← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 111

Sashe 26

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ahankali taga ya girgiza kai sannan ya kalleta sai dai murmushin mugunta ne kwance akan fuskarsa "ina jinki !?ta mika masa takardar hannunta ya kalla sosai ya kwa’be baki tare da cewa "bai min ba ."bai maka ba ?ya d’age mata girarsa d’aya alamun Eh!me kake nufi sir ?” abinda nake nufi ai kinji baya bukatar na sake maimaitawa tayi shiru tana dubansa qirjinta na dukan tara tara “maryama ! ya kira sunanta cikin wani irin yanayi wanda yasa tsigar jikinta suka mike "yana da kyau ki canza wani kuma a yanzu ya fad'a yana d’auke kansa.” muryarta na rawa tace "okay sir amman me zai hana na tafi gida zuwa gobe sai na qarasa "no! A yau nake bukata leave” ya d’aga mata hannu alamun ya sallameta babu shiri ta fita tun kafin ya sake yanka mata wani sabon wulakanci.”

Bayan fitarta "sectary tace "sir amman gabadaya aikin maryama sunyi kyau "na sani! nasan sunyi kyau but ina bukatar wanda yafi wanda tayi ,”gsky tana da bambamci da sauran masu zane kawai dai tana da matsala ne yana magana yana daddana keyboard zanenta yayi sosai in fact ma ban ta'ba ganin zane mai kyawun nata ba” ya qarasa mgnr yana lumshe ido so yake ya azabtar daita akan kasadar data so masa, yanzu da sultan ya za’beta fa ?ya sake tmbyar kansa yana jin fad’uwar gaba "da komai zai faru sai na dawo daita karkashina ya bawa kansa amsa ."

Tattara kayanta tayi ta dawo office din sectary dan ta gaji da shige da fice ,ta sakê dukufa akan aikita ta bud’e wani takarda ta ajiye tana dubawa ta cigaba da zanen ,tayi zane taga baiyi ba ta dunkule ta yar da takardar ta sake bud’e wani shima haka ta d’aura pencil a bakinta lokacin sultana ta shigo ta wuceta ta shiga office din mr ata "haba yaya me yasa zaka min hk bayan kasan  saboda kai na zabi aiki akar kashinka"me zanyi ai yayanki ne shima kuje can ku qarata dan ni ban d’aukeki a matsayin mai aiki ba saboda you're totally nonsense ,duk maganganun da suke maryama tana iya jiyowa sai dai ko d’ago kanta batayi ba .”

waya ya d’aga yayi maganr second goma sannan ya ajiye ya tashi yana tafiya ahankali ya fito har yayi taku biyu kafarsa taci karo da daya daga cikin takardun da marayama ta yar  anatse ya kai idanunshi kafin daga baya ya dan ja wondonsa kad’an ya duka tare da dauka ya mike had’e bud’ewa a hankali yana dubawa taga tsayuwarsa amman ko kallonsa batayi ba, ta cigaba da abinda take dan tunaninta ba’a wurinsa yake ba tunanin yadda zata masa abinda yake bukata ta kama gabanta take ."

Ya cigaba da kallo mace ta fara zanawa sanye da kayan weeding ajikinta a hankali ta d’ago tana kallonsa tsaye ya d’aura hannusa d’aya akan kujera ,d’ayan kuma yana rike da takardan ahanakali ta mike tsaye a daidai lokacin ya kalleta cikin sa’a idanunsu ya tsarke ckin juna saurin dauke idanunta tai ta maida Kan aikinta tana tunanin tare da sa pencil abakinta shi kuwa tundaya daura idanunshi akanta bai dauke ba sai daya kai minti talatin "sir sir!! ammm "Nace kice wani abu ne ?shiru tayi kawai tana kallonsa ya maida idanushi kan zanen da take yanzu wani yanayi suka tsinci kansu “set! ta kasa zama Kmr yadda ya bukata  ya mika mata hannu alamun ta bashi pencil din hannunta ,babu mutsu ta goge kan pencil din saboda ta sakashi cikin bakinta ta mika masa ya kar’ba ya d’aura akan zenen da take ."

"Me kike qoqarin zanawa anan ?”Abinda ka bukata ne sir “ta bashi amsa anatse cike da kwarewa ya shiga gyara mata yana mata bayanin yadda zatai sun d’auki lokaci yana mata bayani sultan yazo ya wuce kasancewar koina a wurin glass ne duk yadda zaka wuce zaka ga mutun kawai idanunshi ya sauka akansu ya tsaya yana qare masu kallo batare da sun sani ba amamn yaso ace yasan me suke tautaunawa akai sai dai babu damar hakan dan hk ya wuce ya kama gabansa ."

Mr ATA yayi mata gyara sosai kinga yadda zakiyi amman kin tsaya salo da son nuna iyawa alhalin duk nonsense kike zanawa.” yana gama fad’ar haka ya ajiye pencil din hannunsa duk da ya zageta amman fuskarta cike take da farinciki ,tace "kai gaskiya yayi kyau sosai ,ya kad’a kai ai kinga yadda ake yi amman kin damu mutane kin iya zane yanzu kin fahimci ba iya kwarewarki yasa aka nemoki kiyi aiki anan ba ?”ta gyad’a masa kai alamun “”eh!har ya juya ta kirasa "sir! ya juyo yana kallonta a tsanake yana jin wani iri akanta abinda yake ji akanta na dabam ne ,abu ne da bai ta'ba jinsa akan kowace mace ba. abun ne mai tsaya wa arai .”

