Sashe 33
Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
masu Kin ta take haduwa, a duniya yayanta ne kawai ya taBa sonta, sai kuwa Hamid, mutum na farko da ya nuna mata qauna da soyayya ita kanta duk da ba ta san meye so ba, amma ta san tana san Hamid dan ta san wahalar da take sha gidan su ta linka ta nan gidan sau goma, amma kullum burinta ta samu ta bar " gidan ta koma gida k0 ta hadu da Hamid dibta kuIlum addu’arta kenan musamman idan ta zo kwanciya bacci. “Wayyo Allah ya Ubangiji gani gare Ka Jin alamun taflyar da ta yi, ya sa ta saurin dago kai. Dr. ne ya dawo daga rakiya, gaban Saude ya yi Wata mummunar faduwa ta yi saurin ja da baya tana ba shi hakuri, da kukanta dan gani take dukanta zaiyi Dr... ya ja ya tsaya cak yana kallonta ya ma rasa me zai mata ya huce haushinsa, ya lumshe idanuwansa lokaci guda ya bude ba tare da ya yi magana ba ya matsa da niyar isa inda take ashe bai sani ha ta ajiye tiren kayan abinci a gun « Sai dai ya ji ya yi karo da wani abu, ya fasa wata ‘yar siririyar qara ya durkusa, ya rike babban dan yatsansa, wanda tuni har ya soma zubar da jini abin ka da lallausar farar fatar da hutu ya jika, hankalin Saude ya yi masifaffan tashi, tayi kan shi tana _ fadar ~ ‘Wayyo Allah na shiga uku na lalace "ta rike kafar tana kuka, ‘Wallahi ba da gangan na ajiyeba Na rantse da Allah â€? ya runtse.idanuwansa ba tare da yace da ita komie ba “ta rasa yanda za ta yi ta kalli kan kayan abincin ashe, da yar qaramar wuqar yanka cake da ita ya ‘yi karon harta yankeshi hankalinta ya qara masifar tashi yanda ta ga jini na zuba ba wai kadan ba; ta rude ta cire himar din » kanta tasa hakori â€ta"yaga shi ta yagi kadan ta daure masa dan yantsan Dr ya bude idanuwan shi da Kyar yana kallonta yanda tabi ta gigicc ta rude fada take, ‘Sannu Wallahi bada gangan na ajiyeba, ganin yanda ta fita hayyacinta yasa ya nemi fushinsa, ya rasa. Ya'sake lumshe idanuwansa sbaoda radadin da qafar kemasa yce ‘Dauko min wayata in kira likita. â€? .Hankalin, Saude ya: qara "tashi da taji an ambaci likita, ashe abin mai girma 'ne. Ta. sake rushewa da :kuka ita ko yau ta san hukuncinta mai girmane taje ta dauko masa wayar ta rankwafa ta mika masa, ita ta zauna daga gefe tana 'kallonsa Hankalin ta ya kara tashi tsoronta daya kada â€? jininsa ya qare, don ta ji ance jinin mutum na Karewa mutuwa zai yi, ta sa hannu ta gage hawayenta cikin muryar kuka ta “ce“K0 in kawo ‘maka gishiri ka barbada tunda jinin yaqi tsayawa?â€? Dr. ya waro ido yana maimaita gishiri kuma? Saude ta qara marairaicewa “Don Allah in kawo maka kada jinin ka ya qare.â€? Yanda ta yi maganar a shagwabe shi ya narkar da zuciyarsa ya ji har cikin tsikar jikin shi. : Ta sake langwaBe kai “In kawo?â€?