Sashe 20
Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a cunkushe take saboda duk abin da ake tana jin ‘Yar Baba ta tabe: baki ta wucc soron gidan, Saude ta tsaya da hura wutar tana kallonta idonta ya ciko da hawayce Hamid yana zaune a barin tabarma yana karkada kafafuwansa ya yi irin zaman nan na masu cin tuwo, ‘Yar Baba ta jingina da bangon soro ta kafe shi da ido cikin ido tana wani murmurtsa idanu. Hamid ya tsaya yana qare mata kallo cike da mamamki ya ce, “Ke kuma fa wace ce?� ‘Yar Baba ta‘yi wani qasaitaccen murmushi irin na gogaggun yan duniya kafin ta ce “Ai ni ce iKilima wadda aka fi kira da ‘Yar Baba, da alama baka gane ni ba ko?� Ta Kara jan wani munafukin murmushi tana fadar. “Kowa ma idan nasa kayan nan haka yake fade: beganeni:ba ashe dama haka nake da kyau hummml Kayan suna mini kyau sosai.� Wani takaici da haushi suka kama Hamid cikin takaici ya ce, “Ke da Allah saurara kin ji bana can shirme da sakarci kin, Saudat na ce a kira mini ita nake nema ba wai keba kin gane? � ‘Yar Baba ta ji tamkar ya watsa mata ruwan zafi a zuciya cikin Bacin rai ta ce, “Ai ba ita Baba ya ce kana nema ba ni ya ce kana nema Hamid ya dan sassauta murya, “Kin ga kiyi hakuri don Allah ki je ki kira mini ita ta sanda zuwana please ban san ku biyu bane a gidan." ‘Yar Baba ta waro ido tana kallon shi bakinta na fadar, “Kutumar... wallahi ba zan je ba har ma ta isa in kula ta ‘yar tallan gidan namu ba zan jeba wallahi, sai dai ka daskare a nan.� Ta juya za ta tafi Hamid ya yi wani murmushin takaici ya zura hannu cikin aljihu ya ciro kudi� yan dan biyar biyar sababbi dal guda hudu ya miqa mata. ‘An shi ga wannan ladan kiran nata idan ba za ki kira ta don Allah ba. � ‘Yar Baba ta sa hannu ta fizge kudin tana fadar, “Ai raba mugu da makami ibada ne� Ta juya ta yi cikin gida. Laure ta tarye ta tana fadar, ‘Ya akai ne?" ‘Yat Baba ta fashe da kuka tana fadar, “Wai Laure wai ba ni yake so ba, wai SAUDE yakeso.� Laure ta ja wata ashariya ‘Kan habbm.... Bake yake soba uwar wa yake so?� � “Yar Baba ta nuna' mata kudin da ya 'ba ta, “Kin gama waiyabani inkiramasa ita Laure tace daukomin mayafina naje na sameshi ‘Yar Baba ta kwasa da gudunta ta dauko mata mayafinta ta baza saman kafada ta nufi soron kamar an hankada ta. Hamid yana zaune hmnunsa riqe da qatuwar wayarsa yana wasa da ita, yana ganinta ya fadada fuskarsa da fara’a. “Sannu da fitowa Umma barka da rana.� Inna Laure ta amsa fuskarta ba yabo ba fallasa sannan ta gyara tsayuwarta tana fadar, “Kai ne bakon Saude?� Ya dan sunkuyar da kai qasa alamun kunya kafin ya ce “Eh nine Umma.� Laure ta kuma gyara mayafinta mai kama da an kwato shi daga bakin kura ta ce “To Saude dai da ka ke ganinta shegiya ce ‘yar gaba da Fatiha, ce yarnan da ka gani kuwa ni ce mahaifiyarta nina haife ta da cikina, kuma ka san an cewa shi dan gado sai ya zarta to Saude kuwa har tace ban iya ba, dan wurin gantali da yawon bariki gari gari babu inda Saude bata zaga' ba. Kai in taqaice maka har cikin shege sai da ta yi.