← Book details Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 90

Sashe 29

Yar Tallah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saude ta ja ta tsaya tare da juyowa , muryarta na rawa ta sake yin wata sallamar, Ahmad ya bude idanuwansa wadanda suka kada sukai jawur, yana kallonta, kallon da ke tabbatar da tsananin tsananta cikin idanuwansa ya sake she idanuwansa kafin ya soma magana tamkar wanda yake sanyin rada. “Ba cewa nayi kar ki bari in sake hada hanya da ke ba? Okay ba kiji ba kenan, shi ne ki ka dawo k0?� Muryar Saude na rawar disko ta ce hajia ce tace min Ba ta qarasa fadar abin da za ta ce ba ya zabura a Qufule yana fadar, “Wuce ki bar falon nan,‘idan kuwa ki ka bari raina ya baci za ki hadu da abin da baki yi tunani ba. Gate out! � ‘Yan cikin Saude suka Kara Juyawa, wannan shi ne gaba kura baya hayaki, wasu irin hawaye suka biyo kuncinta ta durqusa a gabansa cikin kuka tana � fadar, “Don Allah don Annabi ka‘yi min rai ka yi haquri wallahi idan na koma na ce mata ka kore ni kasheni za ta yi don Allah ka yi hakuri � . Ahmad’ya tsaya yana kallonta tsawon lokaci yana jin tamkar ya shake ta saboda takaici, don a duniya idan akwai abin da ya tsana‘to bayan kuka Ne k0 cikin film baya Kaunar ya. ga ana kuka, ' Ya ja tsaki mts! Tare da fadar “Tashi na ji ya ishe ni haka.� Muryarta a raunane ta ce “Na gode. �* Bai tanka mata ba ya juya ya koma kan kujera ya yi kwanciyarsa abinsa tsawon Iokaci babu wanda ya Tanka can dai Saude da ta lura idan za su kwana a haka bai damu ba sai ta mike ta dan matsa kusa da shi kadan ta durkusa tana fadar, ‘Ko kwai abin da ka ke buqata in kawo maka?� Ahmad ya dan tsura mata ido= kadan, kamar wadda ta zage shi sannan ya juya tare da kada mata yatsun hannun shi ba tare da ya yi� magana ba, zuciyar Saude ta Kara tsurewa, don ta lura mutumin ya tsane ta da wuya idan kuma zai bata mazaunin mai aikin nasa. Kwalla ta cika mata idanuwa cikin muryar kuka ta soma magana, “Don Allah to in kawo maka wani abu mai sanyi.� " � “Na ce miki a� a, a’a shin wai k0 dole ne?� Yanda yake mata maganar ya firgita ta, saura kadan da ta fadi saboda razana. hawayen da suka taru a kwarin idanuwanta suka samu damar biyo kuncinta. ' Ahmad ya ja wani gajeran tsaki yana fadar, “Oh! My God, jeki kawo mini koma meye zaki kawo, k0 baki Jiba?� Ya fada a harzuke Saude ta mike a razane ta nufi gurin firij din ta , bude, lemuka ne kale-kale sun fi kada ashirin jikinta sai rawa yake ta rasa wane za ta dauko masa, can idonta ya sauka kan fresh milk ta kwali, tasa hannu ta dauko masa tare da kofi na tankaran guda mai gindin turmi ta rufe firij din ta nufo inda yake. Ta durkusa a gabansa tasa hannu ta gage hawayen da ke zuba a idanuwanta sannan ta balle murfin ta tsiyaya masa fiye da rabin kofi din, ta miqa masa, ba musu ya sa hannu ya karba Saude ta sauke wata nannauyan ajiyar zuciya, wadda ta janyo hankalinn Dr. Ahmad ya dan zuba mata idanuwansa kadan sannan ya dauke kansa. Ta yunkura ta mike tana fadar, ‘Sai da safe.� K0 uffan baice mata ba har ta fice Kai tsaye dakinta ta nufa ta kwanta zuciyarta ta lula duniyar tunanin abin da ya faru dazu ya rinqa dawo mata ita kanta ta ba kanta tausayi dan zama tare da miskilin mutum irin wannan ba Karamin aiki ba ne, shin k0 yaci abincin ma ko k0 haka nan ya kwanta? Allahu ‘A'a lamu. Ta daga kanta tana kallon agogon dake manne a bangon dakin karfe goma da� yan mintina, ta qara ' juyawa sosai a kan gadon, dan to san saura ‘yan mintina lokacin shan coffee dinsa ya yi, yanzu dan kawai zai sha wani coffee har sai wani ya je ya hado masa saboda san kai kawai irin na masu kudi 1page is missing Saude ta zabura ta durgusa tana gaida shi, k0 inda take bai kalla ba ballantana ta sa ran zai amsa, don haka taja bakinta ta tsuke tana kakllonsa ya isa gaban firiji ya bude ya dauko robar ruwa guda, ya murde murfin ya daga sama yana kwararawa cikinsa ya sha ya kusan rabi sannan ya ajiye ya waigo da niyar wucewa. Saude ta yi saurin sunkuyar da kanta ta ci gaba da abin da take, don tsoron kar ya � kama ta tana kallonsa. ' Bai kula ta kanta ba ya haye sama abinsa. Saude ta girgiza kai a zuciyarta tana mamakin miskilanci irin nasa, don har ma ya zarce matar tasa , ' tunda ita duk abin da kai za ta yi magana, amma shi sai dai ya kore ka. Ta girgiza kai ta ja gefen kafet ta zauna tana muzurai; , Da misalin Karfe goma saura minti biyar Ahmad ya