“Ko zan iya cewa wani abu ? karki ce komai dan bana son jin komai ki zauan ki cigaba da aiki kawai kai ta gyd’a masa shi kuma yasa kai ya wuce ."ta sake zama ta cigaba da aiki bayan kamar second goma ya shigo hannunsa rike da cup biyu d’auke da coffee ya ajiye mata cup d’aya mai d’auke da sunan kamfaninsu sannna ya kalli aikinta ta kallesa “sir dan allah ka bari na tafi gida lokaci ya soma ja hankalin iyayena zai tashi “babu inda zaki sai kin gama min aikina ya sake juyawa rike da nashi cup din yana kur’ba ahankali .”

Sosai tayi concentrate akan aikinta ta sake zaro wata takarda ta cigaba a natse ya fito daga office dinsa zai fita idanunshi ya sauka akanta diret inda take ya nufa ya tsaya yana kallonta yana tsaye sectary dinsa ta qaraso ta tsaya tana cewa” sir ina bukatar ka saka hannunka anan ya cire hannunsa d’aya cikin aljihunsa ya amshi biron hannunta ya saka hannu yana saka hannu amman hankalinsa da idanunshi yana kan maryama ita kanta sectary tana lura dashi tana mamakin yadda ya damu da yarinyar da yadda yake yawon kallonta byn duk ba haka yakewa sauran yammatan dake aiki akarkashin ba ."

Bayan ya gama ta wuce shi kuma ya qarasa kusa da maryama yayi daf daita sosai ,hannunsa d’aya cikin ajihun wondonsa yana duban aikin da take ,jin tsayuwar mutun yasa ta d’ago idanunsu suka tsarke cikin juna suka dinga kallon juna har basa son ko kifta idanunsu da kyar ya iya d’auke idanunshi ya kalli zanen da take "har yanzu kina Kan aikin nan ?"eh ina kai sir kokari nake na qarasa na wuce na tafi gida “yayi shiru yana tunani dan baya son ta wuce abu biyu ne aransa yana son hukuntata ta hanyar ‘bata mata lokaci haka kuma baya son tayi nisa dashi dan yana son akoda yaushe tana kusa dashi yana matukar son ya bayyana mata sirrin dake ranshi amman ya fuskanci yarinyar tana da matukar zafin kai da tsautsauran raayi tare da rainin hankali ,ba lallai lokaci daya ya samu had’in kanta ba ."

Ya kalli zanen sannan ya d’auki pencil yana sake mata bayanin yadda zatai daga can bayansu kuwa sultana ce tsaye tana dubansu ashe bata wuce gida ba idan fa tayi sakaci wannan yarinyar zata yi galaba akan ya Adam zata iya mallake zuciyarsa dan taga gbdy ya maida hankalinsa kanta abinda bata ‘bata gani ba kenan sauraran wata yarinya ko kula da ayyukan ma'aikatan dake kula da kamfanin yayinda a bayan sultana sultan ne ya tsaya yana sauke numfashi "kiyi hattara wannan yarinyar ta kware sosai akan aikinta irinsu ATA yake bukata dan tasan aikinta ni nayi danasani da ban d’auketa ba idan kikayi sake zakiyi loosing opportunities dinki na zuwanki wannan kamfanin domin ki siye zuciyarsa ,ya kamata kiyi duk abinda zakiyi wannan yarinyar ta bar kamfaninan .”

ranta a matukar ‘bace ta juyo tana kallonsa “ kai me yasa bakawa mutun fatan alkhairi sai na tsiya addua ya kamata ka min saboda kasan yadda nake son ya Adam arayuwata bai kamata ka fad'a min hk ba ,ba wai bai kamata ba kawai Kiyi abinda ya dace ba sha shanci ba yana gama fad’ar hk ya juya ya koma office dinsa itama ta juya ."

Mr ATA ya ajiye pecil din hannunsa sannan ya juya ya wuce har yayi taku biyu tace"sir ko zan iya wucewa gida yanzu saboda lokaci ya tafi sosai tayi mgnr tana duba agogon hannunta ya kalleta a natse yace " bake ba barin wurin nan sai kin qarasa aikin nan domin ina bukatarsa karfe bakwai daidai zaa zo akar’ba yana gama fadar haka ya juya ta koma ta zauna hankalinta a matukar tashe tare da saka pencil acikin bakinta can dai taga bata da wani mafutar da ya wuce ta cigaba da aikinta  fitsari ta soma ji sosai  marayama ta mike tsaye sakamakon marata dake kokarin kulewa ta nufi bayi tana shiga sultana ta qaraso taga yanayin zanenta yayi kyau sosai zane ne da zai d’auki hankali mutun hakan yasa haushi ya kamata lallai sultan yayi gsky idan batayi hattara ba wannna yarinyar zata gama da zuciyar ya Adam dan haka ta d’auki cup din coffe din da mr ATA ya ajiyewa maryama ta  juye gbdy akan zanen ta bar wajen da sauri ta koma gefe ta tsaya tana jiran taga me zai faru ."

maryama na dawowa ta iske tashin hankali nan take ta gigice ta dinga kallon zanen tana kuka ta d’auki d’aya daga ciki takardan wani ma har ya fara yagewa tana kallo "waye yayi min hk ?garin yaya haka ta kasance ?cikin haka mr ATA ya shigo sakamakon jin sautin kukanta idanunshi ya sauka akan zanen "what !?ya furta da karfi me ye haka zan gani Ke fa nake jira dan by this time ya kamata ace ina gida "?nima haka na gani na shiga toilet nayi fitsari na dawo na gansu haka "you're very stupid” ya fad'a a zafafe yana duba zanen sultana dake gefe babu abinda take sai murmushin jin dadi tayi Kmr bata gansu ba "amman dai ke anyi dakikiyar yarinya wani irin iskanci ne hk ?garin yaya ma haka ta faru ?”
Chapter 26 · 0% Book details