Sashe 57
Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya fito, tsoro ya cika masa zuciya tun yana addu’a a zuciya har ta fara fitowa fili. . . Can cikin ikon Allah sai ga Dr. Mariya , ta fito,Hamid ya zabura ya miKe ya nufe ta yana fadar,“Lafiya dai k0 likita?� Dr: Mariya ta yi murmushi kafin tace *‘Ka kwantar da hankalinka Malam Hamid * insha Allahu ‘yar uwarka za ta samu sauKi � amma yanzu ka biyo ni ofis akwai wasu yan ; tambayoyi dazan maka Cikin karyayyar zuciya hamid ya amsa da, “To". Sannan yabi ta ofis din Sai da ta zagaya ta zauna ta cire gilashin fuskarta sannan ta nuna masa wurln zama, Hamid ya ja kujera ya zauna yana kallon magidanciyar matar, wadda a qallah ba data wuce shekaru arba‘in. Ba Dr. Mariya ta gyara zamanta tare da tattaro duk wata nutsuwa, kafin ta ce “Malam Hamid don Allah akwai wasu ‘yan tambayoyi da nake so in maka, da fatan za ka yi min. uzuri, ka kuma fada min gaskiya, amma fa kayi hakuri". Hamid ya qara tattara nutsuwarsa sosai yana kallonta, kafin ya ce “lnsha Allahu" Doctor Mariya ta yi wani murmushi kafin ta ce “To na gode kwarai�. Ta dan ja numfashi ta ci gaba da cewa, “Da ma ba wata magana ba ce kan maganar ‘yar uwarka ce Saudat a katinta na ga ka . rubuta sunan unguwarku wadda ke cikin Dandagoro haka ne? � Ya daga mata kai alamar eh ~ Ta girgiza kai, "To amma Hamid ka ce. Saude Kanwarka ce, don Allah ka yi haquri ka fada min gaskiya, ya ka ke da Saudat tsakaninka da Allah?� Hamid ya dan zuba mata idanuwa yana mamakin tambayar tata, kafin lokaci guda ya sauke numfashi; “Duk cikin magarta babu wadda na fada miki ba daidai ba, Saudat Kanwata ce wani abu ne likita?" Dr. Mariya ta koma ta jingina da bayan kujerarta cikin sanyin jiki ta girgiza masa kai alamar a’a kafin ta buda baki, “Saudat ta samu tsagewar qashi a hannunta na dama sannan a qafarta ma ta goce, sannan akwai buguwa a qashin bayanta duk da dai buguwar ba ta cossing din wata matsala ba, amma na yi . � mamakin irin wannan manyan ciwuka haka a . jikin mace, kuma qaramar yarinya ga shi ka ce ba hadari tayi ba, ba komai ba�. Hamid ya ce “Wallahi ba hadari ba ne, duka ne kawai". Dr. Mariya ta ja wani tsaki-kafin ta ce “A gaskiya akwai marasa tausayi a duniya, yanzu ko dabba ai ba a yi mata irin wannan dukan ba�, Ta qara jan wani siririn tsaki sannan ta ja dan siririn gilas dinta ta sanya a idonta, tare da janyo biro ta yi wasu rubuce-rubuce ta yage ta mika masa, ya sa hannu ya karBa tare da miqewa ya yi mata godiya ya fice. Dr. Mariya ta kwantar da kanta saman makarin kujerar tana kallonsa har ya fice daga ofls din nata. Hamid bai bar asibitin ba har garin Allah ya waye yana ta faman zurga-zurga siyo wannan auno wannan, karbo wancan har sai da aka kira assalatu sannan ya tafi masallaci ya yi sallah, a lokacin an daura mata karin ruwa, yana gama sallar ya dauki mota ya fice don hado mata� abin karyawa, sannan ya wuce gida, kai tsaye restaurant ya nufa ya yo take