← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 90

Sashe 25

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta dauke ki don Hajiya Kande ce min ta yi ta kawo mata yara ‘yan mata sun fi guda talatin tana cewa ba su yi mata ba, don haka saiki kula ni dai kin ga tafiya ta.� Ta mike ta bar Saude na zare namujiya, zuciyarta na faman kaiwa da kawowa, a yanzu ma kukan ya gagare ta' saboda tashin hankalin da take ciki yanzu ya fi gaban kwatance, tunaninta daya yanzu wace irin rayuwa ce za ta yi a gidan da ba ta san kowa ba? Wane irin� qalubale ne yanzu kuma za ta fuskanta? ' Ta Iumshe idanuwanta Kirjinta na barazanar � fashewa, ga� bacci, ga yunwa, ga gajia, ga uwa-uba fargaba da tashin hankali da suka� dabaibaye zuciyarta. Tana nan zaune tana muzurai ta ga wata dattijuwar mace ta shigo falon sai dai ita da ganinta Bahaushiya ce wadda shekarunta ba zasu wuce arba’in ba. Ta dubi Saude cike da kulawa kafin tace, “Ki taso muje in nuna miki masaukin ki.� Saude ta yunkura ta mike tana jin tamkar za ta. kifa saboda rashin kuzari. Ta wata hanya ta ga sun bi ta cikin falon sai ga su sun flto wani Karamin bedroom shi daya, ba wasu karikitai a cikinsa sosai, � karamin gado ne kwara guda mai kyan gaske kwanciyar mutum guda, sai wardrobe dinsa a gefe, shi kenan sai kafet da ke malale a dakin mai laushi. Matar ta juya ta dubi Saude tana fadar, ‘Nan shi ne dakin da Hajiya ta ce a sauke ki da fatan za kiyi . farin ciki, don gaba daya ma’aikatan .gidan nan masaukinsu a waje yake sai ga ki ke daga ~zuwan ki anwareki, natayaki murna." � Saude dai ba ta ce komai ba don ita abin da ke cikin zuciyarta yafi gaban wannan. Ta zauna gefen gadon wanda ya sha lallausar shimfida ta ci. gaba da bin dakin da kallo, wanda take ganinsa ‘tamkar wata aljannar duniya. Matar ta sa kai ta fice saboda ganin hankalin Saude baya kanta. Ba ta jima da fita ba sai ga ta ta dawo hannunta riqe da plate da ke rufe, tare da pure water ta ajiyewa Saude ta juya ta fice. Jikin Saude har rawa yake wurin saukowa ta bude plate din, ta kafe idanuwanta saman abincin. Shinkafa ce jaloup babu ko wadatar kayan miya a cikinta. Saude ta sa cokali ta soma ci, sai dai bakinta ya gaya mata dan ba ta yi tunanin shinkafar za ta yi dadi a yanda ta ganta ba. Hannu ba ka hannu kwarya haka ta rinqa cin abinci, lokaci guda ta kawar da shi, sannan ta dauki ruwan ta fasa ta shanye shi tas. Tana sauke ledar ta saki wata� nannauyar gyatsa, idonta ya soma lumshewa ta yunkura ta haye kan gadon ta kwanta. Tana kwanciya wani barci mai nauyi ya dauke ta. Ba ta sake motsawa ba sai lokacin da ta jiyo ana ta kiraye-kirayen sallar Asuba, ta yunkua ta mike tana faman zazzare idanuwa can ta hango wata kofa jikinta na rawa ta nufe ta, ta bude ta tsaya sororo � tana kallo; 'an qawata wurin da kayan qawata bandaki. � ' � Da sauri Saude ta maida ta rufe dan ita a zatonta wani dakin hutawa ne, ta dawo ta zauna tana san yin sallah amma ba ta san inda za ta kama ruwa ba, balle , ta dauro alwala. Da ta gaji da zama ne ta koma ta kwanta. � Sai dai a yanzu ba barci take ba. idonta biyu, tana kwance tana tunani, wai ita ce yau a kwance saman lallausan gado irin wannan, ko a mafarkinta bata taba tunanin hakan ba. Fargabarta guda yanzu yanda ta ga matar gidan da ganinta tasan bata da mutunci, dan tunkan su hadu wani irin tsoranta ya mamaye zuciyarta� Tana nan kwance tana juyinta, ita kanta ba ta san awannin da ta kwashe ba, ta ji motsin ana shigowa dakin ta yunqura ta tashi zaune tana kallon mai shigowar. Matar Jiya ce ta shigo da sallamar ta, a yanzu ma hannunta na dauke da plate da cup a sama sai ruwa guda daya a dayan hannun ta ajiye, Saude da ke kan gado ta amsa mata sallamar ta tare da gaishe ta, ita kuma matar ta dan zuba mata idanuwanta kafin ta ce“Yau dai kin yi kwanciyar kadaici k0 ya ki ka ji gidan namu?� Sande ta yi murmushi ba tare da ta tanka ba, matar ta Kara gyara zama tana fadar, “Kin ga dai matar gidan sai kin yi takatsantsan dan ba ta da kirki, yanzu dubi duk dukiyar mai gidan nan amma abincin su daban na masu aiki daban. Haushi ya kama Saude a duniya ita akwai ta da surutu da naci amma ba ta iya gulma ba, dan haka cikin qosawa ta dubi matar tana fadar, ‘Don Allah inane bayan gida in je in kama ruwa har yanzu ban samu na yi sallah ba � Matar ta ce, ‘Wane bayan gida kuma bacin wancan.� , Saude ta waro ido tana fadar, “Yanxu wancan kewaye ne?