← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 90

Sashe 16

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kallon shi sai faman sosa gemu yake wanda ke _ faman yi masa kaikayi duk ya yi wani quda~quda da alama ba za a rasa kwarkwata a cikin saba, saboda tsabar qazanta da kurar duniya da ya sha. Saude ta dame zuciyarta ta amsa masa don k0 kadan ba tajin za ta iya yi masa wulaqanci saboda girman shekarunsa dan ya yi jika da ita. Garba ya Kara watso haqoran nan wadanda su kai kore fatau kamar gansa-kuka yana fadar, “Haba Saude na ga alamar kamar ba ki san magana dani, ki yi hakuri ni masoyinki ne ba makiyinki ba kuma ni aurenki zanyi bawai wasa zaikawoni wurinkiba yanzu haka idankika amince min mahaifinki kawai zan nema a yi magana.� Saude ta watsa masa wani kallo mai kama da harara ta zumburo baki kafin ta ce, “Ni fa ba anre zan yi ba yanzu Ya yaqe baki yana fadar, “Haba Saude ke yanzu idan bakiyi aureba saime zakiyi?idan ki ka amince: ki‘ka aure ni, killa ceki zan yi a‘gidana, kin gama zuwa talla idan ma kina tunanin matana hudu ne to a shirye nake dana saki daya daga cikinsu Ya kikacene Saude?� � Haushi ya kamata ta mike afusace tadauki bokitin tallarta ta yi gaba ta bar shi nan zaune Garba Gurgu ya yi dariya yana girgiza kai yana fadar� “Yaro yaro ne.� Ya mike yana cangala qafa shi ma ya yi gaba abin sa. Bayan Saude ta gama tallarta da yamma likis ta koma gida a gajiye ta samu ta ci abinci ta yi sallar Magariba, sannan ta dauki tallar dare ta fita kofar gida ta zauna da ‘yar fitilar aci-balbal. Kamar daga sama ta hango shi tsangal-tsangal haushi ya cunkusheta ta bade fuska a zuciyarta ta kudiri aniyar idan ya sake ya zo inda take sai ta cire kunyarsa daga idanuwanta ta yi masa rashin kuunya tunda ta lura bai san girmansa ta gani ba ta daga masa kafa ba Da mamakinta sai ta ga ya yi wa kofar gidansu tsinke, ta saki baki da idanuwa tana kallon shi, ta ga ya kira wani yaro ya tura shi cikin gidansu. Yaron bai jima ba ya fito tana kallon su can sai ta ga mahaifinta ya flto sun tsaya suna gaisawa, gabanta ya yi ’mata mummunar faduwa hankalinta ya yi masifar tashi ba dai Garba wurin mahaifinta ya zoba. Wayyo Allah na shiga uku! Abin da ta iya fada kenan wasu zafafan hawaye suka shiga zarya a kuncinta tana kallon yanda mahaifinta ke ta faman washe bakivyasa hannu ya karBi kudin da Garba Gurgu ya ba shi, sannan suka sake yin musabaha, sannan ya shiga gida shi kuma ya wuce abinsa ba tare da ya kalli inda take ba. Saude ta ta kwashi kayan tallarta ta nufi cikin gida. A tsakar gida ta samu mahaifin nata na fadawa “Laure kin ga wani abun murna k0 wai mutumin nan Garba Gurgu ke son Saude Laure ta rangada kuda ta ce, “Kai amma abun ya yi min dadi wallahi, ka ga sai a hada su su duka da ‘Yar Baba. don ita ma ta ce yaron nan mai zuwa wurinta da jar motar nan ya ce zai turo ai maganar aure Malam Bala ya ce, “Ai ko haka za ai dama ni na amsa masa, yanzu haka ya ce jibi za a kawo kayan nagani-inaso yanzu haka har kudi ya ba ni kin gansu dubu biyu. Kai gaskiya mutumin nan yana da mutunci.� Laure ta ce“To, ai sai ka tsakuro mini nawa tunda ba kai kadai keda diyar ba Malam ya ce, “Kefa tsiyarki ke nan duk abin ki ai kya bari' na mutu sannan ki rufe ni ai k0?� Ya ja tsaki ya cimimiya kwarar dubu guda ya cilla mata ya juya zai tafi ya ga Saude tsaye rungume da kayan tallarta hawaye sun gama bata mata fuska. Malam ya ce, “Ke kuma fa lafiya?� Cikin muryar kuka Saude ta ce “Ka yi haquri Baba don Allah wallahi bana san shi ba zan iya aurensa ba, sabo... Malam ya katse ta ta hanyar fadar, “Ke dalla Saurara mini kin jiki Ba kya son shi sai wa ki ke so?� Saude ta yi shiru tana faman shashshekar kuka Malam ya sake fadar “Na ce idan ba kya son shi, sai ubanwa kike so?Munafukar Allah,nankikaso ki jibge mana kita zama kitsufa a tasha kina talla, tunda kebaki da tunani ko Allah yataimaka kemaya kawo miki dauki, tunda ki ka tashi akwai bakon takalmin da ya taBa zuwa wurin ki da sunan so, iye? Amma shi ne har kina da bakin magana. Shekarar ki nawa yanzu a duniya? Kin zauna kin jibge babu mai taya ki kek0 kishin kanki ba kya yi, kina kallon ‘yar uwarki kullum wannan ya shiga wannan ya fita, harda masu motoci, amma saboda rashin kishin kai ba ki taba damuwa ba.