← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 111

Sashe 68

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba gali ya taresu cikin girmamawa yayinda mr ata sai sunkuyar da kai yake alamar nauyi da jin kunyar abinda ke tafe dashi bayan sun zauna baba gali ya mika masu hannu alamar su gaisa sai dai cike da girmamawa suka ki bashi hannu sai dai daga zaune da suke su ka d’an rusuna abinda ya kara daurewa baba gali kansa kenan “to me ya kawo haka manyan mutune haka masu daraja da arziki zasu rusuna masa lallai akwia babban alamarin daya kawo su .”Bayan sun dan zauna jimm, baba gali ya kalli oga amar yace “wallahi ranka ya dade tunda naji wayar ka na kasa samun natsuwa ina ta zullumi da fargabar ko lafiya?Oga amar ya danyi murmushi yace “lafiya qalau baba daman muna son rokon wata alfarma ce a wajenka “ Alfarma ? Wallahi kunfi karfin komai a gurina yallabai. A yanda nake jin labarinku a gari nan ban taba tabbatar wa ba sai da naga zahiri yadda kazo janaizar sadam ka bamu kudi masu tarin yawa sannna kullum cikinn taimakawa mutane dana kasa daku kukeyi jifa kwanakin baya akan maryama tayi aiki a qargashin yalla’bai kudi masu yawa aka bani a ina ake yin haka ai giramanku ya kai kusa ayi ko babu kosisi ku din na daban ne allah dai ya taimakeku .”baba komai baba mubar maganar nan haka abinda ya kawo mu muna neman Alfarmar auren maryama ne a wajenka “baba gali ya dago kanshi da sauri yana dubansu kafin muryarsa a dan rikice yace “maryama kuma ?”

Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

             Page 32

Ahankali oga amar ya gyad'a masa kai alamun "eh!shiru baba gali yayi zuciyarsa cike da matsanancin mamaki kafin ahankali ya motsa labbansa yace "kada dai in ce kai ne ke son auren maryama  ?"oga amar ya girgiza masa kai yana cewa "a'a bani bane  baba d'an uwana dake zaune agefena ke son maryama da aure kuma yake  son ta zamo uwar 'ya'ya nsa ya qarasa maganar yana nuna masa mr ata dake zaune a gefensa .wani irin tashin hankali baba gali yaji yana shigarsa,yayinda farinciki dake bayyane akan fuskarsa a mintuna data gabata yaji ya d'auke. nan take zuciyar baba gali ta shiga  tsinke wa,lokaci d'aya jikinsa ya kama rawa rawa ya mugun tsurawa mr ata dake zaune shiru idanunshi na kallon had'add'un takalman  dake sanye a qafafawunsa ido cike da tsananin mamaki "Allah mai iko yanzu maryama din ce zata auri mutun kamar wannan shahararren mutun da duniya tasanshi  tasan da zamansa ?" zuba ma mr ata idanu  kawai baba gali yayi yana kallonsa yana jin wani zallar 'bacin rai na ratsashi ,suna cikin tashin hankali shi da matarsa basu fita acikin ba sai ga wani sabon tashin hankali yasan muddin matarsa salma taji wannan labarin sai ta kusan hauka dan duk duniya babu abinda ta tsana kamar maryama da cigabanta .bataki kullum ta ganta cikin damuwa ba ,burinta  taga tozarta ta wulakanta ta rasa mai sonta."

oga amar ya gyara zamansa kana ya cigaba da magana a tsanake "alfarmar da muke nema a wajenka itace ka taimaka mana da aurenta acikin kankanin lokaci sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba muna bukatar aurenta ne batare  da saninta da sanin kowa ba saboda wasu dalilai namu  amman idan komai ya daidaita nan da wani lokaci kad'an zamu bayyyana mata komai "baba gali ya d'auke kwayar idanunshi daga kallon mr ata ya maida kan  oga amar, ido cikin ido  suke kallon juna kafin ahankali yace "wannan wani irin aure ne haka  ?taya za'ayi aure haka batare da saninta ko sanin kowa ba ?”kusani maryama nada mahaifiya ,sannan tana da kani,bayan ni kuma  tana da kannen mahaifin kunga wannan bukatar taku  ba abune mai sauki ba abu ne mai matukar wahala gara dai yaje ya  sameta idan sun daidaita kansu shikenan ni ta wajena mai sauki ne amman babu yadda zanyi mata irin wannan auren ta ina ma zan fara aikata haka ?"daman mutane suna min kallon bana qaunata ai a yanzu zasu sake tabbatar da hakan dan nasan duk runtsi duk wuya sai maganar ta fito wata rana ".

