← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 90

Sashe 56

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saudat na kife a katifarta tana rusar kuka, Iyah ta shigo, “Saude tashi maza mu tafl" ,, Saudat ta dago da sauri tana kallon Iyar da jajayen idanuwanta, ji take tamkar zolayarta ta ke Iyah kuwa ta mika hannu ta kamo hannun Saudat tana fad'ar, “Tashi. maza mu tafi, yau mu ai mun ga ikon Allah�. � Saudat ba ta iya yin musu‘ba ta mike ta bi Iyah suka fito, inda suka iske har hare ta kai qofar gida don haka suka rufa mata baya suka rankaya, Saudat jin abin ta ke tamkar cikin mafarkinta, to me ke faruwa ne? "� """"""""""". '"""""""" Tunda Dr Ahmad ya yi wa motarsa key ya dauki hanya tafiya kawai yakr amma ba tareda yasan irin tunaninda yakeyiba gudu yake saman titi ba na wasa ba, tamkar wanda ke dambe da iske,, Allah dai ya kawo sa garin Abuja. . ~ Babu inda ya yi wa tsinka sai gidan iyayensa; yana faka motar tasa ya kulle murfin , motar ya sa qafa ya shiga tamkar'wani mara lakka� ya na cikin gidan nasu, da ‘yar siririyar sallamar da shi kadai ya san yayi ta. � Babu kowa a falon shiru babu komai sai kukan AC,kamar wand aka hankada ya fada saman doguwar kujera ya rungume fitan kujerar ' tare lumsha ,idanuwansa tamkar wanda ya sha wani abin maye, yana shakar sanyayyen qamshin turaren wuta dake tashi,sannu ahankali yana falon tsawon mintunan da suka haura talatin babu wanda ya fito falon , sai can Hajiyarsa ta fito daga falonta da alama ma ma fita za ta yi don� sanye ta ke da atamfa super Holland wadda . aka yi wa dinkin riga da siket, ta da wani qaton mayafi wanda tsadarsa ta tasar wa dubu talatin. Hannunta na riqe da hannunta na riqe da qaramar jaka bazaka taba cewa ta haura shekaru arba”ba, amma nan sittin ne hard ‘yan kai. < Kodayake k0 shi uban gayyar a yanzu talatin da shida ne ke kanshi Ganin Dr a falon ya bawa Hajiyar mamaki Dr. ya bude idanuWansa da gyar yana . kallonta tamkar wanda ya yi cutar shekara guda wuyansa tana fadar, “Lafiyarka kuwa Ahmad? Me ke damunka ne " Dr. ya dago hanunsa da kyar ya dafa kansa .kafin ya ce “Momy kaina kamar zai rabe biyu, zuciyata fashewa za ta yi�. Hajiya ta dimauce ta soma kiran sunan Allah tana fadar, “Yau ni na shiga uku Ahmad tashi mu je in kai ka Maitama District Hospital a duba min kai". Dr. ya girgiza mata kai, “No Momy ki kyale ni don Allah, ciwona ba na asibiti bane, bugun zuciya ne idan na dan samu relive zai damau. . Ta ce“Kamar ya zai daina Ahmad? wacce irin damuwa ce wannan da ta ke qokarin kai ka kabari?� Dr. ya ja dogon numfashi kafin ya ce “Momy sun hana ni Saudat, wallahi Momy ina sonta, taBa zuciyata ki ji yadda ciwo ke� nuqur kusar zuciyata". Momy ta dan zuba wa dan nata ido, kafin tace “To ita Saudat din sukace bazasu baka ita baka ita ba sai kace wani mai mugun hali? Duk duniyar nan da ma akwai inda zakaje neman aure ahana ka?”Dr. ya girgiza kai “Wallahi Momy baza su barni na auretaba don Allah Momy ki ba ni shawara, ya zan yi?