� Wani irin abu ya dakarwa Hamid zuciya mai zafin gaske ya samu da kyar Ya iya hadiye shi kafin ya iya fadar, “Amma Umma da mamaki a gaskiya ba zan Boye miki ba Saude ba ta yi wa rayuwarta adalci ba sululu kenan macijin sari ka noqe Ki yi hakuri Umma insha Allahu ba zan guje mataba don wannan qaddarar ta fada nayi miki aIqawarin auranta a hakan in ceto rayuwarta.� Laure ta ce, “A’a ahir!.Dinka karka fara don ba zaka taba iya ceto Saude ba saboda kin Allah irinna yarinyarnan ya wuce tunanin ka� Laure ta sa kukan munafurci har da su fyace majina. Hamid yana kallonta saidata gaji dankanta ta dan sassauta ta ci gaba da fadar, ‘Dan nan shu’umancin Saude yana ci min zuciya wai yarinyar hartasan tanemi mace ‘yar uwarta,bacin mazan datakebi yandakasan karyar mazahaka take. Na zubarwa Saude ciki yakai biyar a asibiti har sun haddace mu, sun gaji idan mukaje ma yanzu kararmu sukace zasuyi wai saboda zubdawa Saude cikin da muke yakai iyaka.� Hamid ya ce“Duk wannan ba matsala ba ce Umma, wallahi ahakan insha Allahu indai saude mai shiryuwa ce sai na shiryar da ita.� Inna Laure tace, “Kai malam,Saude bazata taba shiryuwa ba saboda ba ta tsoron Allah k0 kadan babu Allah a ranta.� Hamid ya ce “Ai Umma Islamiyya zan sanya ta insha Allahu kekanki saikinyi mamakin yanda zata shiryu ta nutsu.� Inna Laure tace“Dannan kenan bakasan Saude ba har yanzu, ai kwakwalwarta a dode take ba ta daukar komai ba ka da abin da Saude ke iya dauka ballentana harta iya haddace shi.� Ya ce, “Ai Umma babu abin da yafi qarfin addu’a, sai mu taya ta da addu’a insha Allahu za mu yi nasara amma ni ina son ta kuma wallahi aurenta zanyu Inna Laure ta harzuka cikin haushi ta ce “Tokai baza,a auramaka itadinba ‘yatadaicetonayi mata miji koka tashi kabarnan yanzunnan wallahi k0 in maka ihu kwarto, dan iska kai ana gwada maka Annabi kana rintse ido.� Hamid ya mike ya ajiye mata bandir din yan dari bibbiyu na dubu ashirin ya ce, “Zan tafi Umma ga wannan a sai sabulu zan dawo sati mai zuwa da fatan za ki sauko daga dokin qiyayyar da kika hau, na gode Ya juya ya fice daga soron ya bar Laure tsaye dakam tamkar wadda aka kafe sai zazzare na mujiya take a kan kudin, wani abu na yi mata zarya a zuciya ta duke ta suri kudin ta yi cikin gida tana kwalawa Saude .kira Sande da take duke gaban murhu ta yunkura da niyartatashi, amma ina dukanda Laure ta soma kai mata yasa ta duke babu shiri, Laure ta janyo bakin wuta tana faman dukanta sai ka cc yaqi fidi take. “Yau sai na kashe ki har lahira in ga ta soyayya, ke nan har kin isa wani ya ce yana son ki a hakan. To idan ma farar fatar ce ta janyo shi yau sai na lalata ta.� Tun Saude na ihu har ta soma Kokarin kwatar kanta, ‘Yar Baba ta tare ta tana fadar, ‘Laure fuskar za ki toya ki lalata mata ita mu ga ta kyau da iyayi.