← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 111

Sashe 13

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"oh !
"gaskiya ne kam shiysa naga kun bukaci na dawo nayi aiki anan ? ya rufe file din hannusa da sauri yana kallon qaramin bakinta da magan Ke fitowa ta ciki ,kwata kwata babu wani alamar tsoro ko fargaba irin wanda yake hangowa a fuskar mutane dake aiki akarkashinsa idan suna tare dashi ."ni wallahi da an sani an barni alico insurance dina nayi aikina dan ma yafi kwanta min arai ."tayi mgnr tana rausayar masa da kwayar idanunta ."tsaki yaja yana motsa lip's dinsa "kisani duk inda zakije da sunan Kiyi aiki bazai ta'ba kai nan ba saboda aiki a AGC compaing ba qaramin abun alfahari bane ..."kayi kuskuren fad'ar hk sir ." ya ware tsumammun idanunshi sosai yana dubanta da mamaki kwamce a fuskarsa "eh haka na fad'a kayi kuskure sir kawai da dai da kun barni acan kawai batare da kun nuna karfin iko ba bare kace me ?mema kace ? "aiki a AGC compaing ba qaramin abun alfahari bane ."?"to a wurin wasu kenan yake abun alfahari amman ni dai abinda nayi imani dashi ko wani kamfanin na samu aiki zanji dadinsa sannna zanyi alfahari dashi kuma zanyi masu aiki mai kyau ." kun tursasa mutun yazo yayi aiki daku yanzu kuma kazo kace kayi busy dawa kenan kayi busy kai kai waye ma kai tukun ?ta fad'a a fusace .."

Mmn sudais

Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

             Page 6

     sai da gabansa yayi wani mummunar fad'uwa, zuciyarsa ke qoqarin motsawa amman ya dinga kwantar daita dan idan ya bari maganganunta sukai tasiri zai yi daya sani dan haka yayi shiru kawai ya cigaba da kallonta ba dan ya rasa abun yi  ba she's the most beautiful  girl I have ever seen in my life ya fad'a acikin zuciyarsa yayinda fuskar maryama ke cikin wani yanayi na fushi sai dai kuma kwayar idanunta na kanshi ta tsura masa idanunta kamar yadda yayi mata muryarta a sanyaye ta cigaba da motsa lip's dinta "kana tunanin dan zanyi aiki daku zan d'auki  wannan wulakanci ne ?no I can't take it any more ta  fad'a tare da zaro masa  fararen idanunta ,da wani irin sauri ya tashi daga kan kujerarsa yana cewa" yana da matukar mahimanci kisan wani abu , yana da kyau  kisan cewa kinyi mistake arayuwarki ba wai wulakanci bane kmr yadda kika d'auka, har sau biyu  kina samu aiki damu kina rejecting wacece ke da zakiyi rejecting din  aiki alokacin da kika só sannan ki so aiki alokacin da
kika so "yayi mgnr yana kallon cikin kwayar idanunta ."

Ahankali ta kawar da  kanta zuwa gefe tana hura  hanci tace  "to kuma saboda banyi joining aiki daku ba alokacin da kuka so sai ya zama matsala ? wani irin kallo yayi mata mai tattare da gargadi sannna yasa hannusa d'aya cikin aljihunsa yana kallonta yana jin wani azababben qaunarta na bin jinin jikinsa ahankali ya dinga sauke numfashi  kamar wanda  yayi  gudun tsare sannan yaja tsaki ya kai hannu sumar kanshi ya shiga ya mutsawa yana ciza gefen lips dinsa da d'an karfi "ya Allah karka sa yarinyar nan ta bani matsala "yayi mgnr a kasan ransa still yana cigaba da kallonta ." kusan mintuna goma ya d'auka yana  kallonta sannna ya koma ya zauna yana sauke numfashi ya sake d'aukar wani  file ya cigaba  dubawa sakamakon rashin abunyi "kawai kuce kun nemi na dawo ne saboda kunsan ina da baiwar fikira da zaku amfana dashi well shikenan kawai sai ku rubuta ku ajiye ya zama tarihi ga AGC  compaing ,sun ga maryam hussein na da baiwar fikira sun dawo daita aiki  byn sun koreta a ranar farko ."yana jinta  amman yayi mata banza yayi tamkar bai ji abinda ta fad'a ba haka kuma  bai d'ago ya kalleta ba ya cigaba da abinda yake yana satar kallonta  ta kasan ido yana danne bugun zuciyarsa dan wani irin sabon yanayi ya dinga jin yana shigarsa."

yayinda maryama tayita fad'ar maganganu  son ranta wannan karon kam a matukar zuciye ya  ajiye file din da yake rike dashi ya sake tashi  ya tsaya cak a gabanta yana sauke numfashi har suna iya shakar numfashi juna  da jin bugun zuciyoyinsu "Keep your mouth shut  ki kama kanki kisan irin maganar da zakiyi anan dan ba'a kawo min raini , ba'a sakani kuma ba'a hanani and no body question me okay ."ya fad'a a matukar tsawace yana  sanya kwayar idanunshi cikin nata, shi aiki da mahimanci ake d'aukarsa kamar yadda  shi mai kasuwanci yake d'aukar kasuwancinsa ,ban dawo dake dan kizo kina min haukan banza anan ba, na koreki ne saboda na nuna miki kuskurenki, sannna na dawo dake  ne saboda tausayawa domin na fahimci kin shiga tashin hankali mai tsanani a wancan ranar dana koreki idan zaki iya aiki damu kiyi  idan kuma bazaki ba "leave!ya nuna mata hanyar waje da d'an yatsansa yana fesar da huci mai zafi daga bakinsa yayinda zuciyarsa ke cike da matsanancin fargaba dan yasan kad'an da aikinta zata iya  juyawa  ta kama gabanta ."

