Sashe 21
Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hawayen da suka tsaya da zuba daga idanuwan saude suka Ci gaba da zubowa tana sharBar majina kana ta fara magana. “Kamar yanda ka sani sunana Saude, tunda na . tasona bude idanuwana na ganni tare da Yayana,shine uwata shi ne ubana shine komai nawa. Bai barin nayi kuka , kullum burin shi ya samamin farin ciki da gatan da na rasa a rayuwa, Ni kuwa burina kullum in matsa masa in sanya shi yimin abinda baidai konyinsa Hamid ya ce, “To yanzu yana ina shi Yayan naki? � Saude ta Kara rushewa da kuka kafinn ta ce . an raba ni da shi, su suka raba ni da Yayana.� Ya ce, ‘Su waye?� Muryarta na rawa cikin kuka ta ce, “Baba da inna Laure.� Hamid ya ja wani numfashi mai nauyi yana jin yanda take ta faman kuka da shashsheka tausayinta mai tsanani ya shige shi, muryar shi a sanyaye yake magana. “Ina mahaiflyarki da mahaifinki su ke?" Saude ta ce, “Ban san inda mahaifiyata take ba, Ban taBa ganinta ba, wannan kuma da ka gani shi ne mahaifina, Inna Laure kuma matarsa ce ‘yar Baba ita kuma qanwata ce Hamid ya sake sauke wani nannauyan numfashi ya fahimci yarinyar tana cikin matsala, ya zuba mata idanuwansa farare tas cikin sanyin muryarsa ya ce, “Ki yi hakuri Saudat na fahimci irin abin da ki keji a zuciyarki, ki kwantar da hankalin ki insha Allahu na yi miki alqawarin taimaka miki da dukkanin karfina in dai ina raye sai na daga darajarki a duniya, sai kuma na wanzar da murmushi a idanuwan da Yaya ya bari cikin hawaye.� Ya dan qara numfasawa kafin ya ce “Ki je " 'lallar ki dawo, zan zo da daddare in same ki wurin tallarki za mu yi magana, amma don Allah ki daina kukan nan haka nan kin ji?� Saude ta daga masa kai tana goge hawayen da ke fuskarta, ya dan tsura mata ido da murmushi a kumatunsa ya ce, “To dan yi murmushi mana beauty *Dukda batasan abindayace ba,ammatayi murmushin kuma kalmar beauty din ta yi mata� dadin sauraro a kunne. Sai da ya ga tafiyarta sannan shima ya juya ya tafi zuciyarsa na raya masa abubuwa masu yawa. Da yamma likis Saude ta dawo daga wurin tallarta Laure ta jibgo uban wanki, sannan tace ta ' dora sanwar tuwan dare. Saude ta duka a gun ta yi kukanta har ta gaji sannan ta ja ruwa ta dora sanwar ta dawo ta ci gaba da wankin. Ana gama sallar Magariba Malam Bala ya dawo gidan, Laure ta shimfida masa tabarma a tsakar gida ta kawo masa fura da mafici ta zauna gefensa. Malam Bala ya bude furar ya soma sha, sannan ya dubi Laure yana fadar, “Wai ya suka yi da yaron nan ne Laure?� Ta taBe baki tare da furta, “Uhmm! Malam kenan, ai yaron dan iska ne takadari kana ganinsa kamar na kirki suna hira da ‘Yar Baba ya nemi taushe ta cikin zaure Allah ya rufa asiri yarinyar nan ta yi ihu, na kwaso da gudu na raka shi da bakin wuta har waje, mutane na ta bani hakuri suna fadar in kyale shi ai ni’wannan abu ya ci min zuciya wallahi har kuka na yi. Yanzu dan kawai an gan mu talakawa matsiyata shine za a shigo har cikin gida a ci zarafin mu. Kai Malam wannan abu da me ya yi kama?� . Tunda ta fara zancen ‘ya’yan cikin Saude suka fara juyawa wani irin gumi ya shiga tsatstsafo mata, take juwa ta kwashe ta, sai dai ta ganta zaune a gefen bokiti. Malam da tunda ta fara zancen ya hau sallallami, ai sai ya rufe furar yana fadar, “Wai harni za a ciwa mutunci a garin nan Laure na rantse miki da Allah sai na yi kararsa kotu, kuma ta addinin Musulunci.� Laure ta ce ‘Aa, Malam abin ai duk bai kai na kotu ba wurin mahaifinsa za ka gobe tunda sassafe ka kai qararsa ka ce ya jawa dansa kunne ga abin da ya yi maka in ba haka ba za ka sa hukuma ta (shiga tsakaninku.� Bakin ciki ya cika malam Bala ya zabura ya mike ya suri buta ya nufi bandaki. Laure ta tabe baki ta raka shi da harara a zuciyarta tana fadar sauna kawai. Ta yunkura ta mike ta dubi Saude da ke 'zaunc ta ce, “Toke kuma tsohuwar munafuka kin zauna kin kasa kunne kina sauraran jama‘a sai ki tashi ki dauki tallar gyadar ki tafl idan kin dawo kin qarasa wankin tunda cinikin na yauzu ne." Saude ta lallaba ta mike tana jin tamkar za ta fadi ta dauki tallar ta ficee, kuka maya gagareta idanuwanta sun yashee babu komai cikin zuciyarta sai duhu. ' ‘K0 minti goma bata yi da zama ba ta hango shi ya nufo inda take; yau sanye yake cikin manyan kaya, ‘na wani lallausan yadi milk colouz; mai hasken gaske dukda a'cikin duhu ne amma bata kasa ganin shekin yadin ba, kansa yana sanye da hula baka yasa bakin takalmi a Kafafuwansa, tun kafin ya Karaso kamshin tuiarensa ya daki hancin Saude ta lumshe idanuwanta, sai a lokacin wasu hawaye suka tarar mata � Hamid ya yi mata sallama tare da durKusawa gabanta, muryarsa a sanyaye ya ce “Sannunki yan matana barka da Kokari.