← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 111

Sashe 3

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

fitarsu ke da wuya  ya sauke wani wahalallen numfashi ."ahankali ya zauna jagwab akan kujera kwakwaluwarsa ce ta shiga caji na neman mafuta dan dole yasan abun yi anya kuwa bazai d'auki shawarar ammar ba ?ya furta hakan a fili zufa na tsatsafo masa a saman goshinsa da karan hancinsa ahankali ya soma magana shi kadai"adam dan dole ka nemawa kanka mafuta dan zuciyarka na tsananin son yarinyar nan akanta kai ba kowa bane ka tuna tun lokacin daka dauka kana dakon soyayyarta  tana da tasiri acikin rayuwarka kamar yadda ammar ya fad'a "to mai zanyi ?mai zanyi ?!!yayiwa kanshi tambayar da bashi da mai bashi amsa shiru yayi yayinda ya maida idanunshi ya runtse gam yana jin wani irin zafi mai tarwatsa  sansar jiki."yayinda bangaren salim da ammar kuwa tautaunawa suke akan abinda ya faru salim ya dubi ammar dake gefensa  hankalinsa a matukar tashe ya cigaba da magana "a zahirin gaskiya ammar baka kyauta ba sam sam bakayi wa adam adalci ba kafa san komai akanshi tun daga tahirin mafarkinsa irin tashin hankalin daya shiga alokacin da zaa aura masa maryam kuma kasan duk akanta ya kasa bawa matan dake mutuwar sonshi dama amman sai kayi masa haka kai da kamata yayi ka d'aukota ka kai masa ita ba sai kayi masa surprise ba   "kai dan allah naga ka damu dayawa yarinyar fa bata da aure yanzu amman ta ta'ba yin aure ."yana gama fad'ar haka ya cigaba da tafiya da sauri salim ya biyosa ya sha gabansa yana cewa "da gaske ammar ?murmushi ammar yayi yace "wallahi babu aure yanzu akanta nan dai ya zayyana masa komai daya faru daita bari naje na fad'a masa salim ya juya zai koma ammar ya rikosa "ka barshi tukun  zan fad'a masa da kaina amman sai naga karfin soyayyarsa gareta, ba dai yace ya hakura ba ?zan gani da gaske zai iya hakura daita kamar yadda ya saba hakura da komai ." da kallo salim ya bishi dashi fuskarsa dauke da murmushi yana mai qara godiya ga allah daya sa maryama ba matar aure bace ."

a qalla ata ya kusan minti talatin zaune yana nazarin maganar ammar wanda zuciyarsa take son ya dauka ahankali ya sauke naunayen ajiyar zuciya ya kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa tare da jan qaramin tsaki bai san me zaiyi ba idan yace zai dauki shawarar ammar "me kenan zaiyi ?"me ma yasa zai aikata haka ?duk runtsi duk wuya zai danne abinda yake ji akanta bazai ta'ba shiga gonar wani ba dakace babu auren kowa akanta ne to yana da tabbacin duk wanda yayi yunkurin aurenta to sai dai a bayan ransa amman yanzu bai ga abinda zai yi da wuce hakuri ba, yayi hakurin rashin ganinta abaya a yanzu kuma ya zame masa dole yayi hakuri da sabuwar qaddarar data samesa ,bama zai bari wani mahaluki yasan da zaman wannan labarin ba ". mikewa yayi cikin sanyi jiki zuciyarsa cike da rauni yana jin kamar ya zubar da kwalla ya shiga zagaye office din yana sauke numfashi kamar wanda yayi gudun tsare kafin ahankali ya shiga yamutsa gashin kanshi sannan ya koma kan kujera ya fara aiki akan system
zaune ata yake yana aiki amman sam tunaninta yaki barinsa ji yayi  kwata kwata  gara kawai ya cireta gbdy aransa ya huta ."

*****

A matukar jigace maryama ta karaso unguwarsu  da kyar qafafuwanta suka qaraso daita  cikin haraban gidansu  kai tsaye bangaren umma ta nufa tana layi inda ta iske su tare da hajiya grany suna ganinta a yanayin da take suka zabura suka mike cikin tsananin tashin hankali nan kuma suka shiga kallon kallo umma ta kalli hjy itama hjy ta kalleta a karshe suka maida hankalinsu ga maryama da kyar umma ta bud'e baki ta kira sunanta maryama !"da sauri ta qaraso gareta dan sam maryama babu kuzari ajikinta ai kuwa zubewa tayi ajikin umma ta fashe mata  da kuka tana kiran sunanta  umma .."
"Me..."me kuma ya   faru dake maryama "?cike da muryar kuka tace " sun wulakantani umma sun tozartani a qarshe kuma sun koreni a gurin aiki ta qarasa mgnr tana sake rushewa da wani sabon kuka Shikenan na sake rasa aikina ban san meke faruwa dani ba kamar ni kadai ce acikin  duniya ,laifin me nayi ?umma ki fad'a min meye laifina "kai kai karki sake cewa haka babu wani laifi da kikayi jarabawa ce ,itama hjy ta qaraso suka sakata a tsakiyarsu gbdy suka rud'e, umma na shafa mata kai hjy na shafa mata bayanta alamun rarrashi "akan wani dalili kenan suka koreki byn sun d'aukeki aiki ?" wai kawai dan nayi rejecting din ayyukansu wannan  kawai shine dalilin da yasa suka koreni byn ban yi hakan dan bana so yin aiki dasu  bane , nima ina son aikin nan amman alokacin suba'a  tafini bukatar shi allah ka gani nayi komai saboda kai ne."

