← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 90

Sashe 60

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Taso mu je gida Saudat ki huta in ba ki tarihin mahaifinkuda irin taskun da na shiga a lokacin aurena da shi". Ta riqo Saudat ta taimaka mata ta mike, ta dauki makullin motarta suka fito har zuwa harabar asibitin inda aka tanada don ajiye motoci. Ta bude wa Saude gidan baya ta shiga ta maida ta rufo sannan ita kuma ta zagaya ta shiga mazaunin direba ta yi wa sabuwar motar key qirar Jeep mai taya a baya suka hau hanya kai tsaye Goruba road suka nufa a road ta tsaya qofar gate din wani madaidaicin gida mai kyan gaske da wadatar furanni masu tsayi ta yi' oda kusan sau biyar sannan aka bude gate din gidan ta cinna hancin motar a ciki maigadi yana daga mata hannu ta yi cikin gidan kai tsaye harabar wurin ajiye motoci ta nufa ta raba motar tata kusa da wata Matris sabuwa dal ta kashemotar ta fito sannan ta bude wa Sande ita ma ta fito ta riko hannunta ta ratayo a wuyanta saboda taji dadin taka qafar sannan suka shiga falon inda qofa ta ke a gefe suka nufi falon kai tsaye Bai da girma sosai, madaidaici ne wanda ya cinye saitin knjeru guda da show glass tare da kayan kallo da santa table a tsakiya. Suna shiga falon qananan yaran da ke zaune suna wasa suka yo kansu suna, “Oyoyo ga Momy�. Saude ta bi yaran da kallo, ‘yan qanana \ masu Dr. Mariya ta yi wa Saude masauki saman kujera sannan ta bi ta kan yaran ta rungume su a jikinta tana amsa sanu da zuwan nasu, ta nuna masu Saude, “Bakuga Antynku bane? Kuje ku gaishe ta�. Yaran gnda biyu mace da namiji suka durkusa gaban Saude suna fadar, “Ina kwana Aunty�. � Saude cikin karayar zuciya ta amsa da lafiya lau tana kallonsu, macer ce ‘yar babbar wadda ba za ta wuce shekaru shidda ba, sai namijin wanda bai wuce uku ba, Dr. Mariya ta ce, “Kannanki ne, Nabil da Nabila suna karatu ne a nan Saude su duka da maigidana Alhaji Ashiru yana aiki a central bank yanzu kizo muje ga dakin baqi can ki wanka kici abinci ki huta, sannan inzo muyi magana". , Saudat ta amsa da, “To�. Sannan ta mike suka nufi dakin. . Karamin daki ne mai dauke da gado da kujeru Kwara uku sai kayan kallo. Falon ya yi kyau sosai saboda yadda aka qawata shi da kayan dakwareshin masu kyau, akwai toilet da dan wurin hutawa a cikin falon. Dr. Mariya ta juya ta fito ta bar Saude taqarewa falon kallo ganin abin ta ke take tamkar a mafarki wai ita ce yau da mahaifiyarta, ikon Allah ko’ina Yaya Rabi’u ta san da zai samu labari ba qaramin murna da farin ciki zai yi ba. Dr. Mariya ta sake shigowa rungume da sabuwar jallabiya a hannunta ta ajiyewa Saudat tana fadar, “Ki je ki watso ruwan ga jallabiya nan ki saka nasan za ta yi miki a Saudiyya na siyo ta�. Saude ta amsa da,� “To na gode�. Dr. Mariya ta yimurmushi kafin tace, “Me ye abin godiya kuma Saudat? Don Allah ki saki ranki ki rinqa kallona a matsayin mahaifiyarki kin ji?� Murmushi kawai Saude ta yi tare da ‘sauke idanuwanta qasa Dr. Mariya ta juya ta fita sannan ita ma Saude ta yunkura da kyar ta mike tana tsangala kafar da kyar ta shiga bandaki ta watso ruwa ta dauro alwala ta fito ta murza mai a jikinta sannan ta kawo jallabiyar baka ta saka ta nade kallabin rigar a kanta sannan ta yi sallarta ta daga hannuwanta ta soma tana godiya ga Allah da Ya muna mata wannan ranar, Dr. Mariya ta shigo ta kawo mata abinci ta juya ta fita, Saude ta shafa addu ar ta mike ta nufi inda kulolin abincin suke ta bubbude, tuwon shinkafa ne da miyar alayyahu ta ji naman kasuwa sai gasasshen kifi da kayan lambu wanda ya ji curry da kayan kamshi, sannan kunun aya cikin jug wanda ya ji kwakwa da dabino da madarar gari. Saude ta zauna kasa tana tsatstsakurar abincin ba wani da yawa ta ci ba ta ajiye ta sha kunun aya sosai, sannan ta dauki magungunan da ta ga an ajiye mata ta sha, ta mike ta‘nufi kan gadon ta kwanta. Wani bacci mai nauyi ya dauke ta ba ita ta farka ba sai gab da maguriba ta mike ta nufi bandaki ta dauro alwala ta fito ta yi sallah,� tana nan zaune Dr. Mariya � ta shigo da sallamarta, tana sanye da wasu riga da siket na wata atamfa super wax mai kyan gaske Ta raBa saman gadon ta zauna tana jiran Saude ta kammala Saude ta shafa addu’ar ta waiwayo tana gaishe da Doctor. Cikin fara’a ta amsa tare da fadar, “Sannunki da qoqari, ai na dauka kina nan kina bacci, kin san marar lafiya bai san motsa jikinsa saukinki ma ba ki da Kan-jiki�. � Saude