“kayi hakuri baba ka fahimcemu babu wanda zai sani daga mu biyu din nan sai kai "sam ko d'aya bazan amincewar da haka ba nan gaba ake gudu ku nemi wata alfarmar amman banda wannan ". “wannan alfarmar kawai muke bukata a wajenka wallahi  nan da wani lokaci zamu sanar mata zamu sanar da kowa ,idan ma lokaci yayi tsinke bama  so daga gareku sai ita kad'ai ,haka ma maganar hidima zamu  dauke muku nauyin komai kai ma zamu maka duk abinda kake da bukata ka fad'a min ko ya kai nawa zan mallaka maka ,jin haka yasa baba gali yayi shiru yana nazari yayinda kwakwaluwarsa tayi zurfi cikin tunani abun yi ahankali ya dinga filla filla da maganar amar dan yasan baqaramin alkhairi zai samu ba a wajensu matukar ya amince da buqatarsu amman bazai ta’ba yin haka ba lallai yana buqatar yayi magana da salma sai daya numfasa kana yace "Alhamdulilla na  gode  sosai da wannan mutuntaka  domin a gareni mutuntaka ne sai dai ina kan maganr farko kuje ku daidaita da maryama idan kunyi haka  baku da matsala dani .”

ahankali amar ya dinga binsa yana kwadaita masa irin alkhairi da zai samu idan ya amince masu shi kam mr ata tunda oga mar ya soma magana da gali bai tsoma masu baki ba haka zalika bai dago ya kallesu ba sai dai wani irin bugawa zuciyarsa take da qarfin gaske "duk naji maganarka amman ku sani ina da yan uwa mata wadanda suma suna da hakki akan yarinyar nan zan so ka bani lokaci muyi magana dasu sai lokacin mr ata ya dago idanunshi  a natse ya zuba masa tsumammun idanunshi “wato dai zargin da yayi acikin maganganun maryama na ranar farko daya fara kawota gida gaskiya ne akwai wata manakisar da mutanen gidansu suke kulla mata wanda hakan yake da alaqar fasa aurenta da maza ke yi ,kuma a kallon da yake wa baba gali ya fuskanci yana d'aya daga cikin mutanen dake damun rayuwarta ,ba iya hassada suke mata ba har da son rayuwarta ta zamo koma baya “allah sarki maryarsa "ni nasan me nayi going tru arayuwata a yanzu ba aure ko soyayya bane a gabana akwai abubuwan daya kamata nayi kafin aure bare wata aba soyayya .”

" batun  yan’uwanka wannan ba komai bane daga baya  zanmu kasance tare dakai nan gaba sai kayi mana jagora mu  gabatar da kamu a wajensu bayan nan sai  mu  aiko da magabatanmu a sake daura aure a zahiri kowa ya sani amman a yanzu baba karka yi tunanin ko gaggawa fadawa kowa dan bama son kowa ya sani mu bar maganar daga mu sai kai .”
baba gali yayi murmushin takaici yana cewa " wallahi bazan iya aikata haka batare dasaninsu ba dan a gaskiya ina tsoron fadawa cikin tashin hankali kada nazo nayi abinda maryama zata zo daga baya ta birkice mun ko mahaifiyarta gara dai kuje  ta amince masa  dan da alamun maryama bazata amince dashi bane yasa yake son aurenta boye"karkayi wannan tunanin dan kai ma kasan babu yadda zaayi maryama taki amincewa dashi kuma ni nayi imani yau adam ya furta yana sonta zata so shi  .”baba yace "nifa wannan duk ba damuwa bace idan dai har ta amince dashi ,bazan duba wani tarin abun duniya da zaa bani ba kawai abinda nake so maryama tazo min da maganarsa "amar tashi muje !” mr ata ya fad'a a zafafe yana mikewa , kai tsaye ya nufi hanyar fita daga d’akin ."ata ka tsaya mana mu gama magana dashi "bazai ta'ba fahimtarka ba ka taso muje kawai yana gama fadar haka ya qarasa ficewa ."

Akan hanyarsu ta dawowa oga amar ya kalli ata
yace "mai yasa komai kai sai kayi gajen hakuri ?"
"kai ma fa kasan wannna al'amari ba abu bane mai saukin samu ,kuma ma ni naji matukar dadi yadda talaucinsa bai sa ya bada auren maryama ta wannna hanyar ba "ba wannna bane acikin zuciyarsa idan zaka kwana kana masa magana akan auren bata lokacinka kawai zakayi ,kai yanzu baka fuskanci duk maganar da yake ba?” kasani ba gaskiyar dake cikin ransa yake fad'a ba auren ne kwatakwata baya da muradin tayi ,ba wai wannna alafarmar ne bazai iya yi ba ,kuma komai zaa bashi bazai yarda ba saboda tsananin bakinciki da hassadar da yake mata .”
sosai mr ata ya dinga nusar da shi abubuwa da dama daya dauka acikin maganganun maryama ."to tunda kasan da haka ka fito a zahiri ka mana ka fahimtar daita .”numfashi ya sauke da qarfi "zanyi qoqarin nifa ba wai ina jin shakkarta ko tsoronta bane yasa kaga zanbi ta wannan hanyar ,idan ina son maryama ta amince dani umarni kawai zan bata kuma dolenta ko tana sona ko bata sona ta amince da aurena .”dole zaka mata kenan ?mr ata yayi shiru yana ciza lip’s dinsa ,”kasani baawa mace dole akan aure kai dai kayi iyakar qoqarinka ku fahimci juna .”
Chapter 68 · 0% Book details