� Matar ta yi murmushi tare da fadar, “Taso muje in nuna miki yanda za ki yi amfani da 'su Saude ta yunkura ta mike ta bi bayan matar. Daya bayan daya ta rinqa nuna mata yanda ake amfani da komai da yake kwanyar tata a bude: take, a take: ta dauka, don haka suka fito, matar ta tafi ita kuma ta haye saman gadon ta janyo plate din ta bude, soyayyan dankalin turawa ne da kwai sai ruwan tea dan tsururu mai kama da fitsarin godiya. Dadi ya kama Saude yau za ta yi karin kumallon ‘yan gayu. Ta tisa dankalin tana ci tana faman santi a zuciyarta yanzu dama wannan shi ne rayuwar da masu aiki ke yi a gidajen da aka kai su aikatau? A gaskiya suna morewa don ita in dai za ta rinka samun abinci mai rai da motsi irin haka, to ai ba aikin da za,a sata a ,ciki batayiba bayan ta kammala sannan ta kwashe kayan ta ajiye gefe ta mike ta nufl bandakin ta dauro alwala ta tayi sallarta. Tana gammawa ta kishingida saman kafet din aiko nannauyan barci ya dauketa saiji tayi matarnan tazo tana tashinta ki tashi hajia nason ganinki A falo yanzu nan da minti biyar Hajiya zata sauko ta ki gana da ita.� ‘Yan cikin Saude su kai wata masifar juyawa, alamun tsoronta ya bayyana a fili qarara. Matar ta-yi murmushi ta mike tana fadar. “Hajiya na da matukar kwarjini a idanuwan kowa, ki dake ki fltO yanzu dan kar ta riga ki fitowa ki samu matsala.� Ba ta jira abin da Saude za ta ce ba ta juya ta fice, ta yunkura da hanzarinta ta nufi bandaki ta wanko fuskarta da bakinta jikinta sai faman rawa yake tamkar wadda za ta gana da Azara’ilu ta fito falon, Wanda yake tas-tas tamkar ba a shigwarsa saboda tsabar gyara. Saude ta raba daga qasa ta zauna zuciyarta na barazanar fashewa, don ta san yau za ta wuni anan ba ta fito ba. Sai dai da mamakinta ba ta kai minti biyar da zama ba ta jiyo Kamshin turarenta mai kwantar da hankali, zuciyar Saude ta tsananta bugawa da sauri-sauri, tamkar ana buga ganga, da Kyar ta iya daga kai kadan ta dan saci kallonta. Sanye take da wata dakekiyar shadda baka ‘yar Mali, dinkin riga da siket sun bala’in kama ta, an yi mata aiki da jan zare da fari da kuma kore, kwalliyar nan da gani ta kanti ce, tun daga hannuwanta zuwa qafafuwanta da wuyanta gwala-gwalai ne sai daukar ido suke takalmi ne baki mai masifar tsini a Kafarta. A yanzu idanuwanta rufe suke da baKin gilas din da . ya mamaye mata fuska,‘da makullin mota rike a hannunta tana kadawa, ta qaraso ta zauna saman daya daga cikin kujerun da ke baje a falon ta dora Qafa daya kan daya tana kadawa Saude ta zube tamkar mai shirin yi mata sujjada. Asma ta taBe baki tana yatsina fuska tamkar wadda ta ga abun Kyama ta daga mata hannu. “Ya isa bana san yawan gaisuwa, ya ya sunan ki?� . ~ Muryarta na rawa ta ce, “Sande.� Ta yamutsa fuska tamkar ba .za ta sake magana ba can ta ja fasali kafin ta ce, “Malama Saudat na san dai kin san nan k0 gidan waye a qasar nan aka kawo ki ba ki da bukatar sai na maimaita miki?� , Ta dan yi shiru tamkar wadda maganar ke mata � wahala kafin ta ci gaba, “A dan jiya zuwa yau nasa a , dan yi mini binciken ki a bugi cikin ki dan a fahimci idan kina da yawan surutu. Is oke zuciyata ta nutsu da na dauke ki aiki, ni dai ba mazauniya ba ce ‘yar siya ce ba ni da time din kaina ma ballantana na wani, kullum cikin sabgogina nake; Don haka na ce a samo mini yarinya mai nutsuwa wadda _zata kula da maigidana. za ki tsaya ‘yar aiki a sashin maigidan, idan ki ka gaza kula da shi kuma zaki fuskanci fushina. Aikin ki shine zaki rinqa kula da abincinsa, abin shansa, gyaran sashinsa, wurin hutawarsa. Ki nutsu ki fahimci abubuwan da yake so da wanda baya so akwai lokutan da baya san magana, ki nutsu ki fahimta kar ki kuskura ki rinKa cika shi da yawan magana, baya san yawan kallo koda yaushe yana bukatar abu mai sanyi kusa da shi Yana cin abinci sau hudu a rana, yana shan fruits da daddare around 12:am kuma yana shan coffee, yana tashi daga barci qarfe bakwai, yana motsa jiki a lokacin da ya farka yana gamawa zai sha tea, sannan ya tafl ya watsa ruwa. Yana karyawa da misalin Qarfe goma na safe. � Wannan shi ne tsarinsa, da fatan za ki kula, duk yan aikin da na daukar masa rashin fahimtarsa ne da basayi kesa inakorarsu. Ayanzu kece damata ta qarshe daga ke idan ki ka kasa kula da shi ba ' buKatar a Kara kawo masa wata, don haka ki tsaya ki nutsu ki fahimce shi ban san sakarci, idan kin yi aiki irin yanda yake so ni zan rinqa biyanki nera dubu ashirin duk wata. Da fatan kin fahimta?� Saude ta daga mata
Chapter 25 · 0% Book details