away sannan ya fito ya siyi fruit da kayan tea da duk abin da yasan za ta iya bukata sannan ya dawo asibitin a lokacin kuma ya iske Doctor na ta nemanshi aka ba shi wani list din abubuwan da zai siyo, kuma sai ya fita asibitin, Hamid ya sauke numfashi don yasan yana zuwa yanzu Dad dinsa ya gama Kuluwa don tun cikin daren jiya ya keta faman kiran wayarsa yana fad‘a masa ga shi nan za shi nan, daga qarshe ma sai ya kashe wayar gabadaya tabbas ya san kuwa sunada dabi a gidan yau. Ya zura hannu cikin aljihunsa ya ciro wayoyin tare da kunna su sannan ya yi gaba yana ta faman sauri kamar mai shirin "tashi sama, ba shi ya samu ya yi saitin din komai ba sai wurin daya saura na rana, shi ma kuma yana kokarin tafiya Dr. Mariya ta tsayar da shi za ta rubuta masu sallama. Hamid da ke zaune bakin gadon na Saudat ya ji wani farin ciki ya kama shi, ya dafa gadonda Saude ta ke zaune a kai, wadda ta sha ledojin ruwa biyu, ta yi fayau kuma tana nan kamar an kulle biredi, muryarsa a sanyaye _ ya ce, “To yanzu idan aka sallame ki ina ki ke � ganin zan kai ki Saudat kafin in nemo mana mafita?" Saude ta lumshe idanuwanta wanda .damuwa ta ke cike fal a cikinsu, Hamid ya sake kiran sunanta, “Ki yi hakuri Saudat ki manta, insha Allahu lokaci ya yi da zaki dandani zaqin rayuwa ke ma kin ji?" ' Saude ta bude idonta da kyar tana kallonsa, aka turo Kofar dakin aka shigo daga ita har shi suka zuba wa mai shigowar idanuwa, ba kowa ba ne sai mahaifin Hamid, fuskarsa ba yabo ba fallasa ya shigo � Dr. Mariya na bayansa da takardu riqe a hannunta. Yana qarasowa tun kafin Hamid ya yi wata magana ya cire hannu ya zabga masa wani mari wanda ya sa shi saurin dafe kunci, Alhaji Bashir ya nuna shi da dan yatsa, ni za ka dauka mutumin banza ka nuna � wa duniya ban isa da kai ba? Wato har wannan � yarinyar ta fiye maka mu k0 Hamid? Kai yanzu in bacin ma ba ka da zuciya har ka sake kallon yarinyar nan wadda ubanta ya nuna bai sonka, bai Kaunar tarayyarka da ita, amma shine kake like ka nace har ka ke bibiyarta da aurenta? To wallahi ba za ka zubar min da mutunci ba, cikiri satin nan zan daura � maka aure da duk wadda tayimin tunda nalura auren ka keso, wuce mu je mutumin banza kawai, na san babu abin da ke dibarka ~ sai wannan kyan fuskar� . Hamid ya zaro ido tare juyawa baya, muryarsa a sarKake ya ce“Dad ka tafi zan zo don Allah 'ka dubi halin da yarinyar nan ta ke~ . ciki, ba ta da kowa sai ni sai Allah idan na tafi ' na barta zata iya shiga kowane irin hali, don � Allah Dad ka yi haKuri ka ba ni awa daya", Alhaji Bashir ya zuba masa idanuwansa cike da mamaki, kafin ya ce, “Ka san kuwa abin da ka ke fada Hamid? Wato har wannan abin yafi ni ke nan k0? Yanzu kai har kana da ~ hujjojin kare kanka idan iyayenta suka samu labari, yanzu har ka manta cin mutuncin da mahaifinta ya zoya yi mana har gida ke nan? To wallahi tallahi ka Kara minti biyar a nan ban yafe maka ba, mutumin banza kawai�. Ya juya