← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 90

Sashe 17

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Yanzu zuwa ki ka ki ka kwanta dan kin raina mutane, ya yi miki dadi sosai wallahi. To sai ki fito ki shirya in ga ubandaya isa ya hanaki kije dubiyannan ki ciro cikin kayan da yake kawo miki ki sanya kin ji na gaya miki� Tana gama fada ta juya ta wuce abinta. Wasu irin hawayen bakin ciki suka zirarowa Saude ta yunkura ta mike jikinta ba kwari, ta fito ta janyo ruwa cikin rijiya ta dauko sabulu guda cikin kayan nasa da ya kawo mata ta nufi bandaki ta yo wankanta wanda rabon da ta yi irinsa ba za ta iya tuna shekarar ba. Tana gamawa ta fito ta nufi dakinta ta janyo mai ta shafawa fatar jikinta, ta zazzaga farar hoda a hannunta tamurzawa fuskarta, ta bude ledar da kayan ke ciki kala uku .ne daga wata atamfa ‘yar roba sai wani yadi mai santsi an yi masa dinkin riga da wanda, sai wani leshi marun an masa dinkin jaka tsaye. Saude ta dauko shi ta saka ta Ciro takalmin robar ta sanya ta kawo milk din hijabin da ke cikin kayan ta sanya, sannan ta fltO zuciyarta na faman suya. A lokacin Laure da ‘Yar Baba na zaune gaban murhu ana ta faman soyen kaji da sanrayin ta ya kawo Saude ta dubi Laure da idanuwanta wadanda suke san zubar da hawaye ta ce, ‘Na fito.� Laure ta dago tana kallonta, alamun mamaki bayyane a fuskarta qarara, wanda har ta gaza danne shi a zuciyarta sai da ta furta. “Saude ke ce haka? Dube ta ‘Yar Baba ki ga abun mamaki.� � Kallo daya ‘Yar Baba ta yi mata ta dauke kanta tare da jan tsaki, Laure ta kada kai kafin ta ce, “To sai ki tafi k0 wa ki ke jira?� Haka Saude ta kama hanya jikinta a sanyaye ta yi. gaba. � � Gidan Garba Gnrgu yana can qasan unguwarsu ta baya, haka Saude ta taka~ da qafa. Gidan qaton gida ne ginin qasa,~rabin katangar duk ta zube a Kasa wanda aka sa buhu aka zagaye. Saude tasa qafarta cikin dogon zauren wanda aka fito da Katuwar kwata ta tsakiyarsa har tsakar gidan, gaban ta ne ya shiga faduwa lokacin da ta sa qafa cikin soron gidan, ba ta san irin tarbar da za a yi mata ba, ta san mugunta ce kawai ta sa Laure ta ce ta zo gidan ba wani abu ba. Saude ta yi sallama a tsakar gidan wanda yake a hargitse sai ka rantse da Allah bai’taBa ganin Shara ba ga wasu manyan tukwane da murahu a tsakiyar tsakar gidan ko’ina komatsai ne a tsakar gidan ba masaka tsinke, ga yara nan suna ta faman tsalletsallensu a tsakargidan sai ka ce ba su taba ganin ruwa ba a rayuwarsu saboda tsabar Kazanta. Saude ta Kara daga murya tana sallama sannan matan da ke ta faman zirga-zirga suka ankara da ita aka amsa mata tare da . yi mata maraba, jikinta a sanyaye ta qarasa cikin, gidan tana danne fargabar zuciyarta. Daya daga cikin matan ta janyo kujera ‘yar tsugunne ta miqa mata ta zauna suka shiga gaisawa, wasu su biyu babu riga a jikinsu sun saki nonuwa a waje sai ka ce silifas suna ta harkokin su babu abin da ya dame su, sai Karamar su ce keda daurin qirji. Kai da gani ka san an yi masu kisan Kuli, an kashesu ko kadan baza akirasu da mata ba. Saude ta qakaro wani murmushi wanda iyakarsa saman laBBanta kafin ta ce, “Na zo ganin jariri ne.