← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 90

Sashe 11

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

*CHAPTER 10*

Dan iska wulakantacce Allah ya tsine maka Rabi’u ban ga
amfanin rayuwar ka ba.
Yanzu uwar taka ce za ta mare ka har ka daga hannu za ka
rama, don kana marar kunya lalatacce. To bari in tsine
maka ka je can ka Karasa lalacewar ka tunda kai din ba dan
mutunci ba ne, yaro jinin sunna ya yi haka alhalin kana dan
iska kishiyar uwa ba uwarka ba ce, k0 k0 hudubar da uwar
taka ta tafi ta bar maka kenan? In ban da na shigo da yanzu
marinta zakai da gaske, « don kana marar kunya.�
Laure ta sa kukan munafurci tana fadin, “Kuma Malam wai
kan abin da bai taka kara ya karya ba yaron nan ya dinga
marina har yana fadar shi zai zamo ajalina wai dan kawai
na ce bai kamata ya sanya Saude makaranta ba da kan shi
ya bari har ka zo ya yi maka magana. Shi kenan yaron nan
ya shiga zagina ta uwa ta uba wai har: yana fadar shi zai
zamo ajalina....�
Ta Kara fashewa da kuka, ‘Wallahi Malam bazan iya zama
ba, yaron nan ya kashe ni a banza a woli ba, wallahi tafiya
ta zan yi in bar masa gidansu tunda yana da gaskiya gidan
ubansa ne
Malam ya ce ‘Da alla bar' wannan magamar
Laure kar ma ki ja yaron nan ya Kara raina ki gidan ubansa
da wa ya fada masa, ina uban nasu yake nan
yaranda akaimin wuru-aka manna min tsiya~
Ya juya yana kallon Saude da Rabi’u yana fadar, “Baku
sanibane koba a taba fadi maku bane kama uwarku da
kwarto Kiri-kiri akayi iyayenta suka koreta dalili kenan
tabarku tatafi yawon karuwanci yace wlh kukaci gaba da
takuramin ko matata a shirye nake dana koreku daga
gidannan
Rabi� u ya riqo hannun Saude suka nufi dakinsu suna: shiga
ya jingina kansa da bangon daki yana wani irin kuka maicin
zuciya.
Itakanta Sauden kukan take yanzutafara fahimtar suwayesu
dakuma matsayinsu acikin gidan duk da qarancin
shekarunta hakan bai hana ta fahimci dalilin tsanar da ake
masu ba tasa hannunta ta riko hannun Rabi� u tana fadar
“Wai Yaya da gaske ne abin da aka fada? Yaya
da gaske mahaifiyarmu karuwa ce mu ma bamu da iyaye?�
Rabiu: ya waigo yana kallonta hawaye sun gama bata masa
fuska ya Kara riko hannunta yana girgiza
Ya girgiza mata kai cikin muryar kuka ya ce, “Karki soma
wannan tunanin Saude nasan kowacece mahaifiyarmu don
ni na rayu da ita :nasan kowace ce ita, ita din mutuniyar
kirki ce knma ‘yar manyan mutane.
Saude ta ce, “Yaya idan har mahaiflyarmu mutuniyar kirki
ce to me yasa ta watsar da mu ‘yan uwanta suka guje mu
ta bar mu mu kadai mina rayuwa cikin qunci da wahalar
rayuwa?�
Rabi’n ya ce, “Saude mahaiflyarmu na son mu kamar yanda
kowace uwa ke san danta, dole ce ta dolece ta rabata damu
badan tasoba kiyi mata uzuri Saude duk qunci da wahalar
da ki ke ciki bai kai wanda ita . ta shiga ba.� .
Saude ta ce, “To,amma �
Ya daga mata hannu da sauri alamar ba ya san jin abin da
zata fada, sannan ya juya ya fice ya bar mata dakin Wani
kuka ya qara zuwar mata ta kwanta ta ci gaba kukan
abinta. tanajin zuciyarta. na suyakamar garwashi,yamaza
ai Rabi’u yace mata qarya ne abin da su Baba da Laure
suka fada a , kan mahaifiyarsu alhalin almomi sun nuna
gaskiyar
Shin idan har mahaifiyarsu tana son su me yasa � ta tafi ta
barsu babu k0 waiwaye? Shin idan mahaifiyarsu mutuniyar
kirki ce me yasa ‘yan uwanta suka kore ta? Shin idan har ta
tsare kanta me
Zaisa mahaifinsu ya zargeta harya kyamacesu da zama
yayansa?
Tambayoyin data jeroma kanta kenàn
Wanda bata da mai amsa mata su
1 page is missing am sorry
ya farkar da ita, don haka ta dauki kayan ta koma gida babu
cinikin ko sisi.