� ' Saude ta bude idanuwanta tana kallonsa. hawayen da suka taru a kwarin idanuwanta suka ziraro � � Hamid ya mike tsaye ya ciro farin hankicif Dinsa daga cikin aljihu ya miqa mata, Saude ta girgiza masa kai don ta san k0 rike hankicif dinma kadai ta yi sai ya yi dauda, to balle ta goge fuska dashi wai sunan wani wai shi � Danduwala. . Hamid ya sake mika mata hankicif. din yana fadar :‘Wallahi sai kin goge garama ki karBa kawai� � ' Jim yanda ya yi saurin rantsuwar ne yasa Saude ta amsa ta goge hawayen, ya ce, “To bani abuna� Ta yi wani dan taqaitaccen murmushin da bai , wuce kan labbanta ba ta ya qara goge fuskar shi da shi sannan ya saka a aljihu yana fadar. “Wannan tafiyar yau ba ta ki ba ce wurin Baba nazo don haka ni kin ga taflyata." Bai jira abin da za ta ceba ya juya ya tafi abinsa zuciyar Saude ta qarasa karyewa ta kifa kanta saman kayan tallar tana rera wani irin kuka mai cin zuciya. . Hamid ya karasa Kofar gidan da qarfin zuciyarsa ya aiki yaro ya yi masa sallama da Malam Bala. Yaron bai jima da fitowa ba ya ce ga � shi nan zuwa, sai ga Malam Bala ya fito da alama masallaci za shi saboda an fara kiran sallar Isha’i, yana ganin Hamid a qofar gidansa ya ja ya tsaya yana fadar. “Malam laflya?� Hamid ya durKusa har qasa yana gaishe shi. Malam Bala ya ce“Kai dakata ban san rashin kunya ka ji har ni za ka dauka mutumin banza da WOfl, to ka je komai ka yi dan kanka ka, Allah ya isa tsakanina da kai, duk da ka gan ni talaka ina da wadatar zuci.� Mamaki ya kashe Hamid ya dago yana kallon Malam muryar shi cike da rudani ya ce Don girman Allah ka yi hakuri Baba wallahi ban san abin da nyi ba wanda kake fadarsa a yanzu« Malam Bala ya ce ‘Ai dama ba zaka san abin da kake; fada a kansa ba, tunda ka ci idon dan akuya ' amma abin da nake so da kai anan shi ne ka tashi ka ba ni Wuri kar in sake ganin ka gifta k0 qofar gidan nan, kuma zanje in samu mahaifin naka ya yi maka tsakani da� ya yana mutumin banza kawai� Yana gama fada ya juya zai tafi, Hamid na kiran � Baba don Allah ka saurare ni, amma bai kula shi ba , ya yi gaba Wani abu ya tsaya zuciyar Hamid, ya lallaba . � ‘ya mike jikinsa ya yi masa masifar sanyi ya nufi � inda Sande take zaune tana faman raira kukanta. � � « Tausayinta ya lullube shi ya kura mata ido ' na wani dan lokaci kafin ya soma magana muryarsa a ' sanyaye ya ce“Ba zan hana ki kiyi kuka ba Saudat, « dan zubar hawayenki ya zama dole na fahimci abin da aka shirya mana, amma don Allah ki yi haquri kamar yadda na dauki alkawari’n taimaka miki ba . zan fasa ba Saudat da yardar Allah sai na ga rayuwarki ta inganta, kar ma Wannan abun ya dame ki ki yi hakuri kinji share hawayen ki karma ki Jawa kan ki . ciwon kai� ' Ya samu ya lallasheta ta yi shiru sannan ya tafi zuciyarsa na faman saqe-sake � Washe gari da sanyin saflya Malam Bala ya shirya ya nufi gidan Alhaji Bashir saboda yanda Laure ke ta faman ingiza shi. A kofar gidansa ya same shi zaune saman mota da News paper a hannunsa yana dubawa. Malam ya yi masa sallama, Alhaji Bashir ya dago tare da amsa masa cikin sakin fuska ya miqa . masa hannu su kai musabaha. Malam Bala ya ce ‘Dama Alhaji wajen ka nazo.� Alhaji Bashir ya ce, ‘To mu shiga daga ciki k0?� “A’a daga nan ma ya isa, Kara na kawo maka.� Alhaji Bashir ya ce, ‘Kara kuma tawa?� Ya ce ‘Danka Hamid na kawo maka qararsa ka ja masa kunne dan kuwa ya shiga har cikin gidana zai keta mini haddin� ya shi yasa na zo wurinka na kawo maka kashedinsa, don kar naje in dauki mataki kaga anatare babu dadi,don haka nazowurinka kai masa kashedi da iyalina.� Alhaji Bashir da ya nutsu yana kallonsa mamaki ya dabaibayeshi muryar shi a sanyaye ya ce, “Lallai ka haifi yaro ba ka haifl halinsa ba, don Allah ka yi haquri Malam in dai nina haifi Hamid ya gama bi k0 ta gefen gidanka kayi haKuri don Allah, don Annabi.� Malam ya ce, “To ni dai kashedi na kawo maka ka ja masa kunne.� Alhaji Bashir ya ce, ‘Insha Allahu.� Sannan ya juya ya Lafi buzun-buzun. Alhaji Bashir ya sauke wani gwauron numfashi, sannan ya yunqura ya nufl cikin gidan zuciyarsa a cunkushe ya shiga falon gidan, babu kowa a falon sai Hajiya Hanifa tana tsaye tana goge-gogenta a