Sashe 30
Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ciko da hawaye muryarta na rawa tace, “Ka yi hakuri don Allah. � Ya watsa mata idanuwansa tare da Jan wani dogon tsaki “Mts!� � Saude ta yi saurin sunkuyar. da kanta Kasa, yana kallonta cikeda tsanarta ya ce, “Ki fadawa Madam, ina da meeting yau kar ta ga ban sa an kawo mata sakon nan ba sai, zuwa gobe komai kr nan mu hadu ta network.� Yana gama fada ya mike ya sa kai ya fice ya bar Saude a tsaye, wasu siraran hawaye suka biyo kuncinta tadurkushe a gun. Wayyo ni Allah na ya. Ubangiji ga Saude na san baka mance da ita, ba ya Allah Ubangiji ka cire ni daga' wannan rayuwar qangin� bautar da rashin galihu.� A hankali ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya, sai da ta yi mai 'isarta bata da mai lallashinta sannan ta share ’hawayenta. Ta diba tiren abincin dake gabanta t duba ba wani da yawa yaciba sannan itama ta zauna ci tsakura kawai tayi saboda yanda take jin zuciyarta babu dadi. Tana gamawa ta mike ta fita da kwanukan sannan ta dawo ta gyara falon tamkar ba a taba shigowa ciki Ba sai da ta gyara ko’ina ta yi turaren Wuta ta sassaki labulayen tagogin ta qara gudun AC � a koina sannan ta rurrufo falukan ta fice, ta nufi can Bangaren. , Babu kowa a falon qasan sai Aunty tana turaren wuta, ta gaishe ta cike da girmamawa, Aunty ta bi ta da. kallo tamkar mai karantar, wani abu. Muryar Saude a sanyaye ta ce “YallaBa‘i ya ce“A fadawa Madam ba zai dawo ba sai gobe Aunty ta ce, “To ki hau sama ki fadawa Hajiyar da kanki.� Saude ta dan yi jim cike da tsoro. Aunty ta katse mata tunanin da fadar, “Kije mana Saudat tunanin me ki keyi haka?� Saude ta girgiza kai sannan ta wuce ba tare da ta ce uffan ba, ta tattaka matattakalar benen ta haye sama. A karo na farko kenan da ta fara hawa saman. � Haka kawai ta tsinci gabanta na faman faduwa,_ wani irin tsoro mai tsanani ya dirar mata, ta rinqa bin falon da kallo aljannar duniya, lallai ba banza ba masu kudi ke mantawa da ni’imar da Ubangiji ya yi masu ba. Muryarta na faman sarkewa ta yi sallama� har sau biyu. Babu wanda ya amsa ga shi kuma tana jiyo hayaniyar mutane a falon da ke gefe, don haka ta Kara matsawa tare da yin wata sallamar. Tun kafin ta karasa rufe bakinta ta ji an watso mata wata dunkulalliyar ashariya cikin ta ya duri ruwa, kafin ta yi tunanin juyawa ta ga Asma gabanta, tun kafin ta karasa tantance ta, ta ji saukar wani mahaukacin mari a kuncinta gefen dama da hagu. Saude ta durkusa ta dafe kuncin lokacin da ta ga wata wuta ta gifta mata a idanuwa, cikin takaici Asma ke fadar, “You are very" stupid, ke jakar ina ce? Da ina meeting za ki shigo ki distubing dina banza sakarai shashasha, uwar me aka yi ne da ta sa ki ka shigo mini har falo?� Saude ta durkusar da kanta qasa daga duqen da take, hawaye suka soma zarya a kuncinta, cikin muryar kuka ta ce “Ki yi haquri dama Yallabai ne ya aiko ni, ya ce ya yi tafiya sai zuwa gobe da yamma za.. ‘So What! Na ce sai me? Da ya aiko ki sai ya ce ki iske ni duk inda nake ki fada mini, iye?� Ta ja wani dogon tsaki mts! Kafin ta ce, “Da alla gate out on my parlour� Ta sake kwatsa mata tsawa, “I say gate out k0 ba kya jine?� saude ta zabura ta mike ta bi hanyar da take nuna mata jikinta na rawa, Asma ta sake jan wani tsaki tana fadar, ‘Stupld kawai.� Sannan ta juya ta koma ciki abin ta. Saude na fita kai tsaye bangarenta ta fada kan gado ta fasheda Wani irin kuka mai cin zuciya wayyo Allah yau ta ga ta kanta, wannan wace irin rayuwa ce ta samu kanta a ciki me cike da qaskanci da wulaqanci ni Saude? Kuka take ‘sosai bata da mai lallashinta. Rayuwa kenan. ,,,,,,,,,,,, ,,,,,,,,,,,,,, Haka rayuwar Saude ta ci gaba da tafiya cikin kaskanci da rashin galihu, kullum tana cikin bauta, ita da bayi ba su da bambanci, ’sauqin� ta ma tun a gida ta riga ta saba da wahala. Yanzu haka rakube take gefen kujera bayan ta gama. gyara falon ta gaji, ta rakube gefe tana kallon tashar Saudiyya, wani shiri da suke yi duk karfe biyar na yamma. � Dr. Ahmad ya sauko daga sama yana sanye da kayan wasanni na kwallo, gajeran wando da singleti sai takalmin ‘yan kwallo, Saude ta saci kallon shi kadan. Kayan sun masa kyau sai ka ce irin turawan , nan da ke buga wasan kwallon kafa, ba tare da ya kalli inda take ba ya wuce abinsa yana fadar. “Ki biyo ni da robar ruwa mai sanyi.