adduar ya shiga yi domin neman taimakon Allah" ya Allah kada kasa zantuttukana suyi tasiri a zuciyarta Allah kasani ina matukar son yarinyar nan da d'aukacin rayuwata  ta shiga zuciyata dayawa ta sace zuciyata,ya  Allah kasa na shiga cikin rayuwarta kamar yadda ka shigo daita cikin rayuwata domin ta zamo abokiyar rayuwata ta har abada ina matukar qaunar wannan halitta taka ya Allah ka jarabeta da soyayyata tun kafin na kai ga furta mata soyayyarta dake raina domin na azabtu akanta ,na sha wahala akanta ,ya Allah ka tausaya min ."Ita kuwa maryama shiru tayi na second goma tana dubansa batare da tace masa komai ba har ya gama maganarsa sai dai maganarsa tasa zuciyarta tayi sanyi daga zafin datayi tare da tunani ,duk da ya jefeta da kalmar hauka amman kuma ta wani bangaren sai taji  kamar ya fita  gsky domin kuwa a wannan zamani aiki wahala yake, idan ba kana  da hanyar samunsa ba  ko wata baiwa ba sai dai ka mutu haka babu aiki amman da kwalinka da karatunka sai su zama banza bazasu maka amfani ba ."dan haka Ke maryama kiyi maza maza ki  shiga taitayinki ki dawo cikin hankalinki karki yarda Kiyi kuskuren da zaki sake rasa aikin nan dan haka muryarta a sanyaye tace "shikenan zanyi aiki da amana da gasky kuma in sha allahu kamfaninku  zatai alfahari da ... "da kyau go back to work ." yayi sauri katseta ta hanyar  fad'ar hk  batare daya kalleta ba duk da kallon nata yake da bukata dan baya gajiya da kallonta amman ya kasa sai ma boyayyayen ajiyar zuciya ya sauke dan maganrta ba qaramin dadi sukai masa ba ."

"Yanzu ko zan iya sanin da me zan  fara ?meet sectary "ya fad'a a dake ,ta juya jikin a sanyaye  har ta kama handle   zata bud'e kofa ya tsaidaita ta hanyar cewa "ke .." ta tsaya cak batare data juyo ba  sai dai qirjinta na wani irin bugawa  da sauri sauri "idan zaki zo  aiki gobe karki kuskure kizo min da wannan package  din,  kizo cikin tsari shigar aiki Kmr  kowani ma'aikaci ."da sauri ta juyo tana masa kallon tsana zuciyarta cike da mamaki to mai ya samu kayanta ?ta jefawa kanta tambaya tana dubansa bai  kalleta ba sai dai ta  kasan idanunshi yake d'aukar kallonta tana kallonsa ya janyo system gabansa ya cigaba da aiki ta bud'e kofa ta mayar  da karfi  ji kake kiiiiii  har sai daya d'ago yana duban kofar kai kawai ya girgiza tare da furta cray girl kawai ."maryama ta fice tana jan tsaki ranta duk babu dadi  "a hankali ta dinga  tunanin maganga nunsa gabadaya maganarsa babu dadi sai bugar da zuciya  da saka mutun cikin tashin hankali ta sake jan tsaki tana maimaita kalmarsa ta karshe "idan zaki zo aiki gobe karki kuskure kizo min da wannan package  din, kizo cikin tsari Kmr  kowani ma'aikaci har ta shiga babban  office din daaka tanada masu a ranar farko maganarsa bata bar zuciyarta da gangar jikknta sun huta ba ."

anan taga yusura tana ganinta  ta qaraso da sauri ta rungume maryama  tana cewa  "kai naji dadi kawata da kika sake dawowa amman fa Kiyi hattara da mr ATA  da mr sultan dan ba kai  garesu ba kowa anan tsoronsu yake ji ,suna cikin mgn  sultana ta shigo tana cewa "maryam hussein  sannu da dawowa compaing mu " wani kallo mryma  tayi mata na mamaki  fuskarta da alamun tmby "yes ! Ok fa a she bakisani ba ko, to bari na fadi miki wannan kamfanin had'in gwiwar iyayenmu ne ni cousing sister din Mr ATA ce nan maryama ta fahimceta sai dai bata ce mata uhmm bare uhmm uhm  .""Kinyi  sa'a da kika   dawo wannan kamfanin  amman kuma Kisani  nice nan  sanadin dawowarki domin nice na nunawa ya Adam zanenki da kikayi wanda tashin hankali an koreki yasa kika tafi kika barshi "shiru  maryama  tayi kafin a hankali tace "na gode excuse"ta fad'a sannan ta ra'ba ta gefenta ta wuce ."
Gabdaya suka samu guri suka zauna akan makeken table din dake  zagaye da office din ."maryama ta bud'e jakar kayan aikinta  ta d'auko abun aikinta hanakalinta kwance ta fara gudanar da aikinta "wannna duk wahalar banza kikeyi domin duk kwarewarki bashi zai sa ki burge ya adam  ba tana gama fadar haka fita daga office din maryama tabi bayanta da kallon mamaki  ."
Chapter 13 · 0% Book details