← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 90

Sashe 10

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

kwanta Washe gari tunda safe Saude ta yi Shara ta kai markade, ta dawo sannan ta debo ruwa cikin rijiya ta rafta tayi wankanta babu soso babu sabulu, � tana gamawa ta fito ta nufl dakinsu Laure na kallonta bata dai tanka mata ba, sai Ma tsakin da take ta faman ja akai akai. Saude ta dauki kayanta ta sanya sababbi tas sun mata kyau sosai, Rabi u da ya dawo daga dibar ruwansa ya shigo yana kallonta cike da sha’awa yace“tace yya nayi kyau Yace eh mana Saude ai ke kyakkyawa ce ”Ta kada kai tana fadar, “Amma kullum mutane sai su rinka ce mini Kazama mummuna har yaran unguwar nan wai ba za su yi kawance da niba, sai dai da ‘Yar Baba, wai ita ce Kawarsu mai tsabta, ba ‘yar talla ba, amma Yaya ai ka ce ina da kyau k0?� Tausayinta ya kara kama Rabi’u, yaji tamkar zai mata kuka ya daga mata kai alamar eh, babu alamar kuzari a jikinsa. Saude ta sanya takalmanta sannan ta mike ta dube shi. “Taso mu jc Yaya, kada rana ta yi.� _ ‘Rabi’u ya mike suka fita yana riqe da hannunta zuciyarsa cike da tausayawa. Laure da ke zaune saman kujera ‘yar tsugunne gaban murhu tana qukkulla waina, ta ga sun fito, ba ta san lokacin da ta ture tiren ba ta tashi tsaye idonta a warwaje tana fadar. “Me nake gani ni Laure, me zan gani haka?� Rabi’u ya kafa mata idanuwansa kafin ya ce “Makaranta zan kai ta baki gani ne kayan makaranta ne a jikinta." � ' Laure ta ce, “Karya ka ke wallahi idan ka ga Saude ta yi makaranta to ba na numfashi ne, don har abada ba za ku taBa morar� rayuwar duniya ba, in dai ina raye kuma Saude talla za ta yi min ban yi niyar ta yi karatun bokon ba, wato abun ma ya zama gasa kenan, tunda an sa ‘Yar Baba kai ma bari ka kulla ka sanya ta. To ba ka isa ba wallahi ka yi kadan ka nuna mini iyakata ban ga bayan ka ba kowaye kai wallahi.� Rabi’u ya gifta zai wuce yana fadar, “To sai ki gayawa kaji dan su tantabaru tashi suke." Laure ta sa hannu ta riko Saude da qarfi tana fadar qarya ka ke wallahi ba za ka kai ta makarantar ba talla za ta yi min yau sai na ga qarshen danyan kanka ba dai kai dan rashin kunya ba ne. Rabi’u ya ce “Sakar ta kar ki karya ta, tunda ba ke ki ka haife ta. ba, ba ki san ciwon taba.� Laure ta ce, “Aikin banza ruwa biyun k0 ka manta nan aka karma uwarku da kwarto cikin daki?� Ai dama shi dan zina har abada bai ganin kowa da mutunci, dan iska dan asara.� Bakin ciki ya cika Rabi’u zuciya ta zo masa iya wuya cikin Bacin rai ya ce ‘Wallahi ni ba dan asara ba ne kuma uwarmu ba mazinaciya ba ce face ke ce babbar la’ananniyar da ki ka tura mata sharri, kuma insha Allahu a sauna sai sharrinki ya qare Tun kafin ya rufe bakivLaure ta share shi da wani gigitaccen mari mai kummatar da qaramin yaro cikin zafin nama Rabi’u ya. dago Zai shara mata nasa marin ya ji an rike hannunsa, cikin Bacin rai Malam Bala ya shiga dauke shi da nashi marin hagu da dama. , Rabi‘u ya dafe kunci da baki wanda tuni har ya fashe jini ya kwararo cikin qunar zuciya Malam ke Lol ya abin ya kene mu kubiyonii donjin ci gaba sannan idan naga comment da yawa dan anjima xan iya sake muku post. [1/17, 7:44 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚 [1/17, 7:48 AM] A A Dboy: *YAR TALLA*
Chapter 10 · 0% Book details