← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 90

Sashe 24

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

TUNda suka fara tafiyar Saude ke raira kukanta, a hankali har sai da suka kusa kawowa Suleja, sannan wani bacci mai nauyi ya dauketa Ba ita ta farka ba sai da ta ji Dillaliya na tayar da ita, Saude ta bude ido ta ga har sun kawo tasha, mutane na ta fita, sannan ita ma ta bi ayarin masu fitan Tun da suka sauka tasha Saude keta faman zare na-mujiya, ta zo garin da ba nata ba, za ta iya rantsewa tunda take ko gidan Mutum Daya bata taBa zuwa ba, to balle ta tsallaka Kano k0 wani garin da ke kusa� da su, amma yau ga ta cikin ‘Abuja tsamo-tsamo. Ikon Allah. . Dillaliya ta tsaida musu tasi tasha suka shiga, Saude dai na biye da ita da idanuwa sai faman waige-waigen idanuwa take. A hankali ta ga sun shigo cikin rukunin wata unguwa wadda kai tsaye za a kira ta da G. R.A Unguwar shiru ba ka Jin motsin komai sai kukan tsuntsaye da haushin karnuka ga manyan shuke shuke da suka sa titin unguwar tsakiya, kowane gida ka kalla ka san na wani kusan ne, gaba daya babu gidan da bana wani babban mutum ba a unguwar. Saude na cikin kallon jerin gidajen ta ji Dillaliya na fadar. “Nan za ka ajiyemu.� A hankali Saude tabi kofar gidan da aka ajiye su din, wanda za ta iya rantsewa tunda suka taho gidaje kadan ne suka kai shi kyau da tsaruwa. Saude ta zuro qafafuwanta ta fito kamar yanda ta ga Dillaliya ta yi, ta tsaya ta biya mai tasi din sannan ta yi gaba Saude ta bi bayanta. Kai tsaye katafaren gate din gidan suka nufa makeken gaske mai kama da Kofar shiga gari, ga wasu manya-manyan shuke-shuke da suka zagaye gidan gaba daya. Dillaliya ta tsaya tana latsa wata ‘yar karamar na’ura da ke like a bangon gidan. ' Wani irin tsoro da faduwar gaba suka bugi Saude anya kuwa, ba tahowa akai da ita a saida ita ba, don tana da yakinin wannan ba gida bane sai dai k0 wata ma’aikata ta sarrafa naman mutane Ba ta gama tunanin ba ta ji qarar tura gate din take ta yi ido hudu da wasu manya-manyan qarti har hudu, bakikkirin da su majiya qarfi, sun bude qofar, suna qokarin shiga suka ga wata bakar mota yar dunkulalliya mai daukar hankali ta ratsa ta shiga cikin gate din Dillaliya ta janyo hannun Saude da niyar su shiga, qartin nan suka yo kansu da wata irin masifaffiyar tsawa wadda tasa ‘yan cikin Saude juyawa gaba dayansu,fitsari ya fara kwace mata a wando, ita kanta Dillaliyar ta firgita, don cikin rawar murya take fadar. “Ku yi hakuri wurin matar gidan muka zo ni ce wadda na taBa zuwa da Hajiya Kande, wan,,,,,, “Shut up! I don ’t speak Hausa.� , Tuni ‘yan cikin Dillaliya suka juya, .don ita dai k0 zo in kashe ki da Turanci ba ta sani ba, ido ya ' raina fata ta dubi Saude tana fadar. ' � “Me suke cewa?� Cikin muryar kuka Saude ta ce, “Ban sani ba nima.� Dillaliya ta harzuka “Yanzu ashe duk makarantar da ki ke zuwa asarar kudin tara kawai ake baki san komai ba?