a fusace ya bar dakin, Dr. Mariya ta matso daf da Hamid muryarta a sanyaye ta ce“Hamid ka yi .hakuri ka bi mahaifinka kada fushin Allah ya tabbata a kanka�. ' Idon Hamid ya kawo Kwalla cikin sarqewar murya ya ce, “Doctor ba ta da kowa baiwar Allah ce idan na tafi na barta ban san halin da za ta samu rayuwarta ba, na tabbatar tafiya in barta ita ce silar da rayuwarta� za ta salwanta". Dr. Mariya ta sa hannu ta dafa kafadarsa tana fadar, “Ka je Hamid nayi maka alqawarin rike Saudat a hannuna' daga yau har zuwa lokacin da za ku satelin da mahaifinka, na yi maka wannan alkawarin". _ Dadi ya kama Hamid ya soma zuba mata godiya, ya zaro wasu sauran kudin da suka rage masa ya mika mata, wadanda bai san ko nawa ba ne. “Ga wannan don Allah ki fara rikewa a hannunki kafin in dawo�. Dr. Mariya ta girgiza masa kai. “A’a, kai dai kawai ka je, ga Katina mu .yi magana�. Hamid ya karBa yana godiya, sannan ya zuba da gudu ya flce don tsoron cikar lokacin. Yana fita Dr. Mariya ta wuce ta nufi qofa, ta maida ta kulle sannan ta juyo ta dawo inda Saude ta� ke, wadda tunda mahaifin Hamid ya shigo ta lumshe idanuwanta tana maimaita innaIiIIahi saboda yadda ta kejin zuciyarta na barazanar tarwatsewa. Dr. Mariya ta dawo cikin dakin ta ja kujera ta 'zauna tana fadar, “Bude idonld ki kalle ni nan Saudat". Sosai Saudat ta bude idanuwanta wadanda suka yi jajawur tana kallonta, kafin ta ce, “Saudat waye mahaifinki?" Saude ta ji tamkar ta caka mata wuqa a kirji cikin dusasshiyar muryarta ta Malam bala. . Dr. Mariya ta ce, “Mahaifiyarki fa?� Saude ta dan yi shiru tamkar ba zatayi magana ba, kafin ta bude baki cikin muryar kuka,tace “Ban santa ba, banma taba ganinta ba tunda na tashi na ganni da Yayana Rabi’u da matar mahaifina Inna Laure, tunda na tashi ban san dadin uwa ba, ban san wani ' gata ba wanda da ke samu wurin mahaifinsa ba saboda ni. . .� . Saude ta saurara daga bayanin da ta ke saboda hawayen da ta gani suna zubowa daga idanuwan matar, idanuwan Saude suka yo warwaje muryarta a sarqaqe ta soma fadar, “Lafiya dai Doctor, me ya faru?� Dr. Mari'ya ta riko hannunta gam ta rike tana motsowa cikin kuka ta ce; “Saudat nice mahaifiyarku, nina haife ku da cikina tun... � � Kuka yaci qarfunta ta soma wani kuka mai cin zuciya. Saude kuwa dif ta tsaya da kukan nata tana kallon matar muryarta na sarkewa ta ce “Kece mahaifiyarmu? Idan ke ce ' mahaifiyarmu me ya sa ki ka tafi ki ka barmu? Me ya sa ba ki sake waiwayarmu ba ki ka manta da mu ki ka watsar da rayuwarmu kika wofintar da mu, k‘i ka bari aka tarwatsa mu, muka sha wahala muka rasa mataimaki a duniya, kowa ya tsane mun . Dr. Mariya ta yi saurin rufe mata baki cikin kuka tana fadar, “Ya isa! Ya isa haka Saudat wallahi ban bar ku ba sai don hakan shi ne mafita, ban watsar da kuba sai don ina jiye muku tsoron wahalar da za ku iya fuskanta idan na ce zan tafi da ku alhalin ni ma ban san inda zan nufa ba, ku yi hakuri Saudat ina .yayanki?