← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 111

Sashe 76

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayinda zuciyarta ta dinga mamakin maganganun nadiya akan halittar data yi imani bazai ta'ba aikata hakan ba domin itama ta yarda dashi "maryama ki daina mamakin ,bazan ta'ba daina mamaki ba nadiya har sai naga sheida akan hakan yanzu ga wayarki a hannunki nayi imani idan har zaa samu hotunanku a wayarsa ko katin hotunanku to lallai zaa iya samu a wayarki tunda kuna tsananin son juna bai zama lallai ku iya rabuwa da hotunan juna ba "wannan haka ne maryama nadiya ta fad'a tana goge nata hawayen sannan tana qoqarin bude wayarta domin tabbatar mata da gaskiyar data bukata hotuna guda biyar ta nuna mata kuma duk suna tare da sadam babu kayan kirki ajikinsu cikin yanayi na tsananin soyayya "kadan ne wannan maryama ,kinga bazai yuwu na bar wayata a hannunki ba duk da nasan ganin wadan hotuna zasu miki wuya allah dai ya jikan sadam kawai ni zan wuce ta d'auki jakarta ta rataya ta fice daga office din ."

wani yanayi mai tsarkakkiya da wuyar misaltuwa maryamah ta tsinci kanta ciki rawar da jikinta yake yasa ta kasa tsayuwa sosai tasa duka hannuwanta ta dafe hannun kujera dan karta kai ga fad'uwa kasa da sauri mr ATA ya kamota ya zaunar daita akan kujera domin ya fahimci zata iya zubewa kasa, ya rike yatsun hannunta gam yana kallonta yana jin wani irin yanayi mara misaltuwa na shigarsa duk da yaso yayi ma nadiya nashi tambayar amman ganin tashin hankali da maryama ta shiga ya bar nashi amman lallai sai ya cigaba da bibiyi rayuwar nadiya domin akwai wata gaskiyar da yake tunanin ta boye wa maryama ".ahankali mrs ata ya sakar mata yatsun hannunta dake cikin nashi tare da mikewa tsaye yayinda maryama tai shiru dafe da kanta cikin tsananin tashin hankali mara misaltuwa."

"sosai tayi zurfi cikin tunanin rayuwa "a she haka yaya sadam yake cin amanar yardar da sukai masa ?"a she daman baya sonta ya amince da aurenta?"a she daman yana cin amanarta ne ?"hawaye ne kawai yake turereniyar zuba daga cikin kwarnin idanunta yayinda tsumammun kwayar idanun mr ata yake kanta yana kallonta tare da nazarinta kafin ahankali ya cire yar saman suit dinsa yana cigaba da kallonta tare da tura hannuwansa duka cikin aljihun wondon sa still idanunshi na kanta gabad'aya sai yaji damuwarta ta mamaye kowace gaba dake jikinsa."cikin takun nan nasa ya qarasa ya bud'e qaramin frdge ya d'auki goran ruwa ya rufe ya dawo inda take zaune tana kuka sai dai kukan nata ba mai sauti bane domin kuka take da zuciyarta ."

A natse ya bud'e murfin goran tare da mika mata "take some water "batare data kallesa ba haka zalika bata kar'ba goran ruwan ba tace "no ..!thank you." ta fad'a cikin wata irin sanyayyar murya mai tattare da tarin damu wa da tashin hankali "Ala hakikanin gaskiya ta dade bata shiga gigitaccen yanayi irin na wannan lokacin ba, ko zata kwatan tashi da wani abu sai dai ta kwatantashi da irin radadin da taji alokacin da taji tarihin rayuwar da iyayenta sukai kafin aure ,zuciyarta tayi matukar gigitata " iya tashin hankali ta shiga a zaunen da take "hakika yaya sadam ya cutar da umma ,sannan yaci amanar yardar da tai masa kuma yaci amanar tarbiyar datai masa da umma zata ga hotun sadam dinta cikin wannan yanayi da'aka kirasa da soyayya tabbas da take zuciyarta zata buga "why yaya sadam me yasa ka zabi irin wannan rayuwar ?"mai yasa kayi mana haka ?"duk wad'an story din da yarinyar nan ta bayar yanzu shi sadam din ya ta'ba fad'a miki ?."

yanayin da take ciki bazata iya bashi amsar tambayarsa zai fi ya barta taji da tashin hankali daya tsinci kanta ciki ,numfashi kawai take janyowa da kyar tana fitarwa "wannan shine matsalarki ana magana kiyiwa shiru ,okay but now this is your problem tunda kinsan komai akan mutumin da kika yarda dashi ,daman kuma matsalarku kenan mata kuna da saurin yarda da mutun kalli irin abinda ya saka miki dashi, yasan bai sonki mai yasa zai amshi aurenki har yayi nasarar dasa soyayyarsa acikin zuciyarki ?"is better to forget him in your life ki manta ko kuma nace ki goge wannan yarda da kika masa coz you trust him so many "

"bani kad'ai ba gabad'ayanmu ne ,mun yarda dashi mun aminta dashi shi din jigo ne acikin rayuwar ahlinmu kamar yadda mahaifinsa ya kasance alokacin da yake raye "sai dai mun yarda da yaya sadam dayawa batare da tunanin zai ta'ba mana haka ba ,we trusted him blind ,idan wani yace min yaya sadam zai aikata haka agare mu bazan ta'ba yarda ba duk da na ta'ba kamashi yana waya da mace amman siffa ta nagarta da kamala yaya sadam ya had'asu bazakace zai iya rungume wata mace da ba muharamrsa ba bare har ya kasance cikin irin wannan yanayin dana gansu tare da nadiya ba "I trusted yaya sadam without thinking ."ta qarasa maganar tana zubar da hawaye" I trusted him without thinking because I don't believe that yarda dashi din zai zame min qalubali arayuwata ."shiru ne ya ziyarci office din kafin ahankali ta cigaba da magana cikin muryar kuka "shikenan yanzu babu wanda zaka iya yarda dashi ?" ta fad'a wasu hawayen masu zafi da ciwo suka zubo mata "

Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan  littafin  na kudi ne mai bukatar karantashi   byn na kammalashi zai  biya 1000 ta wannan  account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura  domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina  (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 36

Daga inda mr ATA yake tsaye yayi shiru tare da zuba mata tsumammun idanunshi yana kallonta yana jin wani irin zallar 'bacin rai na ratsashi saka makon jin sautin kukanta da kuma ganin yadda hawaye ke turereniyar gangarowa bisa kuncinta."
sosai kukanta ke ratsa kunnuwansa da zuciyarsa dake bugawa da matsanamcin qarfin gaske ."nan take yaji zuciyarsa na qoqarin motsawa sai dai ganin yanayin halin da take ciki alokacin yasa ya dinga kwantar da zuciyarsa  yana qarfafata dan kar yayi misbehaved ."ahankali ya dinga danne matsa nancin kishin da yaji yana taso masa yana kai kawo acikin zuciyarsa dama gangar jikinsa ."naunauyen ajiyar zuciya ya sauke yana mai kwantar da murya cikin salo na kwantar da hankali ya soma magana a natse "maryama look at me!"ya fad'a kwayar idanunshi na kanta ,bata d'ago ta kallesa ba kamar yadda ya bukata sai dai hakan bai hanashi fad'ar abinda yayi niyya ba ,dan haka ya cigaba da magana "maryama dan ka yarda da mutun bai zama kuskure ba ko wani laifi ba ,kamar ka yarda da mutun as ending yaci amanar ka."ya qarasa maganar tare da yin shiru yana sauke numfashi yayinda ita kuwa sai faman sheshekan kuka take da sauke numfashi da qarfi tamkar wacce tayi gudun tsere tana sake jin mamakin irin rayuwar da yaya sadam dinta yayi da nadiya ,"

"yarda da mutun maryama ba kuskure bane amman dai yana da kyau kisan wani abu "shi wannan mutumin ya amince da aurenki ne alhalin zuciyarsa tana ga wata ."idan kuma har ya kasance yana sonki tô kisani da ya rayu zaki sha mugun wahala a hannunsa kasamcewar zuciyarsa tana tare da wata dabam, zuciyarsa tayi miki karya da yawa maryma sannan wannna mutumin baya miki soyayyar gaskiya ,domin kuwa duk abinda kake so tsakanin da Allah duk runtsi duk wuya kana qoqarin fad'a masa sirrin dake cikin zuciyarka ,ya so ya saka yaudara cikin lamarinsa koma nace ya saka yaudara.
A tashin farko da'aka bashi aurenki ya kamata ya fad'a cewar yana da wacce yayiwa alqawarin aure amman sai yaja bakinsa yayi shiru yaki fad'ar gsky kinga ko anan ma yaci amanar mutanen dayawa amanar nadiya amanarki da kuma amanar mahaifiyarsa ."abu na gaba da bai mutu ba da bazaki ta'ba sanin yaso nadiya ba kuma dole kuna tare zai koma gareta wala ya aureta wala kuma su cigaba da soyayyarsu ."mutumin nan ya cuceki dayawa dan ya dasa miki sonshi alhalin shi a zuciyarsa ba haka bane ,yayinda ke kuma kika d'aukesa a matsayin abun sonki da yardarki ,har kika d'aukesa matsayin masoyi kika yarda dashi kika mallaka masa ragamar rayuwarki you know this is your biggest mistake maryama domin kuwa kin so wanda bai dace da rayuwarki ba,haka zalika kin so mutumin da ba kece asalin true love dinsa ba, amman kika zauna kina yaudarar kanki kina cutar da kanki a banza har kika kasa cigaba da rayuwa mai dadi adalilinsa ."

tunda ya soma magana kukanta ya qaru hankalinta ya sake tashi zuciyarta ke qoqarin son amincewa da maganganunsa amman tayi saurin kawar da hakan dan amincewa da hakan ma ganganci né da butulci . "kuka take sosai har da sheshekan tamkar ranta zai fita "wayyo allah ni mryama !"wayyo allah rayuwata ni kuwa wace irin maseefa ce take yawo acikin rayuwata ?"kullum rayuwata cikin jarabawa da tashin hankali take, ahankali ya matso kusa daita tare da kiran sunanta cike da tausayawa ."
"maryama .!"
still dai bata d'ago ba "bazan hanaki kuka ba saboda ya cancaci kiyi kuka fiyye da wanda kikeyi a yanzu so continue crying okay "dan yana da kyau kiyi kukan yarda da amanar da kika bashi na tsawon lokaci so kiyi kuka iya kuka sannan ki dawo ki canza rayuwarki zuwa reality ."sai lokacin ta d'ago shayayyun idanunta da suke cike da ruwan hawaye ta tsura masa tana kallon yadda ya tsareta da nashi idanun yana kallonta cikin tsananin damuwa ahnkl ta motsa lip's dinta dake rawa rawa tace "na.."na kasa fahimtar komai sir bare na fahimci abinda kake nufi dani  a yanzu amman dai ina jin kamar yaya sadam dina yana raye kuma zai dawo gareni sai dai nasan bazai dawo ba ."ta qarasa maganar idanunta na zubar da ruwan hawaye masu rad'adi ".
Chapter 76 · 0% Book details