sauko daga sama kamshin turarensa ya mamaye falon gaba daya, Saude ta dan dago a hankali ta saci kallonSa sanye yake da wani yadi mai laushin gaske sky blue, ya sha aiki da farin zare. Yadin mai Sharashara ne hakan ne yasa akan iya hango farar singlet dinsa da short nirker din da ke jikinsa, farar fatar . nan ta yi wani luwai-luwai kamar jikin Jariri. * * Ya ja ya zauna kan kujera da waya rike a 'kunnensa yana magana cikin harshen Turanci, Saude ta yunknra ta mike ta fita daga falon ta bi wata ‘yar kwana da ke gefe sai ga ta ta Bude qaton dakin dafa . abinci wanda ma‘aikata ke ciki, harsu uku duka mutum daya ne Bahaushiya a cikinsu. To su wai me yasa ba sa son daukar Musulmai zalla aiki ne? Ba ta da mai amsa mata wannan tambayan, don � haka ta karb0 break din yallaBai din sannan ta fito. A bakin kofa su kai karo da Aunty ta zo daukar wa Hajiya nata suka gaisa, sannan ta wuce, ta nufi falon nasa. : : Yana zaune kamar yanda ta bar shi har yanzu bai gama wayar ba, Saude ta dora tiren kayan abincin saman dinning table sannan ta koma can gefe nesa da shi ta zauna tana jiransa ya gama wayar amma da alama bai da niyar gamawa har wani kashe murya yake yana zuba shagwaBa, sai. kace wani qaramin yaro, duk kunya ta ishe ta, ji take tamkar ta zuba da gudu, don duk da ba ta. san abinda yake cewa ba, ' amma zuciyarta ta ba ta da matarsa yake wayar Ashe dama yana dariya irin haka? Lallai k0 da wa yake wayar nan, to an jiKa ta a shanye Ba ta ankara ba tana duniyar tunani sai dai ta ji muryarsa na fadar, “Kawo abincin nan Saude ta zabura har tana neman faduwa ta mike, ta nufi dining din ta dauko kayan karyawar tazo ta gabansa ya nuna mata kan kafet din ta aje masa anan sannan ta koma ta zauna Ya watsa mata wani kalla mai, kama da harara kafin ya ce, “Waye kika ajiye ya yi serving din. " Saude ta waro ido tana kallonsa cike da razana don ita dai ba ta san abin da yace ba, ya ja tsaki tare da fadar, “Na ce waye zai zuzzuba abincin?� . Saude ta yi saurin matsowa tana fadar, “Yanzu zan zuba.� Ta dauki kofi ta zuzzuba kayan tea, sannan ta zuba ruwan ta cika kofin d taf-taf ta juya da cokali ta mika masa. Ahmad ya zuba mata dara-daran idanuwansa cike da takaici ya ce, “Yanzu duk wannan Waye zai shanye shi? Kin tattakura kin shaqare kofl da ruwan tea dan rashin hankali mts!� Ya karBi shayin ya rage fiye da rabi a wani kofl din, sannan ya soma sha. Jikin Saude ya Kara yin sanyi, tana tsoron ta zuba masa abincin ya gwasale ta, muryarta a sanyaye ta� ce, “Abincin kamar yaya za a zuba?� Bai kalli inda take ba ma ballantana ta sa ran zai tanka mata, zuciyar ta ta Kara tsinkewa, ta yi ta maza ta dauki plate da cokali ta bubbude kulolin, soyayyar doya ce da miyar swse sai daya kular yam ball ne Wanda ya ji nama da kwai, sai dayar farfesun nama ,ne da dankalin turawa, wato~ papper chicking, sai gasashshen biredi an masa wani yanka mai kyau an dora saman plate, wato sandwich. Saude ta turo masa . plate din biredin, sannan ta zuba masa farfesun naman a plate din sai ta debi yam ball din ta zuba masa a gefen bredin, ta maida saman ta rufe. “Bai tanka mata ba ya rinqa cin abincinsa sannu a hankali har ya gama, sannan ya dago ya dube ta kamar wanda aka tilastawa sai ya kalle ta ya ce, “Tashi kawo mini morning fresh ‘Yan hanjin Saude suka duru ruwa, yau na shiga uku! Wani abu ne kuma haka? Yanda ya kafa mata idanuwa yasa a dole ta yunkura ta mike. To ina za ta dosa? � Ta tsaya cikin falon tana faman diminiya, tadan juyo kadan ta ga idan yana kallonta su kai ido hudu, gaba daya ya tattara nutsuwarsa a kanta, ai kuWa take ta Kara tsurewa to k0 dai tsintsiya yake nufi, don ta lura da ya yarda wani dan qashi a kasa. � Ta ja wata ajiyar zuciyar samun mafita, sannan ta dauko ‘yar tsintsiyar da take share-share da ita a falon ta nufo shi, ta durkusa tare da fadar, “Ga ta.� Haushi da takaici suka kashe Ahmad. ya watsa mata wani mugun kallo wanda yasa duk wata laka ta! jikinta ta mutu ya ja tsaki mts! Yana fadar. � “Ke jakar ina Ce? Wannan ita ce morning fresh din? Idan ba ki sani ba ba za ki tambaya ba, sai kawai ki je ki ta shashanci, ki kawo mini tsintsiya inyi tsiyar me da ita?� Ya girgiza kai cike da takaici yana fadar, “Kai Allah dai ya wadaran dakikin mutum stuppid girl ni Fice ki bani wuri, na daina hada ido da ke, sakarya kawai.� Zuciyar Saude ta Kara karyewa idanuwanta suka
Chapter 29 · 0% Book details