� Saude .ta sa wata irin kururuwa, ta kwace daga hannun ‘Yar Baba ta yi dakinta ta maida qofa ta rufe, tana jin Laure na fadar k0 ta bude ko ta cin nawa dakin wuta amma ba ta motsa ba. Kuka take sosai kamar ranta zai flta, dan Laure duk ta tattaya mata jiki da bakin wuta abin ka ga jar fata duk jikinta ya yi jawur. Ai kuwa nan ta sulale Kasa ta zauna tana faman kukanta. Tabbas ya zame mata wajibi ta cirewa zuciyana kwadayin wata rayuwa mai dadi, dan ta tabbatarwa kanta Inna Laure ba za ta taBa barinta ba, tasa hannu tana sharar kwalla. Inna Laure ta sake bubbuga qofar tana fadar, “Sai ki flto ki daukar mini talla ta in ba haka ba in karya kyauran in shigo.� Yadda ta ke dukan kyauren da Karfinta ya tabbatarwa Saude za ta iya ma abin da ya fi hakan, ta ta miKe tana kallon kayan jikinta, tun leshin da ta saka ne ta je gidan Garba Gurgu ne a jikinta, har yanzu ga shi Laure duk ta qona shi. Ta dauki hijabinta ta sanya ta bude kofar ta fito, Laure ta kai mata wani duka tana fadar. “’Yar iska munafuka!� Ta watsa mata kayan hannunta, ‘Karbi maza ki canza kayan jikin ki duk wani abu da ki ka san na kwalliya ne a cikin dakin nan ki ki miqo mini shi yau sai na ga qaryar soyayya ai dai sai da kyan aka soyayyar ko to zan gani.� Saude ta amsa ta koma dakin, wata kodaddiyar atamfa ce riga da zani ba dankwali, rigar sai a hada irinta mutum hudu su shiga ciki ga ta duk ta yage saboda tsufa. Sai zanin Jaka tsaye ya yi matukar shan jiki ya sha gamun baki har wuri hudu, ga shi babu dankwali 'sai wata abaya, hawaye suka ciko a idanuwan ta tausayin kanta ya kamata ta cire kayan jikinta ta sanya wadanda ta ba tan, sannan ta tattara komai na cikin dakin ta fito da shi. Laure ta kwashe tana fadar “Munafukar banza, kuma wallahi ki sake in ji labarin kin tsaya kin saurari matsiyacin yaron nan na rantse da Allah sai na lahira ya fi ki jin dadi, ‘yar iska tambadaddiya.� Ta sa qafa ta haure ta sannan ta wuce Saude ta dauki bokitin tallarta tasa kai ta fita, tana faman sharar kwalla. Rayuwa kenan ita dai ta san ba ta daga cikin wadanda sukai sa’ar rayuwa a duniya. Tana tafe tana sharar kwalla tana zancen zuci, ba ta ankara ba sai dai ta ga mutum a gabanta, wani irin kallo yake mata mai cike da mamaki muryarsa a sarkake ya ce Lafiya Saudat, wace irin shiga ce wannan laflyarki qalau kuwa?� ' Saude tasa hannunta guda tana goge hawayenta, ta soma magana cikin kuka. “Lafiyata lau don Allah ka yi hakuri ka flta daga rayuwata na roqeka.� Hamid ya girgiza kai yana fadar, “Impossible, wallahi abin da ba zai taBa yiwuwa ba kenan, sai dai idan har son ki zunubi neto na ratayawa kaina alhakinsa, amma ba zan taBa barin ki ba.� Saude ta tsaya da kukanta tana kallon shi kafin ta ce, ‘Me yasa ba xaka rabu da ni ba, k0 kana san jefa zuciyata ne cikin bala’in da ba zan iya flta ba? . Wannan kukan da ka ga ina yi duk ta dalilinka ne.� Hamid ya ce “Na ji na dauka, amma don. Allah ki yi hakuri ki bani kadan daga cikin labarin ki ni nayi miki alkawarin taimaka miki da duk wata gudun mawar da kike buqata."