K0 da ta maida alalen Laure ta yi ta masifa, tun fadar, “Na
lura mugunta ce kawai yau ki ka sa mini
kuma ‘yar iska ke zata karewa a je min kayana ki.� wuce
Saude ta samu ta ajiye kayan ta yi daki da hanzarinta, don
dama barci ne fal a cikin idonta ta samu ta kada kafadunta
ta kwanta, wani bacci mai nauyi k0 ya yi awon gaba da ita.
Inna Laure ba ta ba su alalan ba sai da gari ya ' waye a
lokacin ta lalace sannan ta miqo masu ita waisu karya da
ita. Rabi‘u ya kai ya zubar ya ciro kudi ya siyo masu koko da
qosai suka karya, sannan ya tafi wurin aikinsa, Saude kuma
ta tafi talla.
Da yamma likis Saude ta dawo daga talla, Laure ta ba ta
dakan kunnun jego wanda ta karBo a makotansu da akai
haihuwa, kawai saboda neman suna, shishshigi cusa kai ba
kwarjini. Saude na cikin dakan ta debi gyalenta ta fice ita da
‘yarta.
Suna fita Saude ta ajiye dakan ta kwanta bakin turmin tana
hutawa a lokacin Rabi’u ya dawo daga � wurin aikinsa shi
ma ya kwaso gajiyarsa ya zauna kusa da ita cikeda
tausayawa ya ce, “Sannu ya jikin na ki ne?"
Saudc ta ce, “Da sauqi sai dai ciwon kirjin da ya matsa mini
yanzu."
Rabi‘u ya ce, “Allah ya sauwaqe karbi wannan bari inje
chemist na siya miki magani." . Saude tayi saurin sa hannu
ta karBa tana: dubawa leda ce baqa guda sai farar leda
guda. Ta bude: soyayyar doya ce da kwai a ciki, dadi ya
kama ta yauzu: itce zata ci doya da kwai. wanda tunda take
a duniya bata taba cinta ba. Ta yi saurin kallonsa da Washe
fuskarta tana fadar.
“Wayya Allah na Yaya, yau zan ci doya, tunda nake fa ban
taBa cin taba wallahi.�
Rabi‘u ya yi murmushi yana kallon ta, sai da ya tashi zaibar
wurin sannan ta bude baqar ledar. Ta yi wani tsalle
ta tashi tana fadar.
“Wayyo dadi, Yaya kayan kwalliyana ne?" Ya daga mata
gira, ta buga wani uban tsalle ta dafa shi taba fadar.
“Wayyo Yayana na gode kwarai wallahi dama ina so nima in
rinka lrin kwalliyar su ‘Yar Baba, inyi; kyau k0 Yaya?�
Ya daga mata kai alamar eh, tasa dariya ta ciro madubi tana
kallon kanta tana ta faman gwalegwalen idanuwa.
“Kai Yaya wai dama haka nake, Yaya kalli idanuwana ‘yan
qanana-qanana, yanzu kuma Yaya wannan bakin nawa har
cokali yana iya shiga ciki?" Ya buga hannun shi saman tafin
hannun shi alamar oho tayi daria
Tace yaya ji haqorina har yayi tsaho da yawa'
Rabl'u ya kwace madubin yana fadar, “Ke tashi kiyi aikinki
saude ta shagwabe masa “kai Yaya don Allah ka bari in gani
wallahi ban gama ganiba
Rabiu ya saka madubin cikin ledar yana fadar, “Idan kin
shigo dakin kin gani ai naki ne bana: wani ba, kin ta gani
harki gaji. Dauki doyarki ki ci kinji
Ta ture doyar can tace tana turje-turjen qafafuwa, Rabi’u ya
dauki doyar yana fadar, “bazakici ciba ke nan to bari in
cinye abuna dama ba qoshi na yi ba rago miki.� nayi
Saude ta yi saurin riqo rigar shi tana fadar. ‘Yi haquri' don
Allah ka ba ni :na daina.�
Rabi’u ya sakar mata ya wuce yana dariya, ta zauna tana ci
tana lumshe ido har ta gama, sannan ta mike ta ci gaba da
dakan yajinta iya qarfinta. Ta samu ta gama, sannan ta
wucc daki ta janyo kayan kwalliyan tana duddubawa, ta
zauna ta manne fuskarta radau da kwalliya abin kada sabon
shiga, duk ta yi wa fuskarta dame-dame man da kwalli
Washe gari ma tana gama sallar Asuba ta janyo kayan
kwalliyar ta hau ranbadawa a fuska, shi dai Rabi’u yana
zaune yana kallon ikon Allah. Tana gamawa ta mike ta nufo
shi tana fadar.
“Yaya duba ka gani wai nayi kyau?�
Rabi‘u ya yi wani takaitaccen murmushi kafin yace.
“Sosaima, don sai yanxu na Kara tabbatar da kamar ki da
Mamar mu daya, sak kamar an tsaga kara wallahi.� '
Saude ta gyara zama tana fadar, ‘Wai Yaya don Allah ya
Mamarmu take, baqa ce k0 fara k0 doguwa k0 gajeriya?"