ta dan yi murmushi tana kallon inda a ka yi mata dressing din ciwonta". Dr. Mariya ta ce, “Da ma ina so mu yi° magana ne shi ya sa na bari ki huha ki dan samu natsuwa Saudat zan ba ki tarihina gabadaya ta yadda zaki cire qullatata a zuciyarki, da farko 'dai ni . ‘yar asalin Dandagoro ce mahaifina da mahaifiyata a can suka haifeni ni da yayana, kuma a ciki muka girma sana’ar mahaifinmu ita ce Kira, ana ce masa Lawai maqeri mahaifiyata kuma sunanta Badiyya, ita kuma tana sana’ar kitso da saka, asalin mahaifiyata bafulatana ce kuma gabadaya ita muka biyo. Tunda na tashi ina qarama ta na iya saKa " harna fara girma mahaifina ya sani a makarantar boko a lokacin ina. da wana Yaya Sani sai ni sai turamu Yayana ya yi karamin bokonsa� daganan ya tafi Sakandiri har zuwa Polytechnic inda ya yi N C. E dinsa, amma bai samu aiki ba a lokacin duk da unguwarmu yaya Sani ne kawai wayayye , don shi me ya fara wucewa. gaba da sakandire. Ina firamare aji bakwai, lokacin har aji . bakwai ake yi, watarana na hadu da mahaifinki Bala, a lokacin ina da shekaru sha uku, shi kuma a � lokacin yana, saurayi don� bai wuce shekaru asirin ba, na hadu da Bala yazo Yaya . Sani' ya yi masa wani lissafin kudi ya buga masa da calculator. Suna zaune saman dakalin. Qofar gida suna magana, ni kuma na dawo daga makarantar allo da yamma na gifta su na gaishe su zan wuce Yaya Sani ya kira ni na dawo na durkusa a gabansu�, “Ga ni� , Ya ce, “Je ki kawo mana ruwan alwala�, � � na amsa da, “To� sannan na tafi cikin gidan na ajiye allona na samu Umma a zaune akan tabarmar kaba tana yi wa wata mata kitso � ' na gaishe da matar sannan na wuce bakin randa na zuba� musu ruwan a butoci na fito na kai musu, na dawo gida na ci gaba da ‘sanwar tuwon da Umma� ta. dora,‘ban san wainar da aka toya ba a waje tsakanin Yaya Sani da Bala ba kwatsam washegari Umma ta aike ni kai kudin daShi nan bayan gidanmu, na shiga gidan kafin in fito yaro ya shigo wai ana kiran � Mariya. Gabana ya fadi, don nadai san ko sauraren Samari ban fara ba,kamar' kar na fita matar gidan tacemin,“kije kiga ko waye ki ka sani k0 yayanki ne?� Jin hakan da ta fada ya sa na samu kwarin gwiwar fita, a rakube na same shi jikin bango ya harde hannuwansa a Kirji yana ta faman mazurai. Ganin Bala mamaki ya kama ni, ni dai na san ba haduwa muké ba, duk da. kuwa yana dan unguWannu don bama ruwana da shiga shirgin maza. � Na dan tsaya nesa da shi na gaisheshi, ya washe baki yana amsawa kamar wanda aka , yi wa wata kyauta, nace, “Ga ni� Kallona ya yi sosai kafin ya ce, "Nasan zakiyi mamakin kiran danayi miki ko?� � Ni dai kaina na kasa, Jira kawai naké in ji yace, ga inda zai aike ni Shikuma batare da ya tsaya sauraran amsata ba ya ci gaba da cewa � . “Ba komai bane ya 'sa na kira k8ba , ,Mariya wallahi Sai don na bude miki abin da ke cikin zuciya saboda na ga barinsa a qirjina bai ,da wani amfani Ni dai Mariya ina dawainiya da sonki a zuciyata ba wai yanzu ba ‘wallahi tunda dadewa amma Allah bai Sa na taBa fada ‘wa kowa ba sai jiya na sanar da‘yayanki Sani, amma sai ya nuna mini gaskiya in yi haquri don kuwa ke karatu za ki har gaba da sakandiri za ki wuce, don burinsu sai kin zama likita, ba yadda ban yi da shi ba amna ya Ki daga qarshe ma har dan saBani muka samu da shi a kanki. Na haqura na tafi gida, amma wallahi Mariya ban iya samun bacci ba a daren jiya, , idan na rufe idanuna hotonki nake gani yana yi min gizo, duk yadda naso in rarrashi zuciyata abin ya faskara, don haka na yanke shawarar~ � zuwa wurinki da qoqon barana don Allah Mariya ki taimaka ki soni koda da kwayar zarra ne� Ni a lokacin sai na rinka jinSa tamkar ; : mafarki don tunda nake babu saurayin da ya taba tara ta da irin wannan maganar sai shi, don haka ban wani dauki abin da muhimmanci ba na dubeshi kafin in ce “Ka yi haquri, kamar yadda Yaya Sani ya fada maka ni ba aure zan yi ba, karatu zan yi, na gode, sai anjima�. Ina ji yana ta faman kirana, ama ban tsaya ba don ni a tsorona kada wani dan gidanmu ya wuce ya gan ni. Abu kamar wasa Karamar magana ta zama babba, don kuwa duk inda za ni sai na ga Bala, k0 makarantar boko' 'ko ta allo, k0 kasuwa za ni ke kamar ana fada masa ga ni nan zan fita, kuma in dai siyayya zan yi ko ta nawa ce shi zai biya kudin, duk wulakancin da zan masa ba ya ji, ya zame min kamar wani kaska na rasa yadda zan yi da shi, tun ina wulakanta shi, har ta
Chapter 60 · 0% Book details