← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 111

Sashe 90

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda ta fara magana bai d’ago ya kalleta ba sannan kuma bai daina abinda yake ba sai a yanzu ne da sheshekar kukanta ya cika masa kunne ya d’ago kansa daga latsa wayar da yake “wace irin yarinya ce ke mai son kanki dayawa magana d’aya taki ci taki cinyewa ke mutuncinki kad’ai ne abun dubawa?”ni rayuwata acikin duhu take shi yasa kaga na damu da mutunci…. tun kafin ta Kai ga qarasa maganarta ya juya ya nufi kofar fita biyosa tai da gudu tana kiransa “sir !”bai tsaya ba har ya isa kofar shiga lifter ya shige koda ta qaraso ya kusan kai wa kasa ta danna G wato number da zata kaita qasa ta shiga tana gama qarasowa ta ganshi yana qoqarin shiga bayan mota da sauri ta qarasa bangaren daya shiga ta bud’e murfin kofar ta durkushe qasa gabansa jikinta na wani irin rawa” idan ka tafi ka barni cikin wannan halin akwai matsala dan bansan ya zanyi da rayuwata ba “ta fad’a tana mai share hawayen dake kan fuskarta idanunshi ya zuba mata gabadaya idanunta sunyi jajur dasu kafin ahankali ya motsa lip’s dinsa “wai meye damuwarki ne maryama ?”

“Wad’an nan hotunan sune damuwata kai idan family’s dinka suka ga hotunanmu bazasu damu ba wallahi ni nawa family’s din zasu damu dan Allah ka taimakeni ka taimaki rayuwata kayi wani abu akai “tsaki yaja yana cewa “bansan dalilinki ba dole sai kin raba matsalarki dani ko ni nace a d’aukenu hoton?nace ki kwanta jikina ?iya kuka kawai nace Kiyi nace ki rungumeni bare har na samu damar rungumeki ajikina?” tai saurin girgiza masa kai alamun “a’a !kafin ahankali tace “amman ai daman ka saba rungumeni ba wannan lokacin ne karo na farko ba “naji na saba amman a wancan ranar nayi qoqarin rungumeki ?shiru tai wasu sabbin hawaye nabin kuncinta “ni dai taimakon ka nake nema kayi duk abinda zakayi a goge wad’an nan hotunan dan nasan zaka iya sawa .”

numfashi ya sauke da qarfi sannan yace “tashi ki shigo muje da sauri ta mike ta zagayo ta bud’e d’ayan bangaren ta shiga ta zauna tana qoqarin rufo murfin motar ko me ta tuna ta shiga girgiza kanta da sauri ta fito daga cikin motar tana cewa
” kawai kayi tafiyarka bazan bika ba dan bansan me zai sake faruwa ba idan na binka .”“kallonta yayi a tsanake ya fahimceta sosai ahankali ya motsa lips dinsa “ki shigo muje! “ina bazan sake gangancin shiga motarka ba idan mutane suka ganmu tare hakan zai sake tabbatar masu da abinda suke zargi akanmu tun kafin ta qarasa maganarta kawai taga mutun tsaye a gabanta yana haci tmkr wani zaki da sauri taja baya “.
Yayi taku biyu ya matsota sosai yana cewa “ anya bayan wannan matsalar baki da wata damuwa ?”
”sorry sorry!! sir bani da wata damuwa kai kasan yadda al’adarmu take wad’an nan hotunan zasu iya janyo mana wani sabon zargi ne” “nace muje na saukeki a gidanku had’e hannuwanta waje d’aya tayi tana cewa “ka fahimceni wallahi mutane zasu..”ke gidanku kawai zan kaiki nayi masu bayanin komai kafin hotunan su isa garesu “what ?! ta fad’a tana zaro idanu “dan girman allah ka rufa min asiri da wani ido zan kalli aunty da umma ya Allah ka saka min akan wanda yayi min wannan cin zarafin ,mai yasa na damu sai na had’u da nadiya ? nasan if na damu da bazaka d’aukeni ka kaini wanan wajen ba” myma muje !” nifa babu inda zan..”on expecting taji ya fixgota qirjinsa da hannunsa mara ciwo ya had’eta tsam da jikinsa yana sauke numfashi wanda hakan yayi sanadiyar katseta .

a matukar rud’e ta soma magana cikin rawar murya “meye haka kake qoqarin yi ? ta fad’a tana waige waige “I don’t know and keep quite ya fad’a yana d’aura yatsan hannusa akan lips dinta “dan ..“dan Allah sir ka sakar min jiki jin yaki sakar mata jiki tace “bana ciki da iskanci kada wani yazo ya ganmu haka ka sake janyo min matsala “ni zaki cewa baki ciki da iskanci?”eh mana dan wallahi iskanci ne dan Allah ka sakar min jiki kar azo aganmu haka “karki damu ai nafi son aganmu haka ba taqamarki rashin kunya ba ?” zanyi maganinki dan na fiki iya rashin mutunci “dan Allah ka sakar min jiki “tayi maganr cikin mawuyacin hali tana haki “dan allah kayi hakuri ka sakar min jiki zan shiga da kaina .”jin haka yasa ahankali ya soma zareta jikinsa yana dubanta duk ta fita haiyacinta kwayar idanunta gabad’aya sun sake canza kala daga fari zuwa kore tsabar kuka “shiga muje wannan shine mafutar da zai kawo miki qarshen matsalarki duk wanda kike ganin zai kawo miki matsala ki had’ani dashi .”Juyin duniya yayi daita ta shiga taki “nace ki shiga zanyi wani abu akan matsalar” ta girgiza masa kai alamun a’a suna cikin haka sai ga motar madam some ta shigo haraban kallo d’aya yayi mata ya d’auke kanshi .”