� mts! Ya wuce yana fadar. “Idankinada wandakikeso to saikituro shi ai lokaci bai qure miki ba daga nan har ranar daurin aurenki Wani irin kuka ya Kara kwacewa Saude, ta aje kayan tallar ta yi dakinta da gudunta tana. wani irin kuka mai tsuma zuciya. Laure ta ja tsaki tatattara kayanta tana fadar, “Ke dai kya kai su idan kaya ne dan bakin ciki sai dai ya kashe ki don na gaba ya riga ya yi gaba har abada ba zaki iya kamo taba.� Saude ta sha kukanta har ta godewa Allah bata . da mai lallashinta haka ta kwanta har bacci barawo ya sure ta. Haka ta farka yau idanuwanta duk sun � kumbura sun yi jawur saboda kukan da ta sha jiya. Haka ta je tallanta ta dawo jikinta ba kuzari kana ganinta ka san tana cikin matsananciyar damuwa. Ta yi zaman daBaro kan sumuntin tsakar dakin, don kuwa dakin bai da arzikin k0 qaramar tabarma Saude ta jingina da bangon dakin ta rafka wani ; uban tagumi ko tunanin me take? Oho ‘Yar Baba ta dago labulen tana mata wani shakakken kallo kafin ta ce “Idan kin gama tagumin sai ki fito ga kayana na ki hado ki wanke mini. � Saude ta dago da jajayen idanuwanta tana « kallonta, haushi da baKin ciki suka turnuqe mata zuciya, tuni dama batun yau ba take jin takaicin abin da ‘Yar Baba ke mata ba sai ka ce ita ce babbar, ita ma kuma ita ce karamar. ‘Yar Baba ta ce, “Ki ka tsaya kina kallona da wasu kananan idanuwanki can masu kama da na kwarkwata kixo ki min wanki na ce Takaici ya kuma turnuke Saude cikin fusata ta ce, “Wai ‘Yar Baba me ki ka dauke ni ne jakar ki ko kuma me? Karfa ki manta a girme na girme ki,amma ki rinka! yi min abu kamar wata yar da ki ka haifa. Ai ba ‘yar wanki ki ka aje ba, da ki ka dama can da ina miki Inna ce ke sani, amma ke baki isakisani inmiki wanki ba� � ‘Yar Baba ta ce ‘Eh, lallai wuyanki ya isa yanka, har ni ki ke gayawa magana yau k0 Saude dan kin ga Laure ba ta nan lallai za ki san kin yi da diya ba shegiya ba, za ki gani.� Ta juya ta yi gaba. Saude ta ja tsaki ta IaIIaBa ta kwanta ta ci gaba da nazarin abindayadameta. Bata ankaraba saidaita ji saukar kayan wanki a jikinta ta zbaura ta mike tana kallon mai wannan aikin. 0000000000 “Wato kenan har� yar iska ce har kin yi girman da ‘Yar Baba za ta sanya ki ki mata abu ki zage ta ki ce ba zakiyi ba. � To yau sai na ga uban da ya ,tsaya miki ki dauke su maza ki je ki wanke mata, ki shanya ki zauna su *bushe ki linke ki kai mata daki, tantiriya marar kunya, ai na godewa Allah morewa ta dama na ga rayuwarki ta wulakanta, kuma na yi nasara, in dai ina numfashi kin auri Garba Gurgu kin gama, bankadaddiya yanda na ga bayan uwarki da wannan takadarin ke ma sai na ga naki. � " Ta ja tsaki ta wuce tana fadar. “Munafukar banza!� . Wasu irin hawaye masu dumi suka zubo daga idanuwan Saude tasa bayan hannunta ta goge sannan ta' shiga tattara kayan wankin ta wuce tsakar gidan, Ta. wanke su gaba daya abun bakin cikinta har da bireziya da dan paint, saboda kawai tsabar raini da wulakanci. Rayuwa kenan. Kamar yanda mahaifinta ya ce za a. kawo kayan nagani-inaso, haka kuwa aka yi Garba Gurku ya aiko mata da kaya cikin Gari ya yi zafi, dinkakkiyar atamfa ce ta roba riga da zani sai dakakkiyar abaya kwaya daya, sai takalmin roba shi ma guda daya da sinqin sabulu guda da Katuwar ’kwalbar mai dangwali-yaBa, sai naira dubu a sama. Laure ta dauki naira duban sannan. ta mikawa Saude kayan don ba abin da ya yi mata a cikin kayan. Wasu irin hawaye masu zafi suka ziraro daga idanuwanta tasa hannu ta karBi kayan ta wuce daki � da su. Tana shiga ta wurgar da su tsakar dakin ta durkushe tana raira wani sabon kukan mai cin zuciya. Tabbas tana cikin halin da ya kamata a tausaya mata,Yayanta ya ringa yi mata gizo cikin idanuwanta ko wane hali yake yanzu? Saude ta sha kukanta ta gaji ta lallashi kanta ta yi shiru Abu wasa-wasa lokaci ya ci gaba da tafiya, Garba Gurgu ya ci gaba da yi wa Saude hidima, idan abun kirki ne sai Laure ta rike, idan kuma ta gajam tagajan ne sannan za ta ba ta, ita k0 ba ta taba kallon kayan ba don yanda ta tsani mai kayan haka su ma kayan ta tsane su. � Ranar: wata Laraba Saude ta dawo daga tallar safe, misalin qarfe daya na rana, Laure tace yau ba tallar rana ta je ta shirya za ta je ta dubo ‘yar Garba Gurgu da ta haihu ta dawo gida wanka jiya ya zo ya gayawa Malarn. . Wani bakin ciki ya tokarewa Saude wuya, ta rasa ma abin da za ta ce saboda takaici, ta wuce dakinta ta yi kwanciyarta, har aka soma kiran sallar La’asar, Laure ta ji shiru ta leko dakin nata ta ganta a kwance idonta biyu k0 motsin kirki ba ta yi. Laure ta dauki sallallami tana fadar,
Chapter 16 · 0% Book details