, babu komai a dakin sai tsohon yadin zanin gado da fululuwansa guda biyu, dakin ya sha sabuwar ledar Kasa an kuma zagaye bangon dakin da sabuwar sitara sai ‘yan kayan ma’aikacinta a gefe. Tsohuwa Iya ita da kawarta' hare suka zaunar da Saude a gefen katifar ba tare da sun zauna ba, ta ce, “To mu za mu wuce Saude sai mu ce Allah Ubangiji ya ba da zaman laflya, a yi ta dai hakuri da rayuwa a duk yadda ta zo watarana sai labari, mu dai mun wuce�. Saude dai dake kife saman katifar k0 dagowa ba ta yi ba ballantana su sa ran za ta tanka su ma ba su saurari tankawar tata ba suka fice abinsu. A soron gidan suka hadu da ango an sha sabon farin yadi da sabuwar hula, bakinnan an cika shi da dusar goro, fuskar nan tasa babu annuri sai sambatu yake, “Yo harni za a yaudara? Ai karya ne wallahi, duk wanda ya ci tuwo dani miya ya sha. Yauwa bayin Allah da ma ku na biyo, ku koma ciki yadda ku ka Kunso tsohuwar karuwarcan ku ka kawo min haka za ku koma ku dauko ta ku koma da ita, ba a gidan Garba ba, k0 da ku ka ganni haka nakasasshe to ban gaji da rayuwar duniya ba". ' Tsohuwa Iyah ta tafa hannaye tana fadar, ‘Muhammadu dan Abadallah, Malam Garba me ya yi zafi haka?� Garba ya taso mata, “Abin, da ke cikin wuta, kin ga tsohuwa ina ganin girmanku kar ki sa in dankara miki ashar ku shiga ku fiddo ta in ba haka ba wallahi zan yi abin da ba a tunani,don dukan mutuwa zansa ai muku a cikin gidannan harda ita tsohuwar karuwar ku fiddo ta in kulle dakina kon tsinke ‘babu babu abinda zai fita bayan ita in kunje ku fada wa tsohon banza na ce na ba shi nan da kwana uku k0 ya aiko min da duk abin da ya san na kashe ko kuma in sa kayan dakin a kasuwa ku fada masa na sake ta saki uku�. Daga nan ya juya yana tsangala qafar ya . bar su a sore Hare ta dafa Iya tana fadar, “Yau munga takanmu ni hare kinga koma kifitoda yarinyar nan mu maida ta hannun iyayenta, " wannan nakasasshen banzar zai iya fiye da duk abin da ya fada� Don daman ance gurgu yafi mai qafa iya shege Iya ta ce, “Aikuwa na gani bari in fito da ita". Ta Juya ta koma cikin gidan. Lol jama,a ya abin yakene ku biyoni donjin yaddah zataci gaba da kayawa [1/30, 10:24 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/30, 4:30 PM] A A Dboy: *YAR TALLA*
Chapter 54 · 0% Book details