� Babbar cikin su ta ce, “Au! Ni dai na ce ba mu. , waye ki ba, suna daka ki shiga ki gan su.� mu kishi da jikannu wallahi, ba ta yiwuwa da sake an bawa mai kaza qafa� A daidai nan Saude ta fito tana qokarin sa takalmanta ta ji matar na fadar, “Munafuka ashe Ieken asiri ki ka zo in dai gidan Malam ne ki shigo kema ki zauna, sannu a hankali za ki koma yanda muke � Sauran matan dai babu wadda ta tanka, harkar gabansu kawai suke. Saude ta sa takalminta dai ta yi waje, tana jin Garba ya biyo ta yana fadar. “Tsaya Saudatu ki ga dakin ki.� Bata tsaya kulashiba tayi gaba da hanzarinta sai sauritake dankokadan batasan ta hada ido dashi, munin shi da qazantar shi kadai ta isa tasa ta tsane shi, to balle ga shi tsohon najadu ga nakasa kai shi dai abun ya yi masa yawa. Bata ankaraba tanata tafia cikin sauri tana zancen zuci, ba ta ji horn din da ake faman kwarara mata ba, saidai taji an hankadata gefe hankalin Hamid ya yi masifar tashi, ya yi saurin yin fakin din motarsa ya fito a guje: ya nufo inda take yana kokarin daga ta, Saude ta yi saurin mikewa dan gudun karya tabata shimaya dago da niyar yabata hakuri, su kai four eyes, ido hudu, wanda ya haifarwa Hamid da bugun zuciya mai tsanani. Cikin tsoro da rudewa Saude ta soma ba shi hakuri, kallonta yake ido cikin ido wani abu na faman zarya a cikin kirjin sa muryarsa a sanyaye ya ce.� Ai nine zanbaki hakuri nidana kadeki kiyi haquri wallahi ban lura da keba ne.� Saude ta kada masa kai sannan ta wuce shi abin ta. Hamid ya yi saurin bin ta yana fadar, ‘Don Allah dan tsaya mana ‘yanmata.� Saude ta waigo tana � kallonsa, ya dan gyara tsayuwarsa kafin ya ce ‘Don Allah idan ba za ki damu ba ki fada mini sunan ki.� . “Saude.� Ta ba shi amsa a taqaice. Ya girgiza kai yana fadar, “Na’am Saudat, don Allah idan ba za ki damu ba kimin kwatancen gidanku Saude ta waro ido tana kallon shi, alamun mamaki bayyane a fuskarta ta kasa ma magana, ya danyi murmusa kafin ya ce, “Ki yi hakuri kar kice na fiya shishshigi da yawa;� ' Saude ta dauke kanta kafin ta ce, “Lafiya dai ko? � “Lafiya kawai dai ina so inxo in Kara duba kine don ban sani ba ko wani abu ya same ki.� Saude ta wuce shi tana fadar, “Ni babu abin da ya same ni.� Hamid ya yi tsaye yana kallon tafiyarta hatta kusa Bacewa ganinsa, ya ja wani taqaitaccen murmushi murmushi mai sauti tabbas yau zuciyarsa ta samu abinda takeso,zaicigabada binta harya samu ya samo kanta. Ya juya ya shiga motarsa ya bi ta a baya harkofar gidansu ya rakota batasanai ba, sannan ya koma abin sa. Saude nashiga gida, Laure ta bitada kallo kafin ta ce, ‘Wai kin je gidan nasu kuwa?� Saude ta daga mata kai alamar eh laure ta yatsina fuska kafin tace “Amma abinda mamakine da akace min amaryarsa mugun kishine da ita aina dauka sai sun karya miki qafar baya.