" kun gani ba !shikenan allah ya amsa adduata ba ke uwar yan kankaba yau ga abinda gwaninta ya jawo miki sarkin iya taimako cewar Aunty hasana data fito daga kitchen ".haba hasana haba Hasana !dame kike son yarinyar nan taji ?idan bazaki mata addua ba ai  bai dace Ki fad'a mata haka ba."  ta kwabe fuska koma dai menene tunda ta rasa aikin ai shikenan bukatata  ta biya .ni a gurina wannan jarabawar daga allah ne kuma yana sane da komai bari zanje ma'aikatan da kaina naga mai kamfanin inji cewar umma "a'a umma karkije ,karki wani wahalar da kanki akan zuwa wajensu kawai suje su wulakanki a banza kamar yadda suka wulakantani "a'a bazasu wulakantani ba hakuri zan basu maryama "a'a ban yarda ba kuma wallahi ko kinje bazan qara komawa wannan kamfanin ba da sunan aiki bayan sun gama wulakantani sun tozartani har fa na fara aiki umma suka koreni basu ma tsaya sun fahimceni ba wai da gangan naki aikin dasu , wallahi banason aikin nan kuma kema bazan barki kije koina ba kuma ko zan mutu babu aiki bazan qara zuwa wannan kamfanin ba duk wannan maganar tanayi ne tana kuka har da shesheka "

umma ta rungumeta sosai ajikinta tana rarrashinta "kiyi hakuri maryama in sha allahu zaki samu sausauci ki cigaba da addau lokacin wahalarki  ta kusan zuwa karshe da izinin allah Aunty Hasana ta kallesu tana turo  masu baki alamun zund'e aranta tace "kwayi kwa gama idan wannan tsinanniyar yarinyar ce mai kashin tsiya ai duk inda arziki yake sai an korota ,sosai umma da hjy suka dinga rarrashinta har hankalinta ya d'an kwanta "yanzu umma kina ganin wata rana zan fita cikin wannan wahalar ?"sosai kuwa maryama  zaki fita mana wannan ai duk matakin d'aukaka ne amman fa idan kika d'aure kika d'aina fadar duk abinda yazo bakinki duk maseefar data samu bawa baa son yana yawo fad'ar abinda bai dace ba,abinda ake so mutun ya  yawaita furtawa inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ko lallaha illa anta subuhanaka inni kuntun minal zalim, ya hayyu ya qayyum ya zaljalalu wal ikram da sannu allah zai wanke miki zuciyarki da farinciki
."maryama ta share hawayenta ta zauna sosai a tsakiyarsu tana jin damuwarta ta yaye, ta kamo hannu umma cikin nata "wallahi umma  bakiga kamfanin ba komai a tsare kuma na dade  ina neman aiki a gurin tun alokacin da yaya sadam yaki amincewa da yin aikina  dole ce tasa na barwa subai'a wancan aikin "karki damu  nayi imani zaki samu aiki wanda yafi wanda kika rasa  Ke dai ki rike allah da adduar allah zai bi bayanmu .maryama tayi cikin jikin umma tace "Allah yasa ummah ina sonki mamana murmushi umma tayi tace "nima ina sonki maryama in sha allahu zaki ga haske arayuwarki "ummanki kawai kike so maryama nifa ?hjy ta fad'a tana dungure mata kai lumshe idanunta tayi tana dariya suma dai dariyar sukayi ."

*****

ATA na zaune  yana aikin  tura sako wayarsa ta dauki ringing ya dauki wayar ya manna a kunnesa yana lumshe ido  "yes kuna magana dashi ,okay kuna bukatar kaya new design ok just a second cewar ATA nan take ya kira sunan sectary ,sannan ya cigaba da abinda yake da sauri ta shigo  ta tsaya tana cewa "sir ! ya katse kiran byn ta shigo still ya cigaba da daddana system "mutumin dana gama waya dashi sabon  customer ne  yana bukatar kaya sabbin design dan haka Kiyi kokari ki hada Kan masu fresh design da muke dasu su bamu design masu kyau ayi abinda sabon customer zai ji dadi fatan kin fahimta "yes sir ."ko mu gwada sabbin dauka mugani ? " Eh hakan ma yayi domin muga kwarewarsu " okay sir "ta fita da sauri "maryama hussein ?!ya furta sunan a natse yana danna keyboard din system dinsa da karfi sannan ya cire hannunsa ya jingina jikinsa da kujerar da yake zaune yana jujuya jikinsa "waye mijinta a wani unguwa  take ?da gaske dai idan bai dauki shawarar ammar ba ya rasa natsuwa kenan kuma har abada dan ya tabbatar wa kanshi bazai iya rayuwa babu ita ba"waye mijinta a wani unguwa take duk yana bukatar yasani amman dole yabi komai ahankali darajan auren da take  dashi  ." amman dai zai nemi ammar din dan yana son yasan wani abu a game daita kafin yasan abun yi ."
Chapter 3 · 0% Book details