-. Bai san lokacin da ya daga mata kai ba, Saude ta zabura ta mike da gudu ta fice, Dr. ya raka ta da manyan idanuwansa masu saurin daukar hankalinâ€? yan matan zamani â€? Meke son faruwa da ni ne? Ya tambayi kansa. Tambayar da ba shi da mai amsa masa. Saude ta dawo da sallamarta, ta durkusa ta mika mesa gishirin, ya lusmhe idanuwansa ba tare da ya yi magana ba, ta ce, “In barbada maka?" ' Ya daga mata kai alamar eh, ta durkusa ta â€? ‘warware danrin' sannan ta soma barbada masa gishirin, inda naman ya Bantale, bai san lokacin da ye saki qara ba ya rike hannunta saboda azaba. » â€? Saude ta watsar da gishirin cikinâ€? ta rike qafar tana fadar, “Yi hakuri don Allah‘da zafi ko?â€? Ya girgiza mata kai alamar a’a, ita kanta ta san ya fada ne kawai. Ta rankwafa kanta ta shiga hura masa .da iskar bakinta , tana yi tana sharar kwalla yau Allah kadai ne zai crce ta a gidan. ' Wani irinâ€? tausayin; yarinyar ne ta kama kowace Kofa ta 'jikin sa tausayinsa da ya gani Karara a idanuwanta ya narkar da zuciyarsa, ya ji tamkar yasa hannu . ya shafi gashin kanta wanda kana kallon shi kaga gashin Fulaniâ€?: ta daure shi tamau kamar gammo a kanta, ya Kara laushe idanuwansa a hankali. ;*A haka har likitan yazo ya same su, ta yi saurin , share hawayenta tare da gaishe da likitan ya amsa cikeda kulawa sannan suka gaisa da Dr. ya zauna yana fadin garin yaya haka? Dr cikin sanyayyar muryar shi ya ce ‘Tsautsayi kawai likita yace to allah ya kiyaye gaba .â€? Ya fada yana kallon shi cikin kulawa ya Janyo yar akwatin‘sa ta duba marasa lafiya, â€? saude ta miqe da hanzarinta, Dr ya, dubeta. . â€? Yace ina zaki kuma Cikin sarkewar murya irin ta wanda ya gaji da kuka ta ce, “Zan fita ne ba zan iya kallo ba.â€? Ya zuba mata idanuwansa yanda take maganar yaf8 komai daukar hankalinsa, ganin bai ce komai ba yasa ta juya ta fice ita kanta ta soma tsarguwa da kallon da yake mata yau, wanda ta kasa hada shi da irin Wanda ya saba yi mata a da. Kai tsaye Saude ta wuce daya Bangaren, tana shiga falon ta yi karo da Dillaliya a rabe gefen kujera ita kadai sai ka ce munafuka. Saude ta karaso da azamarta cikin doki ta zauna tana fadar “Aâ€? a Dillaliya kece yau a gidanmu, sannu da zuwa, ina wuni?" Dillaliya ta watsa mata wani kallo mai kama da harara, kafin ta ce“Ina ne gidan naku? Lallai samun wuri tusar asuba, ashe ke nan har gidan , ya zama naku, kai gaskiya ne, an zo birni an asha jar 'miya ai dole a mance mafari. To idan kin manta bari in tuna miki gidanku na Katsina, a Katsinar ma qarshen gari inda k0 wutar nefa ba ta wadaci unguwarku ba, gidanku na nan gidan qasa an masa faci da buhu yana nan yanda ki ka bar shi kuma za ki koma ki same shi munafuka an samu wuri an Bade sai juya mazaunai ake ke da matar gidan baku da bambanci, fata ta murje anyi * kilin To ki sani kin kusa komawa gida,'dan an sa ranar auren ki wata biyu yau saura wata guda, keda Garba Gurgu, yana nan yana jiran ki." Gaban Saude ya yi wata mummunar faduwa ta ji â€? tamkar ta dora hannuwa aka ta rusa kururuwa, saboda tashin hankali da kaduwa. Ta kifa kanta da kujera ta saki wani irin kuka mai ban tausayi. Dillaliya taâ€? tabe baki tana fadar, “Kuka kama yanzuâ€? ki ka fara ni kam ina amsar albashin ki zan wuce yanzun nan don tun safe nake nan a jibge kamar kayan wanki, ungo wannan nataccen saurayin ki Hamid ya ce a kawo miki.