� Ta ja tsaki mts! “Sai ki wuce kafin tallar yamma ta qarisa Saude ta wuce dakinta simi-simi ba tare da ta sake tankawa ba. Tana shiga daki ta kwanta, wani irin abu ya tokare mata zuciya, ta lumshe idanuwanta fuskar mutumin nan ce ke mata gizo, har yanzu hancinta baidaina shakar kamshin turarensa ba mai sanyin kamshi. Dama yace yanasonta tabbas da saitayi kukan dadi. Makaskanciya irin ta a ce irin wannan namijin yasota aidakamar wuya wai gurguwada auren nesa. K0 ‘Yar Baba da ta fita komai ba ta samu kamarsa ba, ballantana ita mafi kaskanciya mai tsananin rauni Taja wani gwauron numfashi tare da saurin kawar da abin dake zuciyarta, don ta san k0 a mafarkinta hakan ba zai taba samuwa ba. Washe gari Saude ta dawo daga tallar safen ta, sannan ta dauro alwala ta yi sallah; sannan ta fita� tsakar gida ta zauna, Laure ta sauke alalar aka zazzage mata a bokiti ta dauka ta fice abin ta. Hanyarta ta kullum yau ma ta ita ta bi idonta na saman hanya ta wuce ta qofar gidan Alhaji Bashir, Hamid da ke zaune saman teburin maigadi ya ga tahowartaya zabura ya mike, ya dubi Malam maigadi yana fadar. “Ina zuwa Baba bari in dawo.� Bai jira abinda zai ce ba ya yi saurin bin ta dan kar ta Bace masa. Saude ta tsinci muryarshi na fadar. “Assalamu Alaikum. � Ta waigo tana kallon shi da mamaki a fuskarta ta kasa bude baki balle ta iya furta wani abu, Hamid ya yi murmushi kafin ya ce, “Ruwan zuma ne ni ba madaci ba na kasance mai began ki tun a lokacin da na soma ganin ki ba wai sha katafi ba, mene na tunanin a kan hakan?� Saude ta fara nutsuwa tana kallon kyakkyawar fuskarsa, wadda ta qawatu da dogon hanci da yalwatattun idanuwa wata nutsuwa 'ta dirar .mata muryarta a sanyaye ta ce, “ZaBina ba tsakanin zuma k0 madaci ba ne, kyakkyawan zabina shi ne yawaita ayyuka, masu kyau da gujewa munanan dabi’u na kasance mai zurfin tunani da. Kwakwalwa ba da zuciya� ba, me ye tunanin ka a kan hakan?� Hamid ya dan saurara kafin ya ce, “Ikon Allah ga .shi nima yanzu haka Dady jirana yake, amma ba damuwa, ki fada masa zuwana gobe insha Allahu zan dawo.� Saude ta amsa da to, sannan ya juya ya tafi ta raka shi da idanuwanta. Ikon Allah mai tsaida wando ba zariya. Mamaki da al‘ajabi su suka dabaibaye zuciyar Saude, har yanzu bata fidda ranta da cewa mafarki take ba, za ta iya farkawa a kowane irin lokaci. Ba Washe gari Saude ta dauki tallar wainar .ta. Bayan ta siyar karfe sha daya da ‘yan mintuna ta dawo, Laure ta hada' ta da sanwar alala duk da matsananciyar ranar da ake kwalawa haka ta zauna a tsakar gidan gaban murhun sai gumi ke tsiyaya a jikinta. Tamkar daga sama yaro ya shigo ya yi sallama, Saude ta amsa tana kallon shi, ya ce, “Wai' ana sallama da Malam in ji wani mutum a waje.� Saude ta nuna masa dakin Laure da hannu tana fadar. ' “Shiga can ka fada masu.� Yaron ya wuce ita kuma ta ci gaba da abin da take, yaron bai yi minti biyar da fita ba Malam Bala ya fito cikin shirin tafiya masallaci kasancewar yau Juma� a bai fita kasuwa da wuri yasa kai ya fice Tsawon wasu mintina da suka haura goma zuwasha biyu sannan� ya dawo gida yana faman Kwalawa Laure
Chapter 17 · 0% Book details