← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 111

Sashe 33

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“ahankali mr ata ya cigaba da tafiya har ya kawo inda direbansa yake idanunta na kashi shi din ma tausayinsa ne ya dinga shigarta yana bin kowacce jijiya dake aiki ajikinta ,yayinda zuciyarta ke wani irin tsinkewa akanshi tare da tsananin jin tsorona jikinta baqaramin sanyi yayi ba jin irin maganganun da sukai ta fitowa daga bakinsa tabbas bata kyauta masa ba amman shima abinda yayi mata ba kamata ba kamata yayi ya mata adalci .”Mr ata bai tsaya direbansa ya bud’e masa murfin mota ba ya bud’e da karfi ya shiga ya zauna zuciyarsa na tsananin dokawa kamar zata fashi .”direba ya shiga gaban mota da sauri yaja suka wuce.” duk wayar da’ake doka masa bai d’aga ko d’aya ba dan koya daga bazai iya magana ba saboda bala’i n dake cinsa dan jikinsa banda kyarma da fitar da zufa babu abinda yake .”kai tsaye gida yace a wuce dashi tafiya mintuna talatin suka qaraso abdullahi estate direba bai gama daidaita tsayuwar parking din motar ba ya bud’e murfin mota a zuciye ya fito da sauri ya shiga part din mahaifiyarsa .”

A fusace ya shiga parlour’n inda kai tsaye ya wuce maryam tare da mami zaune hira ya haye samansa batare da ya cewa mami qala ba mami na ganin haka tasan ba lafiya ya shigo ba ,dan haka ta mike. yana shiga d’akinsa ya hau cire kayansa yana fillinging dasu sannan ya fad’a bathroom ya shiga bathtube ya cika da ruwa ya shiga ya kwanta aciki. ruwan na shiga jikinsa ya kai hannunsa daidai saitin qirjinsa ya dinga shafawa ahankali yana furzar da iska yana tunanin sambatun maryama “Shikenan na rasaka sadam da gaske ka matu baka raye abida ya dinga ji yana fita daga bakinta kenan lokacin daya yi kusa daita ya lumshe tsumammun idanunshi yana girgiza kanshi nan take maganarta ta shiga masa kuwa acikin kunnuwansa da brain dinsa “Jiya ina tsaka da aiki sai bacci ya d’aukeni acikn baccina nayi mafarkin yaya sadam adaidai farm center “.

“very stupid girl kawai bakiyi tunanina ba sai wani banza da baya exit a duniya nonsense girl kawai.” ya fad’a yana sake lumshe tsumammun idanunshi wani zazzafan kishi na taso masa ya dade kwance acikin ruwan dan ya d’auki sama da mintuna talatin sannan ya fito kugunsa d’aure da farin towl yayinda dayan hannunsa Ke rike da wani qaramin towel yana goge sansar jikinsa .”byn ya gama goge koina ajikinsa ya d’auki daddad’an turare body’s spare ya feshe ilahirin jikinsa ya shirya kansa cikin kaya wondo da riga marasa nauyi ya zauna a gefen gadonsa ya mike qafafuwansa tunanin maryama ne har lokacin Ke dawainiya dashi yana zaune mami ta shigo hannunta rike da black cup wanda shigowarta na uku kenan dan ta shigo sau biyu yana wanka “Lafiya tunanin me kakeyi haka ?tayi masa tmbyr tana tattara hankalinta kacokan akanshi sai daya sauke numfashi da ajiyar zuciya atare sannan ya girgiza mata kai alamun babu komai ta mika masa black cup dinsa dake rike a hannunta wanda Ke d’auke da coffee” idan kana da damuwa adamcy karka boye ma mahaifiyarka.”

ya gyad’a mata kai kawai batare daya ce mata komai ba” shikenan idan ka gama sha ka sauko kaci abinci still kai ya gyada mata ta fita ta barshi yana kur’ban coffe yana tunani ,gbdy so yake ya fahimtar daita cewar yaga mafarkinsa da irin matsalar da yake fuskanta akanta amman yana jin tsoron abinda zai fito daga bakinta ,wata killa ma bazata amince da maganar ba kodan sbd matsalarsa da maryam .
Bugu da qari zaa iya samun matsala a bangaren ita maryama din karta zo taki amincewa dashi bayan ya sheida mata , dan a yadda yake kallonta wancan matacce mutumin ya tafi da zuciyarta da rayuwarta gabad’aya soyayyarta ta mutu akanshi ba lallai ta fahimcesa ba bare ta fahimci irin tarin qaunar da yake mata .”

gbdy idanunsa sun sauya kala fuskar maryama kawai yake gani ko a wani hali take ciki a inda ya barota numfasawa yayi yana dafe goshinsa yace “anya kuwa banyi kasadar barinta a wajen nan ba ?“anya kuwa bazan tura a ruwa ya koma ya dauketa ya kaita gida ba ?”wannan tunani yasa shi ya mike yayi taku zuwa inda wayoyinsa suke akan mirrow ya dauki d’aya daga ciki ya soma kiran layin aruwa bayan ya d’aga ya bashi umarni abinda yake son yayi sannan ya katse kiran ya koma ya zauna yana fidda numfashi sama sama.” bai sauko ya cin komai ba ya kwanta yana runtse tsumammun idanunshi tare da rungume hannuwansa duka aqirjnsa yana jin yadda soyayyarta ke fixgarsa .”

