← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 111

Sashe 95

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

numfashi maryama ta sauke da qarfi cikin sanyi murya tace “na gode umma ahankali ta fita ta nufi bangaren mahaifiyarta tana kai wa bakin kofar ta tsaya cak ta kasa shiga tana tunanin abinda zata tarar daga masoyi ya, kuma abar qaunarta sai data sanyawa jikinta jarumta sannan ta shiga inda ta iske aunty zaune ta zuba tagumi daga ganin kasan tunani take wanda bata raba dayan biyu nata ne, ta qarasa ta durkusa gabanta ta dafa gwiwar qafafu wanta cikin tsananin sanyin murya tace “aunty kiyi hakuri ki yafe min bazan sake ba nayi nadamar abinda na aikata hakika baki cancanci haka daga gareni ba. sai lokacin aunty ta dawo daga duniyar tunanin data lula. ta tsura mata ido cikin zafin rai kwanaki uku kenan da faruwar abun amman ganinta yanzu sai take jin kamar yanzu abun ya faru “ki taimakeni aunty ki yafe min ki daina fushi dani bazan iya jurar fushinku ba “just shut up! ta fad’a tana janye qafafuwanta daga gareta batare da tace mata uffan ba “dan allah aunty wallahi bazan sake ba”maryama ki tashi ki fita ki bar nan bana son ganinki dan a yadda nake jin zuciyata zan iya aikata miki komai maryama tayi shiru tana duban mahaifiyarta fuskarta da bayananen mamaki “yau itace ta zama haka ga mahaifiya kuma abar sonta ?”mahaifiyar dake qaunarta fiyye da komai arayuwarta ,mahaifiyar data sadaukar da rayuwarta da farin cikinta dan kawai suzo duniya ita kuwa wace irin baqar rana ce yau agareta?” inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ta soma furta wa cikin tsananin tashin hankali yayinda gbdy ilahirin jikinta ya d’auki rawa kanta ta soma juya mata “nace ki tashi ki fita anan !aunty ta sake furtawa a matukar tsawace tana haki da sauri maryama ta mike jikinta na rawa tayi hanyar waje da sauri tana daf da fita suka ci karo da umma ta riko hannunta suka juyo zuwa ciki dan taji tsawar da aunty ta buga mata tsaye suka iske aunty tana zariya tana haki dafe da goshinta

Umma ta saki hannun maryama ta dafa kafad’an aunty tana cewa” taho nan bilkisu ki zauna ta janyota zuwa kan kujera inda aunty ta zauna tana goge hawaye da gefen rigarta” “kiyi hakuri bilkisu ki daina kukan nan haka .shiru kawai aunty tayi tana cigaba da goge hawayenta “bilkisu ki kalleni aunty ta d’ago idanunta da kyar ta tsura mata cikin tsannain damuwa “ki kwantar da hankalinki babu abinda ya faru da diyarmu maryama ki bar damuwa haka mutuncinta yana nan har yanzu ,abinda ya faru kuma tsaitsayi ne kuma zai iya faruwa da kowa bisa qaddara sam sam kada ki d’auka tana zubar da mutuncinta ne.”
“ ba wai ina tunanin haka bane umma amman ni uwa ce fa abun da ciwo ace maryamata ce na gani kwnace ajikin wani “ta fad’a tana goge hawayen numfashi umma ta sauke yayinda nan take kwalkwal warta ta shiga tariyo mata abinda ya faru a shekarun baya “nasan kema uwa ce a yanzu amman kiyi hakuri ki bar kukan hk sai dai a yau nake son kisan wani abu bilkisu ba wai zan dawo miki da abinda ya wuce bane a’a kawai dai ina son ki gane irin so da qaunar dake tsakanin uwa da d’a ne”Kinsan mai yasa zanyi mgnr tun kafin tayi mgnr kukan aunty ya qaru “bilkisu kina fushi da iyayenki especially mahaifiyarki akan rayuwarki ta baya to kisani taji zafi da radadi fiyye da wanda kike ji a yanzu .kisani ba kiyayya bace tasa mahaifiyarki ta dinga miki abinda ta miki abaya illa so ne da kuma gata da take son tayiwa rayuwarki amman soyayya da qaddara ya rufe miki ido ya hanaki fahimtarta abinda take gudar miki shi kika tsinta kanki ciki ,duk uwa ta gari baza só diyarta tayi rayuwa irin wanda kikayi da hussein ba wahala take gudamarki kuma kin shata har yau kina kan shanta , bazan tillastaki dole ki koma garesu ba amman kisani lokaci yayi da zaki je ga iyayenki ki nemi yafiyarsu da wannna kawai zan kawo qarshen maganata .”nasani umma nasan ban kyauta masu ba, ban kuma san cewar illa nayiwa raywuta ba sai a yanzu” umma ta numfasa sanna ta mikawa maryama dake rakube hannunta alamun tazo gareta “durkusa ki bawa mahaifiyarki hakuri “cike da sanyi jiki ta durkusa tana sheshekar kuka tare da riko hannun aunty cikin nata bilkisu ki yafewa diyarki ki kuma cigaba da yi mata addaua Allah ya shirya mana gabad’aya kasa cewa komai aunty tayi illa ta rike hannun maryama da cike nata sun dade suna kuka umma na rarrashinsu kafin daga bisani umma ta fito ta basu waje”