bayan tayi parking ta qaraso garesu ta tsaya da girmamawa tana kallonsu wanda sai lokaci yace “daga ina kike baza ta iya masa karya ba dan muddin gasky ta fito bazai sake yarda daita ba ,dan haka tace “daga gidanku nake mumy ce ta kira tana son ganina” what?!” akan me kena?” inna ilaihi wa inna ilaihi rajiun shikenan abinda nake gudu ne yake shirin faruwa inji cewar maryama wani kallo ya d’auketa dashi mai had’e da gargadi “me tace mki da kikaje ?”ta tambayeni akan meke tsakaninka da maryama kuna soyayya ne ko kuwa ni narasa me ta gani daya sa tai ta nemi na fad’a mata abinda ke tsakaninku sir “shiru yayi kawai kafin daga bisani yace “some ki sauke min ita a gida ki tabbatar kin kaita har unguwarsu ya fad’a tare da zagawaya ya shiga gidan baya ya zauna yayinda direbansa ya shiga mazaunin direba maryama kam cikin tsananin tashin hankali ta saki baki da ido tana kallonsa hannu ya kai fuskarsa yana shafawa motar escout dinsa ne suka fara yin gaba sannan motar da yake ciki har sanda driver yaja motar idanunta na kanshi sai dai jikinta ne yake wani irin kyarma.”

Ranshi a matukar’bace ya shigo gidan da mami ya soma cin karo kallo d’aya tai masa ta fahimci yana cikin damuwa ya zauna a wata kujera” adamcy lafiya ?lfya sweetheart amman mai yasa zaki kira some zuwa gidan nan kina tambayarta akan yarinyar nan ai sai ta rainani .”
”haba adamcy meye aciki dan na tambayeta na tunanina kana son yarinyar ne sai gashi ta fahimtar dani komai”.“ ta fahimtar dake komai kamar ya?”ya tamabyeta yana mai hura hanci “ce min tayi ba soyayya bace tsakninka da maryama amman ita da kai kuna son juna da..”what ?!ya fad’a yana zaro ido waje jikinsa na d’aukar rawa” ai kuwa some tayi min sosai gata da biyayya gata kyakkyawan kawai dai matslar crista ce amamn wannan duk ba wata matsala bace tunda tana sonka kana sonta babu damuwa zata muslimta dan Allah ka aureta kaji adamcy nah duk da nasan ta ta’ba aure kuma tana da yara biyu Amman duk wannan ba damuwa bane idan akwai love ta fad’a tana guntse dariyarta “haba haba sweetheart ni nasan ko giya some ta sha bazata soma fad’a miki haka ba .”

murmushi mami tayi tana riko hannunsa cikin nata ta zaunar dashi duk bata lura da ciwonsa ba “gsky sweetheart ki sani wannan fa kuskure ne kikayi ai yakamata ki kirani kafin kice some tazo wannan ma ai sai ta rainani me zanyi daita saboda Allah wani irin lalacewa nayi haka da zan rasa wacce zan so sai some ?” meye illarta adamcy ?”mami ta fad’a tana sake kunshe dariyar ta “haba sweetheart yanzu ke bakiga illarta ba ? sam sam bangani ba sai dacewarku dana gani “to ni nasan tana da illa kuma babu wani dacewar da mukayi daita “nasan kace rashin sallah yasa kake kame kame” dan girman allah sweetheart ki bar maganar nan sam some ba kalar type dina bace bare kuma babu komai a tsakaninmu zan had’u daita qarshen aikinta ne tare dani yazo “ya fad’a yana qoqarin mikewa tsaye mami ta riko hannusa da sauri tana kallonsa tana murmushi “idan ita baka sonta maryama fa ?”“ko itama ba kalar type dinka bace “?lumshe tsumammun idanunshi yayi alokaci da mami ta kira masa sunanta hakan nan ya tsinci kanshi cikin tsananin shaukinta yana tuno yanayin daya barota.”

💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

Page 42

Mr ata ya kasa tashi daga zaunen da yake yana cigaba da tunanin maryama kukanta na d’aya daga cikin abinda yake matuqar d’aga masa hankali da tsuma zuciyarsa ,dauriya kawai yake, kasancewar soyayyar da yakewa maryama yafi wanda yakewa kanshi fatan shi Allah yasa ta so shi fiyye da komai.”sosai yayi zurfi cikin tunanin maryama yayinda mami take zaune tana kallon kyakkywan fuskar tilon d’an nata .”ahankali mr ata ya ajiye hannunsa mai ciwo a saman cinyarsa yana jijiga qafarsa d’aya wanda hakan ya bawa mami damar ganin bandage din dake hannunsa .”a matukar tsorace take kallonsa jikinta har rawa yake gurin kiran sunansa ”adamcy!” a natse ya bud’e idanunshi ya zuba mata yana dubanta a tsanake “me nake gani haka a hannunka?ko kuma nace me ya sameka a hannu?”tayi masa tambayar ajere cikin tsananin tashin hankali ahankali ya sake lumshe idanunshi yana tunanin abinda yayi sanadin jin ciwon nashi .”
Chapter 90 · 0% Book details