� .. Hajiya ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ta raBa kusa da shi ta zauna, ta cusa hannunta 'cikin sumar kansa tana sosa . masa cikin Sigar rarrashi ta ci gaba da fadar. “Don Allah ku zamo mai tawakkali Ahmad, ka zamo mai juriya da rungumar abin da Allah ya qaddara maka, ka sani bai hana ka Saudat don ba ya sonka' ba, sai don kawai ya jarrabe ka Ya gwada imaninka, haba dana kai _ din fa mai kwarin zuciya ne, ina kwanjin dana � Sanka da shi? Haba dana ka zamo mai juriya kaji?" � ' Kai kawai ya iya daga mata ta ce � “Yauwa nawan daure ka tashi mu tafi aSibitin � Doctor ya duba ka yanzu mu dawo� , Baimusa ba yayunkura dakyar tana riqe da hannunsa suka fice ta sa direba ya jasu 'cikin babbar Jeep dinta suka nufi asibitin. Iyah na"riqe da hannun Saudat har suka isa gidan, ita dai tafiya kawai ta ke, amma ba ta san inda ta ke jefa Kafarta ba, sunsa qafa cikin zauren gidan ta ji gabanta ya yi wata mummunan faduwa, irin wadda ke sa mutum ya yanke jiki ya fadi. Suna shiga tsakar gidan suka yi karo da Inna Laure, wadda ke qoqarin hada hankalin gidan kasancewar duk ‘yan bikin sun watse tunda har isha ta karato ga shi kuma hadari ya gangamo a garin. Suna shiga tsakar gidan Inna Laure ta zabura ta mike tana fadar, “Me nake gani haka kuma ni- Laure, ba ku kai ta gidan nata ba ne k0 ya ya aka yi?� Iyah ta ja hannun Inna Laure ta damqa mata Saudat. “Ga amana mun maido, yarinya mijinta yace ya mata saki uku saiku nemi dalili a wajensa, mu kuwa mun tafi Allah ya ba mu alheri�. Suka juya suka yi gaba abinsu. Inna Laure ta hankade Saudat da ke hannunta tana kwalla wa Malam Bala kira, wanda ke qoKarin fitowa daga dakinsa yana zuba sallallami, kira yake“Me kunnena ke jiye min Laure?� Inna Laure ta taBe baki. “Abin da ka ji Malam ni ma shi na ji�. Malam Bala ya nufi Saude ya nuna ta, “Ke kuwa wannan yarinya ban ji dadin haihuwarki ba, wannan nan uwarki ta haifa min jaraba da alaqaKai, kalu’inna lillahi wa"inna ilaihi raji’un, keko yau sai kin bar gidan na gaji ba zan iya ba wallahi na gaji. . .� Saudat ta fashe da wani dan marayan kuka na rashin sanin madafa, ta dora hannuwa biyu a kai, ta rasa abin da ke mata dadi, tashin hankalin da ta gani Kiri-Kiri a idanuwan mahaifin nata shi yafi firgitar da ita, ta zuba wa Malam Bala ido wanda ke jin zuciyarsa tamkar za ta tarwatse saboda tashin hankali, wasu irin hawaye masu zafi suka biyo kuncinsa, cikin tsananin takaici da bacin rai ya ce. ; “Ai dole ya sake ki Saude, don idan ba dan iska irinki ba babu namijin da zai iya zaman aure da ke, amma ina so ki sani ni na riga na sauke nauyin da Ubangiji Ya dora min a kanki, don haka sai dai ki nemi inda zaki amma ba dai gidana ba, yadda ki ka taho haka 'zaki juya ki tafi duk gidan uban da zaki, kuma tsakanina da ke Allah ya isa ban yafe miki ba� Saude ta ji kalamansa tamkar saukar . ruwan zafl a jikinta ta durkushe a gurin tana wani gunjin kuka. ' � Malam Bala ya dube ta a fusace, “Eh ’zamama kikayi kenan kina kukan rashin kunyar, ai ko zaki bar gidan nan a nakashe�. Ya