� Saude ta zabura ta mike ta nufl wurin kantar da -ake ajiye lemoka ta bude ta Ciro robar Faro guda kwalin lemo guda tare da kofi guda daya tabi bayansa A qaton filin wasan� dake gefen lambun gidanta� same shi yana ta faman tika kwallo shi daya, duk ya hada gumi, Saude ta rakube gefe rungume da tirenta hannu tana kallon ikon Allah, zuciyarta na _ raya mata wasu abubuwa da dama cike tà ke da mamakin Yallabai din tana mamakin yadda duk abin da ya yi sai ya yi masa kyau, tunda take bata taba ganin muninsa ba, kullum ma kamar~kara masa kyau ake. Shin dama akwai mutum irin haka? Ba ta ankara ba sai dai ta jiyo sautin muryarsa na fadar. “Wai ke k0 kurma ce ne?� Saude ta zabura da saurinta ta nufe shi jikinta na rawa, ta durkusa� gabansa cikin rawar murya tana ~ fadar, “Ga ni.� Ya ja tsaki cike da takaici kafin ya ce, “Hankalin ki yana ina ne lokacin da na wage murya nake ta kwalo miki kira? Me ki ke kallo ne a jikina wanda har ya dauke miki hankali? Tunanin me ki ke�?� � ' Ya sake jan wani dogon tsaki ya gif‘ta ta ya‘wuce yana sharce gumin goshinsa da hannunsa, ya bar ta a duke da tiren lemuka tana faman rarraba idanuwa, tsoro ya kama ta dan ba ta san irin hukuncin da zai yanke mata ba. Haka ta daure ta dake zuciyarta ta bi bayansa, tsaye yake gaban na’urar sanyaya ruwa, ya tara kofinsa yana zubowa, Saude ta durkusa. gabansa muryarta a raunane ta ce, “Don Allah don Annabi YallaBai ka yi hakuri, insha Allahu na yi maka alkawarin ba zan Kara ba.� nazarin wani abu a fuskarta, ba tare da yace uffan ba ya dauki ruwansa ya durawa cikinsa ya ajiye kofi din ya yi mata nuni da hannu alamar ta wuce kawai, ya yi gaba abinsa ya haye sama. Saude ta girgiza kai zuciyarta na cike da mamakin miskilanci irin na dan adam. Duniya kenan. � Da misalin Karfe tara na safe Saude ta kammala ayyukanta gaba daya, ta kunna turarukan wuta a ko’ina sannan ta dauko room freshner ta faffesawa labulayen falukan da kujerun� Dr. Ahmad ya shigo falon daga shi sai dan qaramin gajeran wando duk ya hada gumi, da alama daga motsa jiki yake. Kai tsaye ya wuce ya tsiyaya ruwa a kofl ya sha kusan kofi biyu, sannan ya wuce abin sa. Har ya taka step din da zai kai ka falon shi na sama ya waigo ya kalli Saude fuskarsa ba yabo ba fallasa yace “Kije ki sanar da kuku yau ina da baqi da misalin qarfe sha daya na safiyar nan ya tanadi duk abin da ya san za a iya bukata." Yana gama fada ya yi gaba ba tare da ya tsaya ya saurari amsawarta ba. Saude ta maida kayan sannan ta fice da sauri dan isar da sakon da aka aike ta. Tana dawowa ta same shi tsaye a falon sanye da farar jallabiya a jikinsa yana waya ta ja gefe ta zauna. Ya‘yi wayarsa ya gama sannan ya matso inda ~ take ya� mika mata wani key yana fadar, “Karbi wannan key din ki bude wancan falon ki gyara anan zan sauke bakin nawa.� Saude tasa hannu biyu ta karba, ya juya ya koma sama, ita kuma ta mike ta nufi kofar: da niyyar budewa, amma abun ya faskara, saboda gaba dayan kofofin gidan odar waje ne in ba wanda ya saba ba. ’don ko wancan karan da za ta shigo falon nasa ’anty ce ta� bude mata, Ta dan nutsu tana tunanin * .yanda Suka bude a wancan karon', cikin ikon Allah ta ~samu ta bude kofar sannan ta shiga. Katafaren falo ne dogo mai girma wanda ya ji kujerun silba masu kyau sunkai ashirin sun sa wani dogon char a tsakiya. Kai da ganin haduwarsu ka «san odar waje ne. Ga falon ya ji wani lallausan kafet ya mamaye gaba dayan falon wanda aka Kawata shi Dukda falon ba wani datti ya yi ba, amma haka Saude ta gyara shi sosai ta goge ko’ina da ina ,hatta jikin bangwaye wadanda gaba dayansu “tayil ne sai da ta goge, gaskiya ta sha wahala sosai harta samu ta gama, ta zauna ta turare falon da turaren wuta ta feshe shi da air frshner masu kamshin. gaske ta kunna A.C din falon, gaba daya falon ya shiga fitar da wani sanyayyan kamshi mai ni’ima. . � Saude ta juyo da niyar tifowa shi kuma ya shigo ta yi saurin matsawa ta zube Kasa tana'fadar, “Sannu da fitowa YallaBai an kammala.� Bai tanka mata ba ya Wuce ta yana bin falon da kallo da alama shi ma yanda falon ya dauki qamshi ya burge sa, shi yana kallon falon ita. kuma tana kallonsa, tunda take da shi ba ta taBa ganin yasa qananan kaya ba sai yau, dan sai ta gama yafi mata kyau fiye da kullum. Ganin zai juyo sai ta yi saurin dauke idanuwanta tamike tayi gaba, bataredata bariya kamata tana satar kallonsa ba. Tana fitowa ta ja gefe ta zauna a falon tana kallonsa ya fito yana wani takawa tamkar wanda ba ya san taka qasa. Ba tare da ya qaraso