� � Saude dai ta yi shiru ba ta ce komai ba. Mutanen nan suka maida kofa suka rufe suka bar su nan tsaye, Dillaliya na ta faman saukewa Saude kwandon masifa, don ba ta iya Turanci ba. Kunji fa rashin� kunya. A hankali motar da ta shigo cikin gidan mai bakin gilas' ta faka a qatuwar harabar da aka tanada dan ajiye motoci, aka bude gidan direba da hanzari, wata ‘yar budurwa ta fito cikin shigar suite baqaqe da gani ba zata wuce shekara talatin ba , Tana fitowa ta bude gidan bayan motar tare da ja gefe ta kama, wata kyakkyawar mace ta fito, mai masifar kyau kai ka ce Balarabiya ce k0 Baturiya saboda tsananin kyau da hasken fata Tana sanye cikin shigar wani danyen leshi mai kyan gaske, wanda tsadarsa ta tasamma dubu dari da wani abu, an yi masa dinkin riga da siket matsatstsu irin dinkin matan manya na Legas, dan qaramin mayafi ne saman kafadarta wanda ta dora shi kawai ta yi a gefen kafadarta, kanta an kafa mata wani masifaffen dauri mai kama da daurin inji, qafar nan tana sanye cikin wani masifaffen takalmi mai tsinin gaske da ‘yar Karamar post din su a hannunta Idonta na sanye da wani qaton bakin gilas wanda: ya mamaye rabin fuskarta. A, Kai tsaye za ka lye. kiranta da ‘first Lady� saboda haduwarta. Tana fitowa daga motar ta dubi yarinyar ’da ke tsaye, cikin wata irin murya mai kama da rada rada ta soma magana cikin harshen turanci. “jeki shigo da su.� Yarinyar ta amsa da ‘okey Tare da juyawa da sauri ta wuce ita kuma ta nufi cikin gidan nata tana wani irin taku, da wata irin faskekiyar waya a 'hannunta. ; Dillaliya da ta gaji da ruwan bala’i sai kuma ta yi shiru tana tunanin mafita, can dabara ta fado mata ta Ciro ‘yar qaramar wayarta baby Nokia ta lallatsa lambar Hajiya Kande ta kara a kunne; tun kafin ta soma magana ta ji an bude wata qaramar kofa yarinyar. Tace come and enter Dudda Dillaliya ba ta san abin da ta ceba, amma ta fahimta ta hanyar yi masu nuni da hannu da yarinyar ta yi, don haka ta zabaura ko kallon Saude ba tayiba tayiciki, don haka itama tamike da sauri ta bi ta Kan Saude ya yi masifar daurewa lokacin da ta shiga cikin harabar gidan, gabanta ya shiga wata rugurguza da bugawa mai tsanani, yarinyar ta yi masu jagora har zuwa wani qaton ginin bane hawa hudu, wanda tamkar da gilas kawai aka yi shi, dama da hagu duk iri daya ne, suka nufi Bangaren dama suka tattaka wata matattakala wadda ba tafi hawa shida ba, sannan suka ratsa ta wata Kofa mai fadi, anan ma mace ce tsaye qikam kamar an kafe ta, tana sanye ita ma da bakaken suita jikinta, sai da ta sa wata ‘yar na’ura ta daddana a jikinsu sannan suka � wuce cikin kofar da za ta sada ka da qaton falon gidan. Saude ta bi matar da kallo a zuciyarta tana fadar, ikon Allah yanzu ita kuma wannan aikinta kenan� Kamshin rom freshner da turaren wuta dan Maiduguri shi ya dakar masu hanci su duka hakan ya tabbatar masu da sun iso falon, qaton gaske wanda aka zagaye da kujeru saiti uku, kuma kowane kalarsa. Kai batun ma in tsaya in, labarta muku haduwar falon duk wani bata lokaci_ne na barwa mai karatu ya yi image dinsa a zuciyarsa.