juya ya rarumo muciyar Inna Laure‘kafin ta yi yinkuri ya muka mata a baya .Saude ta fasa wata uwar Kara ta sheme a qasa Malam Bala ya hau maka mata muciyar � ' iya Karfinsa, ya hau fadar, “Ni za ki dauka dan iska? Ni zaki kawo wa shakiyanci a cikin gida? � � Ganin yana shirin kisan kai yasa Inna Laure ta riae‘Ke shi, ta soma ba shi haquri, sai data yi da gaske sannan tasamuya ya. kyaletaya ta nufi dakinsa yana sharar gumi, duk da kuwa ba � «lokacin zafi bane a lokacin. ~ , . Saude kuwa ko kwakkwaran motsi ba ta yi, saboda doguwar sumar da ta yi. Haka duk suka shige ciki suka barta ayashe tsakar gida kamar ba dan mutum ba. Tsawon lokaci wani irin iska mai hade daguguwa yataso tare dasaukar wasu ruwan sama masu qarfi tsawon lokaci ruwan na dukan Saude kafin ta fara motsawa sannu a hankali ta bude idanuwanta a hankali abubuwan da suka faru suka rinka dawo mata tamkar bidiyo. Ta runtse idanuwanta da sauri tanajin tamkar zuciyarta zata tarwatse, ta yunqura ta mike da kyar wata irin tsanar ’mahaifin natane maitsani ne tarinqaji zuciyarta batada wata bukatar data wuce barmasa akurkin gidansa dukda wani irin masifaffen ciwon da jikinta ke mata amma hakata takarkare ta fito daga gidan dukda juwar da ke faman rufe mata idanuwa. ga kuma tsananin ruwan saman, ga-tafiyar tata tamkar: ta ‘yan kayo saboda tsamin da jikinta yayi Cantaji andanno mata oda abayanta da qarfin- gaske Saude ta ji har cikin dodon kunneta tamkar zai rabe biyu gashi kuma an danne odar an Ki saki. Saude taji tamkar ta zuba da gudu saboda yadda ta ke jin hatta ‘yan � cikinta na amsa kuwwar odar sai dai ba qarfin jikin da za ta iya yin gudun, don haka ta durkushe a gurin. Cikin takaici Hamid ya Balle murfin motar ya leko da kansa cikin ruwan cike da masifa yana fadar, “Ke k0 wacce irin mace ce � ana miki oda ba ki ji, kawai ki zauna saman hanya k0 aljana ce ke ai kin kauce daga saman hanya donkar waniyazo ya takaki cikin rashin sani�. Saukar muryarsa a dodon kunnen Saude ya sa� ta saurin waiwayowa don tabbatar wa cikin wata rikitacciyar murya Hamid ya kira sunanta tare da zabura ya fito daga cikin motar ya nufo ta yana fadar, “Saude ke ce kuwa, ko dai gizo ki ke min?� Ya durkusa a ‘gabanta, “Lafiya Saude me ya fiti dake daga gidanki cikin wannan damunan?� Cikin kuka Saude ta some fadar. "Sakina ya yi Hamid, ya sake ni". Hamid ya dafe kai, “Innalillahi wa’inna ilaihirrajiun Wayaji miki wannan ciwon a jiki haka? Dubi yadda jini ke zuba a jikinki�.� � Sai a lokacin ma ta lura da wani irin kwasheshen ciwo da ta ji a gwiwar hannunta. . Hamid ya ce “Tashi !maza mu tafi asibiti kada jininki ya Kare�. ' Ganin tana ta KaKaniyar tashi ya sa ya sure ta da kuzarinsa ya sata a mota ya maida ya rufe, ya zagaya gidan direba ya shiga ya ja, kai tsaye ya nufi medical center da ita. Cikin .ikon Allah yana zuwa ya samu likita Dr. Mariya ta karBe ta aka wuce Emergency room da ita, abu kamar wasa sai da ' aka shafe fiye da awa guda Hamid na nan' zaune babu wanda
Chapter 56 · 0% Book details