â€? Da sauri Saude ta dago kanta don ganin abin da take mike mata. Wata doguwar ambulan ce, ta sa hannu ta karBa jiki na rawa. Dillaliyaâ€? ta ce, “Har na shiga mota ya zo da kansa har tasha ya kawo mini, ya gama ni da Allah ,in kawo miki,â€? ke kin san in bacin ya biya ni kudi masu kauri ai ba zan kawo ba. Saude dai jujuya takardar kawai take, tana jin wata irin soyayyar Hamid na mata yawo a zuciya, jin bai manta da ita ba shi ya mantar da ita kukan da take. Ta mike cike da dokin san ganin abin da ke cikin *‘ambulan din, Dillaliya ta dube ta, ‘Gidan wa za ki ai ba mu gama ba, kiyi maza ki tattaro mini abin da kika tara ko‘kina nufin haka nan ki ka zauna ki ka saki baki da ciki kina ta kwasar dadi ke da ki ka iya cin dadi.â€? Cikin sanyin jiki Saude ta ce ‘Ki yi hakuri Dillaliya wallahi ban ajiye komai ba, tunda na zo babu abin da aka ba ni.â€? Dillaliya ta cce“Ke dalla tashi' can har sai an ba ki keba ki iya ‘yan tattare-tattare ba, duk dan wani abinda kikaga anyi sake dashiki tattaraki boyeba Saude ta ce “Subhanallahi! Haba Dillaliya sata fa kenan?â€? Dillaliya ta ce “Ke gafara can sakarya ai idan ba ki sata kin Boyeba bikinki yazo ke za a bari da abin kunya, idan ko kin sata kin bada an boye miki ai kin san abin da ki ka yi â€? Wani inn takaici ya kama Saude wai a tura mutum sata yanzu idanâ€? yar tace ta sanya ta? Cikin sanyin muryarta ta ce, “Bari in shiga Dillaliya ki gaida gida ki gaida su ‘Yar Baba da Inna Laure da Baba na gode Dillaliya ta hayayyako mata cike da masifa “Idan ubanki ya ba ni kudin motar ba saiki tilasta ni na gaishe su ba, munafuka, mutuniyar banza, ai duk kyan gawa dai cikin Kasa za a turbune ta sai mu ga qarshen jin dadi da kyau.". Saude dai ba ta kula ta ba ta fice abin ta, tan shiga bangaren ta, ta fada kan gadonta ta zauna zaman Dirshan ta balle ambulà n din ta zazzago abinda ke ciki Wasu kudi suka fado yan dari bibbiyu rafa guda tare da yar qaramar wayar saluka Saude ta shiga jujjuyawa cike da mamaki ta qara zazzagawa saiga wani zobe ya fado tare da wata yar takarda da aka cika da kyakkyawan rubutu ta zubama rubutun ido dukda batasan abinda aka rubuta dinba amman rubutun ya burgeta ta dauki zoben nabazurfa dan sirir tana jujjuyashi shima zoben ya birgeta ta zura zoben a dan yatsanta qarmi na hagu Zuciyarta ta kwadaitu dason sanin abinda ke rubuce a cikin takardar Ta linketa da kudin ta boye sannan ta dauki wayar tana lallatsawa dukda bata iya wayaba amman zuwanta gidannan ta iya kunnawa da kashewa da kuma amsa kira sbd akwai wayar tarho da akasa a dakin don kiran gaggawa Saude ta kunna wayar tana qara jujjuyata wayar na kunnuwa kira na shigowa dukda batasan lambar wayarba amman zuci yarta ya bata hamid ne don haka hannunta na kyarma ta daga kiran ta kara wayar a kunne tareda sallama