Kwanciya lamo maryama tayi a saman gwiwowin aunty yayinda ahankali aunty take jin zubar hawayenta ,ta yadda har ta fara jika zanenita duk da har lokacin aunty najin haushi da bakincikin abinda ya faru amman data tuna abinda tayiwa iyayenta sai taga kamar maryama rama masu tayi wani dogon numfashi tare da zubawa bayan maryama ido .”
”aunty kiyi hakuri bazan sake ba, ahankali aunty ta kai hannunta saman kanta tana sheshekan kuka wanda yasa maryama ta d’ago kanta “I’m very sorry aunty !tayi maganar adaidai lokacin da aunty ta mike tsaye cike da sanyin jiki ta juya tana tafiya tamkar wacce bata da laka ajikinta da sauri maryama ta biyo bayanta tana ta faman bata hakuri atare suka shiga dakin aunty inda aunty ta samu waje ta zauna tana sauke numfashi maryama ta qaraso ta zube gabanta cikin tsananin damuwa ki hukuntani aunty ko zuciyarki zatai sanyi domin kuwa na cancanci haka “ta fad’a tana riko hannunsa ta zuba mata ido kawai babu abinda take gani illa maryamar ta kwance ajikin wani kato hannuwansa zagaye da kugunta “dan Allah aunty kiyi hakuri ki daina kukan nan muddin ba so kike rayuwata tafi haka muzanta ba ,dan allah kice kin yafe min ko zuciyata zata samu sausauci “ta fad’a tana hade hannuwnta waje wani numfashi ta sauke sannan ta goge hawayenta “na yafe miki amman abinda nake so dake ki fidda miji aure maryama bazan iya zuyar ganin rayuwarki haka ba, ina miki addua Allah ya baki mijin na kwarai wanda zai duba lamarinki .”bakinta na rawa tace am ..”ameen “amman aunty bani da wanda yake sona da au..” ki nemoshi.” ta fad’a mata haka ta hanyar katseta yayinda fuskarta ke a hade tmkr wacce bata ta’ba dariya ba .”

tun tasowar maryama wannan shine karo na uku data ga damuwa mai tsanani atattare da mahaifiyarta “wata biyu kawai na baki maryama ki fidda mijin aure dan bazan juri ganin a ta’ba min ke ba …”ji maryama tayi gabanta yayi mummunar faduwa sakamakon jin abinda mahaifiyarta ta fad’a “dan Allah aunty ki taimakeni I promise you I will be..”banason jin komai daga bakinki mryama ni dai kinji abinda nake da bukata dake ,ki tabbatar kin fito da miji a wata biyu kuma bance kije ki fad’awa umma ba dan na canza maganata ba idan kikayi haka zanyi fushi mai tsanani dake ,ki tashi kije”. inna ilaihi !”ana wata ga wata dame zataji ina zata samo wanda zasuyi aure dashi nan da wata biyu tana kallon aunty ta mike tsaye ta canza waje ,tabita da wani kallo hawaye na kwarara akan kuncinta da kyar maryama ta yunkura ta mike tsaye haka ta fito daga bangaren aunty zuciyarta cike da mummunar tashin hankali daf da maryama zata fita sukai karo da habib wanda shigowarsa kenan ta tsura masa ido tana kallonsa hawaye nabin kuncinta wani irin tausayi da qaunar yaruwarsa ya mamayesa dan yaji duk matakin da aunty ta dauka akanta riko hannunta yayi cikin zafin nama suka dawo wajen aunty .”

“aunty …..”karka ce min komai habib domin maryama bata canci ta cigaba da zama damu haka ba data dinga janyo min magana gara tayi aure kowa ya huta daman yarda da kalar tarbiyar dana mata ne yasa taga na barta tana yin yadda taso bansan shashancin banza da wofi zata dinga yi a wajen aiki ba “nasani aunty hakika heartbeat bata kyauta miki ba ni kaina naji ciwo abun har cikin raina amman ya zamuyi dole hakuri zakiyi ?wani dogon numfashi aunty ta sauke kana ta cigaba da magana “maryama ta manta tsatsonta, ta manta halin da muke ciki acikin gidan nan ,ta manta irin rayuwar da muke ciki acikin gidan da abu kad’an ake jira akanmu ya zama abun mgn ta manta bata da galihu sai nã allah duk ilar da mutumin nan yyi miki yaci bulus tunda shi yana takama da kudi mufa ?bamu da kowa bamu da gata sai Allah shine gatanmu shi yasa wata biyu kawai na bata ta fito da miji tayi aure “.
“Naji tace babu komai tsakanin su amman sau tari idan ta dawo daga aiki ta shigo wajena Ina Jin qamshin turare ajikinta wanda ba nata ba kuma turare ne mai qarfi sai dai yarda da nayi mata yasa naji kunyar tmbyrta sai da wannan abu ya faru na fahimci daga wannan mutumin ne idan ma bai ta’ba yin komai daita ba zata iya rantsewa kafin wannan abun ya faru bai ta’ba sanyata ajikinsa da sunan runguma ba .”

Maryama ta sake rudewa ta gigice tana zazzare ido jikinta na wani irin rawa umma da habib suka zuba mata ido alamun tunhuma ita kuma Maryama alamun rashin gaskiya ya bayyana atare daita “kagani habib duk ta rude alamun rashin gaskiya nan take maryama tayi kasa da kanta tana zubar da kwalla numfashi habib ya saki yana cewa “duk abinda kika fad’a aunty da alamun gsky ne amman dai kiyi hakuri ki yafe mata ki barta har zuwa sanda allah zai kawo mata miji idan kika matsa mata taje ta shiga wata rayuwa fa sam sam zuciyata bazata lamunci haka ba dan haka ki janye maganarki akanta .
Chapter 95 · 0% Book details