← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 111

Sashe 84

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ahankali ATA yake kallonta cike da tsananin shaukin qaunarta yayinda cike da yanayi na tsananin damuwa yaga ta janyo gefen mayafinta tana goge hawayen dake fita daga cikin kwarnin idanunta ganin hawaye take zubarwa hakan ya sake kunno wutar damuwarsa”oh my goodness god !”yanzu menene abun kuka kuma ?” ya furta a fili yana mai runtse tsumammun idanunshi tare da Jin wani irin tausayinta na ratsa tsantsar jikinsa “why zanji tausayinta bayan ni ne abun tausayi? ya furta yana jan tsaki sannan ya Kai hannunsa ya dafe saman goshinsa yana murzawa yana jin wani irin zafi da ciwo yayinda zuciyarsa ta dinga tuttukin bakinciki”why maryama!”? “mai yasa baza ki fahimci irin zunzu runtun qaunar da nake miki ba?”kusan minti shabiyar yana tsaye zuciyarsa na jin rad’adin azabar rashin son data furta masa yanzu, kafin ahankali ya bud’e idanunshi ya tsura mata daga inda yake har lokacin tana zaune tana janyo numfashi da kyar.”yayi shiru tare da tura hannuwansa duka cikin aljihun wondonsa yana taku acikin office din ,wani tunani yayi dan haka nan take ya soma taku ahankali ya qaraso zuwa bakin kofar office dinsu ya tsaya tare da rike kugunsa yayinda kwayar idanunshi ke yawo a sansar jikinta ”

“qamshin turarensa daya kawowa hancinta ziyara ne yasa ta sauke wani naunauyen ajiyar zuciya ,sai dai ta qara sunkuyar da kanta qasa tana kallonsa tsaye a bakin kofar shigowa shi bai shigo ciki ba shi bai juya ya wuce ba, wanda hakan yayi sanadiyyar da gaban ta ya dinga dokawa da qarfi gefe guda kuma ta dinga jin wani sabon tashin hankali from know where yana shigarta.” ahankali take hango tahowarsa zuwa inda take zaune gabanta ne ya cigaba da lugud’en bugu tana zaune har ya iso inda take ya tsaya kyam yana kallonta tamkar ranar ya fara ganinta .”
d’ago kanta tayi tana mai mikewa tsaye da sauri tare da goge hawayen idanunta ,bai ce mata uffan ba illa tsumammun idanunshi daya zuba mata tamkar zai cinyeta wanda yasa nan take numfashinta ya dinga sauka da sauri sauri ta tsarke yatsun hannunta cikin juna tana sake jin mummunar fad’uwar gaba mai tsanani, bata san dalili ba amman kwata kwata bata son ganin yanayinsa haka domin yanayi ne dake matukar d’aga mata hankali da tsorata zuciya da gangar jikinta.”

tsurawa juna ido sukai na second goma kafin ahankali ata ya janye kwayar idanunshi akanta yana mai shafa sumar kanshi ,wani abu yaji yana tsarga masa tun daga tsakiyar kanshi har zuwa yatsun qafafun sa,ganin har loakcin kuka take wanda shi aganinsa shi ya kamaci yayi mata kuka saka makon mahaukacin soyayyarta dake huda duk wani sansar na jikinsa .”cikin wani irin sauri zuciyarsa yake bugawa kamar zata fito daga cikin qirjinsa nan take tausayin kanshi ya kama shi bai san sanda ya buga mata wani razanannen tsawa tare da furta “enough maryama !” nan take kukan da take ya tsaya cak sai shesheka “bana son jin sautin sheshekar kukan !”nan take shima ta had’iye jikinta na wani irin rawa, yanayinsa ya qara mata jin tsorasa “. matsota yayi sosai sukai mugun daf da juna da sauri ta d’auke numfa shi ,da zai qara taku guda tak to lallai zasu had’e cikin juna “maryama !”ya kira sunanta cikin wata irin kasalalliyar murya mai matuqar ratsa zuciya “kasa amsawa tayi ila ta kame jikinta waje d’aya tana mai sake sunkuyar da kanta had’e da tattaro jarumta ta sanyawa jikinta“I don’t want to see your tears .”da sauri ta d’ago kanta ,a natse ta zuba masa shayayyun idanunta still akwai ruwan hawaye acikinsu “ki goge hawayen nan ki kuma saki fuskarki .” ido cikin ido take kallonta ko kifta idanunta batayi,shima bangaresna kallonta yake yana faman busa mata hucin numfashinsa.”