‘Yarinyar wadda zan iya kira da Ingozi ta yi» masu nuni da cikin falon suka tafi suka zauna dirshan a ‘qasan kafet din duk da kujerun da ke zube kamar a cikin store. Yarinyar ta juya ta tafi abinta tabar. su nan zazzaune kamar masu zaman gaisuwa,; sai :rarraba idanuwa suke ba Sauden ba na Dillaliyar ba, wadda sai ka ce ba ta taBa zuwa ba. Tun suna tsammanin fitowarta har .suka soma . cire rai da za ta fito, don sun share fiye da awa biyar a zazzaune suna zare namujiya, sanyin AC sai kada su yake suna faman karkarwa. Tuni sun gama’fidda rai da fitowarta, ga gajiya ga wata~ masifaffiyar yunwar da ke kwakwalarsu, sai faman gyangyadin gajiya suke. , Kamshin turarenta shi ya farkar dasu; gaba daya Suka wartsake suna daidata nutsuwarsu,. idanuwan Sande na zube a kan matar wadda ta nufo inda suke tana lallatsa faskekiyar wayar da ke-hannunta,*Allah mai halitta abin da Saude ta iya fada kenan a zuciyarta, saboda yanda ta ga tsabagen kyau kwance a jikin matar, wadda ba za a kira ta da doguwa ba ba kuma gajeriya ba ce, sai dai a kira ta da tsaka-tsaki. Ba ta da qiba sosai, amma kuma ba ‘siriri ba ce sosai dai tana da jiki daidai-daidai. 1page is missing A yanzu ma takalmi ne mai tsini a kafarta, sai dai babu gilas yanzu a fuskar tata. Ta karaso cikin falon ta fada kan kujera ta dora kafa daya kan daya ba tare da ta dago ta kallesuba idonta na kan wayar hannunta ta rinka amsa: masu gaisuwar da suke ta faman kwarara mata Duk azaton Saude za ta basu hakurin shanyar dasu da ta yi amma sai taga kwata-kwata ma hankalinta baya kansu yana kan wayar dake hannunta ne falon ya dan dauki shiru, Dillaliya na nazarin ko ta fara. Maganane Cak matar ta mike wadda ba zata haura shekara talatinba ba, muryar nan tatat kamar mai rada ta soma magana. ‘Ki yi hakuri baiwar Allah ina da abin yi yanzu haka kikaga nazo nazauna dan insaurareki dama na lura kamar akwai wani important issue ne shi yasa na ce aje a shigo da ku, yanzu banida lokaci inada apointment da karfe sha daya.� Tana maganar tana taflya. � Dillaliya ta fara bada hakuri cikin rawar murya tana fadar, “Ki yi hakuri ranki shi dade, wailahi na dan saurara ne ki fara magana kada in fara kiga kamar na yi rashin da’a a gabanki, dama ba wani abu ba ne yar aikin da kika ce kina so CE na kawo miki guda tun wancan watan� lokacin da mukazo ni Da Hajiya Kande taya ku murnar cin nasarar lashe zabe kika ce kina san yar aiki guda mai nutsuwa za ki Kara shi ne na tsaya na binciko miki na kawo miki Matar ta dan dakata daga tafiyar da take ta waigo a hankali, ta daura dara-daran idanuwanta kan Saude tana qare mata kallo sama da Kasa, tamkar wadda ta ga wani abun kyama a tare da ita, ta dauke kanta tana � latsa wayarta cikin rashin kulawa ta ce, “Is okey. � Ta dan karkace tasa hannunta saman hannun kujerar ta janyo sai ga wata ‘yar loka, shake da kudi bandir-bandir yan � dubu-dubu, ta zaro masu yawa ba tare da ta Kirga ba ta cillawa Dillaliya tana fadar, “Ki hau mota, sai da safe.� � Ba tare da ta~ saurari godiyarta ba ta yi gaba abin ta, dad'i ya kashe Dillaliya ta tashi jiki na Bari. tana fadar, “Ke kuwa kin yi nasara Saude, da
Chapter 24 · 0% Book details