Bangaren maryama kuwa da kyar ta yunkura ta mike ta nufi gidan cikin tashin hankali wuni daya amman idan kaganta ta fita haiyacinta ta rame da kyar take daga qafafunta tana shiga gidansu bangaren umma ta nufa a falo ta sameta ita kad’ai umma tana ganin yanayin maryama ta mike da sauri ta tarbota ai kuwa ta zube ajiknta tana kuka “Lafiya maryama meke faruwa dake naganki kamar baa haiyacinki kike ba?umma …”sai kuma ta fashe da kuka ta kasa qarasa mgn nan fa hankalin umma ya sake tashi ta mike taje ta kawo mata ruwa a glass cup ta kai bakinta “sha ruwa kiji sanyi .”ta kurbi kad’an tana sauke naunayen ajiyar zuciya .”

umma ta sake tmbyarta bata boyewa umma komai ba ,ta zayyane mata duk abinda ya faru “wannan laifinki ne maryama shiru tayi tana duban umman bazaki fahimci yadda mutun yake shiga idan yayi alkawarin cika aiki ba “umma nima ban so haka ba nayi kokarin nayi masa aikinsa koma dai menene wannan laifinki né d’an ya kamata ki qarasa masa aikinsa ki kai masa albashi daga baya sai ki nemi excuse ki tafi duk inda zaki “shiru maryama ta sake yi tana tunanin maganganunsa “babu wani mutun da ya isa ya fadawa adam tariq abdullah magana akan aiki amman yau anyi ,and it happened because of you “gsky umma nayi kuskure amman idan kikaga yadda mr ATA ya zageni gabadaya ya hanani cewa komai “.ai duk ya faru ne saboda kuskurenki ko haka kawai zai fada miki magana “?

“Kinsan irin asarar da kikasani wai Ke dame kike takama ya tsaidaita ?”Kinsan yadda kasuwancina yake da matukar mahimanci agurina gabaday na daura raina akan designs dinki nasaka raina nayiwa wanda zaizo yagani alkwari amman sai kika ki zuwa kuma idan na kiraki sai Kiyi rijecting din kirana me ma kike yi anan ki bani amsa .”?maganarsa ta shiga yawo acikin brain dinta” idan kinje office gobe ki tabbatar kin bashi hakuri ki nuna masa kinyi Kuskure gyad’awa umma kai kawai tayi .”alamu taji .

*****
Daren ranar daga maryama har mr ATA babu wanda ya runtsa kwana sukayi cikin tunanin juna da maganganun juna ta mike zaune akan gado ta jingina bayanta tare da daga idanunta sama “wai a haka kike son ki zama profetional a ma’aikatan mu?Kinawa mutane iskanci da kika ga dama saboda kina daukar wai dan kin iya designed yasa kike samun aiki cikin sauki ? gabadaya zagin da yayi mata babu wanda ta manta yadda take zaune haka shima bai tsaya iya daki ba har kasa falon mami ya sauko ya dinga tafiya tamkar wanda bai da laka ajikinsa ya wuce ya karya kwana zuwa parlour’nta na biyu tun saukowarsa maryam taji ajikinta dan daman baccin nata rabi da rabi né .sad’af sad’af ta fito ta gansa zaune akan kujera yayi shiru cikin tsananin tunani shiru tayi tana qare masa kallon taso ta qarasa garesa ta tambayesa damuwarsa amman tasan halinsa komai zatayi bazai ma saurareta ba ta jima tsaye kafin daga baya ta juya tana masa fatan sausauci duk da batasan abinda ke damunsa ba .”
Ya dinga jin kamar ya kirata yaji muryarta ko hankalinsa ya dan kwanta tunda a ruwa ya tabbatar masa da yaje bai sameta a wajen ba .”

Washegari daga maryam har mr ATA babu wanda
yayi kokarin zuwa aiki kwamciyata tayi dan tasan tana zuwa zai korata idan taci saa ma bai hada mata da zagi da tozarci ba, sam ransa bai iya baci ba idan ransa ya baci baya control din kansa “numfashi ta sauke tana cewa “wallahi matarka tana dan katoton matsala ta fada gabanta fadawa bangarensa shima zama yayi adaki bayan yayi wanka ya sauya kaya yana zaune mami tashigo kamar daren jiya tmbyrsa ta soma yi stil yace babu komai “idan zaka boyewa kowa damuwarka adamcy banda mahaifiya yadda bazaka yadani ba nima haka né bani da kamarka damuwarka damuwatace “sweetheart maryama ce !”ya furta yana jin bugun zuciyarsa na qaruwa .”wacece ma haka ?ta tambayesa tana tattara gabad’aya natsuwarta garesa .”

Ya d’auki minti goma sannan ya motsa labbansa yace “wannan sabuwar maaikaciyar dana d’auka ce “
ya fad’a yana sauke numfashi “ me tayi maka wanda har ya hana rayuwarka sukuni?”yayi shiru ya kasa magana “ fadawa sweetheart dinka abinda tayi maka still shiru yayi yana tunanin ta ina zai fara mata bayani ta tsura masa idanunta sosai tana karantarsa tare da nazarinsa daman kuma maryam ta fad’a mata daren jiya bai yi bacci ba gashi yayi sanadiyar daya zauna gida bashi da niyyar fita office
“Adamcy!
Chapter 33 · 0% Book details