Ta dinga jin kamar ta barshi ta kama gabanta amman kuma Tana tsananin jin tsoron abinda zai biyo baya dan a kallon da take masa zai iya aikata komai “smile !” ta jiyo fitowar sautin daga bakinsa.a d’an rikice take kallonsa batare da tayi abinda ya bukata ba “nace kiyi dariya”! Dan banason ganin wannan yanayin akan fuskarki “gaba daya maryama ta rud’e ta gigice tana kallonsa da sabon mamaki akan fuskarta “nace kiyi dariya !”wannan karon a fusace yayi maganar batasan sanda ta soma murmushin yake ba wanda ya bayyana d’an murmushin a saman lebbansa yayinda idanunshi ke kanta .”

Ganin irin kallon da yake mata yasa ta janye jikinta tana cigaba da murmushin data saka masa sunah “gashi karka kasheni a natse tabi gefensa ta wuce tana taku a natse ,ya tsura ma bayanta ido yana kallonta tana taku ahankali ,wani naunauyen ajiyar zuciya ya sauke kai tsaye office dinsa ta nufa ta duka ta d’auki jakarta ta fito ta nufi hanyar fita, tafiya kad’an tayi ya juyo taga ita yake kallo ido cikin ido suke kallon juna sannan ta
Sake juyawa” mai yasa nasa tayi dariya ?”nasa tayi dariya dan na daina jin damuwa acikin raina amman har yanzu ban daina jin abinda nake ji ba mai kuma zanyi na samu natsuwar zuciya? Ina son naji farinciki amman kuma na rasa samun wannan farinciki what do I want?”ya furta a fili yana Jan tsaki Allah yasa kar yarinyar ta kasheni !ta kasheka ko dai ka kashe kanka da kanka,haka kawai ka zauna kana cutar da kanka a banza numfashi ya sauke da qarfi ya samu waje ya akan kujera ya zauna yana kallon hanyar data bi.”

Ahankali aunty hassana ta fito daga cikin d’akin umma hannunta rike da takardar gidan biredi,adaidai lokacin umma ta shigo dan dama ba fita tayi ba d’akin yaya sadam ta shiga da sauri aunty hasana ta zauna akan kujera tana tura takarda qarqashinta tasa hannunta ta dafe goshinta ,umma ta tsaya tana kallonta kafin ahankali ta qaraso tana cewa“lafiya hasana meke damunki ?wallahi kaina ke min wani irin ciwo shigowa nayi ko zan samu magani a wajenki “okay bari na duba miki ko zaa samu magani wayyo allah kaina kamar zai cire ,umma ta nufi d’akinta da d’an saurinta cikin kankanin lokaci umma ta fito ta tsaya gabanta tana cewa”kar’bi ki sha .” aunty hassana tasa hannun ta amsa tana sauke numfashi da kyar tace “na gode aunty tana qoqarin kai magani bakinta taji umma tace “ki sha maganin idan kin gama sha ki tashi na d’auki takardar da kika saka qarqashinnki.” a matukar tsorace aunty hasana ta tsurawa Umma ido tana kallonta gabanta na faduwa “ki sha maganin ba kanki ke ciwo ba ?

Aunty hassana tai shiru cikin tsananin tashin hankali “idan bazaki sha ba ki mike na d’auki takardar” jikinta a sanyaye ta mike tsaye sai ga takardun gidan biredinsu ,umma tasa hannu ta d’auka “yanzu dake za’a had’a baki a cuceni na yarda na amince dake amman da irin abinda zaki saka min kenan ? kije ke da allah amman karki sake shigowa zuwa inda nake na rantse da ..”da sauri aunty hasaana ta zube kasa tana kuka tun kafin umma ta ida maganarta “dan girman Allah aunty Kiyi hakuri wallahi ba halina bane yaya gali ne ya turo ne ,ki yafe min wallahi bazan sake ba ,ai baki ta’ba kamani da irin wannan halin ba ko tunda muke dake kin ta’ba neman wani abu naki kin rasa?”wannan ma sausauyi ne ,ki yafe min idan kika sake kamani da laifi makamancinsa na yarda ki dauki duk matakin da kika ga dama numfashi umma ta sauke batare da tace komai inda aunty hassana tayita mata kuka tana mata magiya da kyar dai ta samu umma tace ta tashi taje zatai tunani jiki a sanyayye aunty hassana ta mike tsaye ta nufi kofar fita zuciyarta cike da nadamar abinda ta aikata.”
Chapter 84 · 0% Book details