Rabi‘u ya yi murmushi kafin ya ce “Mamanmu fara CE fat
don har ta fiki . kuma doguwa ce mai
Dan jiki kadan, yadda. Kika ganki haka take.�
Ta ce “To yaya tana son mu?"
Rabi‘u yace, “Sosai ma kuwa don ranar da zata
rabu damu tasha kuka fitar hankali keko saida a kai da
gaske sannan aka Banbare ki daga jikinta kina ta tsalla ihu
a lokacm kina da shekara shida a duniya.� Saude ta yi wani
murmushi kafin ta ce “To Yaya yanzu tana ina?� . Ya girgiza
mata kai yam: fadar, “Allahu a‘alamu." Ta dan yi jim kafin
ta ce “To Yata tafitabar mu?� me akai mata? Kafin ya kai ga
ba ta amsa Inna Laure ta hankado
labule tana fadar, “To tif da taya � talla sai a tashi a tafi
tallah hakanan
Saude ta mike cike da alamun gajiyawa a
fuskarta ta fice ba dan ta so ba. Ta tafi tallar da ta zame
mata waki’a farilla.
Da daddare ciwon mara hade da ciwon ciki mai tsanani ya
rufe Saude tamkar ba za ta kai ba, ta ringa murkususu a
tsakar daki ita daya a lokacin Rabi’u
bai dawo ba.
Laure na jin ta, amma k0 ta kula ta kanta. Haka Rabi’u ya
dawo ya same ta hankalin shi ya yi masifar tashi, ya juya ya
koma ya siyo mata magani ya ba ta, amma a banza,
sumanta biyu cikin dare. Yanda suka ga rana haka suka ga
dare daga ita sai Rabi’u cikin daki babu wanda ya leqo balle
ya ji halin da take ciki, don Malam ma bai san abin da suke
ciki ba.
Cikin ikon Allah ana kiran sallar Asuba, jini ya zowa Saude,
a take kuma ciwon marar ya dauke, don haka ko motsi ba ta
iya yi ba daga inda take ta kwanta sai bacci mai nauyi ya
dauke ta.
Sai a lokacin Rabi’u ya samu kwanciyar hankali ya tisa ta a
gaba ya rabka uban tagumi yana kallonta hawaye masu zafi
suna biyo kuncinsa zuciyarsa ta cika da tausayinta, har gari
ya fara haske sannan ya “farka ya mike ya je ya yi sallah ya
dawo ya samu ya dan kwanta saboda baccin dake cike cikin
ldanuwansa.
Cikin barcinsa ya ji tamkar ana rabka sallallami, Rabi u ya
bude idanuwansa da su kai masa wani irin nauyi saboda
bacci, ya ga Inna Laure na fadar
“Malam! Malamll zo ka ganewa idon ka ikon Allah Malam zo
ka gani.�
Malam Bala ya fito daga dakinsa yana fadar, “Ni
ko kinsan bansan irin wannan kiran natashin ”hankali.�
Laure ta qara hankade labulen dakin sosai tana fadar, “Ai
wannan idan ma akwai abin da yafi tashin hankali to shi ne
dubi yarinyar nan Saude kalli siket dinta.�
Malam ya qara tura kai cikin dakin tsawon wasu ‘yan
sakanni kafin ya ce ‘Kamar jini nake gani Laure?�
Laure ta turo wuya gaba tana fadar, “To duba da kyau jini
ne daman tun jiya nake jin ihun yarinyar nan na dauka wani
iya shege ne ashe yaron nan ne ya haike mata.�
Gaban Malam ya yi wata mummunar faduwa ya juya yana
kallonta a razane bakinsa na fadar, “Ki bari don girman
Allah.�
Laure tabe baki tana fadar, “Ga alama nan.�
Idanuwan Rabi’u suka yo waje don sai a lokacin
ya lura da yanda jini ya Bata siket din Saude sosai kamar
anyi Barin manja a jikinta abin kaga kaya
masu haske da santsi, hankalin shi ya yi masifar
dugunzuma.
Malam ya ce “Lallai kam yaran nan ka cika la’anannen Allah
yau kam sai na gwada maka irin nawa rashin imanin ni za
ka jawa abun kunya, ka yiwa qanwarka fyadeee dan iskan to
wlh daga rana irin tayau ka gama haikewa ‘ya’yan jama’a.�
Ya juya a zafafe sai ga shi ya janyo wani qaton faskare,
Laure ta riqe tana
fadar. A,a don Allh kayi haquri Malam karka kashe shi.�
Malam ya goce yana fadar, ‘Wallahi yau sai dai akwashi
gawarsa cikin gidannan inya so nima a kashi yayi kukan
kura gamida yin kansa da faskaren
Wooooohoho jama,a wai ya abin yakene mu kubiyo ni donjin
yaddah wannan taqaddama zataci gaba da kayawaaaaaa
[1/17, 7:49 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/17, 7:54 AM] A A Dboy: *YAR TALLA*
Chapter 11 · 0% Book details