← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 111

Sashe 64

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Is okay maryama ki goge hawayenki zan nemo miki ita , nadiya sunanta ba anifa ba,zan nemo miki a duk inda take acikin fadin duniyar nan saboda na santa "maryama tayi saurin matsowa kusa dashi har gwiwowinta na gugan nashi "ya akayi kasanta ?sosai kuwa nasata ,amman naji kace nadiya sunanta ba anifa ba “?tabbas nadiya sunanta domin ta ta'ba aiki a daya daga cikin companies dina maganar da nake miki ma yanzu haka ta bukaci aiki da kafanina na auduga “amman ni ce min tayi tare sukai aiki da yaya sadam .”Ta yuwu sunyi aiki da sadam din tare bazan san wannan ba dan ta ta’ba aiki a IA company mahaifinta mai kudi ne sosai tru din wani abokin dad dina na d’auketa aiki a byn ,bata dade tana wani aiki damu ba tace zatai tafiya zuwa qasar amercan idan ta dawo zata sake neman aiki to ina ganin dawowarta ne ta sake tura mana sako neman aiki.”
Ya qarasa maganar yana mugun tsareta da kwayar idanun shi “maryama fad'a min me yasa kike son tsohon mijinki sosai haka ?tayi shiru qirjinta na bugawa fiyye da kaida ,tell me me zakiyi da mutumin da baya raye ?

Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
     MAR'ADAMS
     💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗

BOOK 3

*AYSHA A BAGUDO*

WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim

Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan  09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.

             Page 30

Shiru ne ya ratsa office din ,domin kuwa maryama ta kasa bashi amsar tambayarsa ,yadda ba tace masa komai ba haka shima bai sake cewa komai ba har tsawon mintuna shabiyar yana zaune yana kallonta shiru ko bata fad'a masa ya karanci tunani kala kala take acikin zuciyarta ,har ga Allah bata son yasan komai akan rayuwarta, ba dan komai ba sai dan tsare mutuncinta  amman kuma idan sanin nashi yana cikin taimakon da zai mata ta samu ganin nadiya  bata da option zatayi "maryama !ya kira sunanta da kasalalliyar muryarsa mai tsananin kashe sansar jiki da tsuma zuciyar wanda akayi dominsa"bana maimaita magana d'aya domin kuwa baya daga cikin d'abiata ,amaman akanki kullum sai na aikata haka why ?."still shiru tayi tana nazarin abinda zata fad'a masa wanda zai gamsar dashi "ki amsa min  tamabayata akwai abinda zuciyata take bukatar sani" tana can tunanin abinda zata fad'a masa kawai sai taji ya matso ya dawo daf daita sosai yasa hannunsa d'aya ya sake riko hannunta mai ciwo yana kallo  "karki ga na damu da son sani kiyi tunanin ina yin shishigi ne acikin abinda bai shafeni ba "no sanin dalilin shine kwanciyar hankalina "."

"maryama a karo na qarshe ki  fad'a min me yasa kike son tsohon mijinki sosai ?"ya qarasa maganar yana lumshe tsumammun idanunshi "hallaci ne !"ta fad'a hawaye  na zubo mata akan kuncinta, ajiyar zuciya mr ata ya sauke sannan ya bud'e idanunshi sosai akanta yana jin wutar soyayyarta na sake ruruwa acikin zuciyarsa yayinda qaunarta mai zafi ke nacin zuciyarsa, baya qaunar ganin damuwarta bare kuma zubar  hawayenta. ya kai hannunsa d'aya ya ciro hanky acikin gaban aljihunsa mai azababben qamshi ya soma  share mata hawayen dake gangaro wa akan kuncinta, qamshin turarensa mai sanyi  ya cika hancinta ta shaqa ahankali tare da lumshe ido nã second biyu sannan  ta bud'e tana kallonsa  tana jin wani irin yanayi a gabad'aya ilahirin jikinta ."kasa daina kallonsa tayi dan hk gabad'aya tsigar jikinta suka dinga mikewa tsaye ." kallonta ya sake yi a tsanake yana d'an cizan gefen lip's dinsa ahankali ahankali!!""hallaci mahaifiyarsa tayi min tun kafin nazo cikin duniyar nan ,haka shima yaya sadam yayi min hallacin ,kuma hallacin ne  yayi sanadiyyar dasa soyayyarsa mai qarfi acikin zuciyata wanda nake ji muddin ba dashi  ba bazan iya qara rayuwa da ko wani namiji  ba ."saurin runtse idanushi yayi daga tsura ma marayama idanu da yayi zuciyarsa cigaba da bugawa fiyye da kaida ."

Ahankali yayi baya kad'an da kujera da yake zaune akai yana jin wani irin tattukin bakinciki mai had'e da zazzafan kishi ,ji yayi gabad'aya ya muzanta a gabanta "ashe rashin furta mata soyayyarsa taimako kansa yayi, kuma shine abinda yafi zama alkhairi atare dashi ,shiyasa a kullum manazarta suke cewa duk mutun mai yawon surutu tabbas wata rana sai yayi nadama ,shi kuma mutun shiru shiru kullum cikin nasara yake sakamakon hangen nesan shi "na sani dukkanin rayuwar da nayi abaya rubutaccen qaddara ne ban isa na canzawa kaina ba cike da faduwar gaba ta fara bashi labarin abinda ya faru daita daga kan masu zuwa neman aurenta har zuwa sanda umma ta yanke hukuncin had'a aurenta da yaya sadam da abinda ya faru dasu akan hanyar dawowarsu daga ogun state ta qare maganr tana zubar da kwalla mai zafi tana jin zafi a qirjinta"nasan umma tana rayuwa ne kawai amamn har ta koma ga allah zuciyarta na d'auke da rad'ad'in rashin tilon d'anta wanda nice silar faruwar haka ."

mr ata ya kalleta cike da tsarewa da tausayawa "kin tabbatar a gabanki aka binnesa da ranshi  ?"wasu hawaye ne suka sake biyo kuncinta sakamakon tuno da tashin hankalin ,nan take jikinta ya kama rawa tamkar alokacin alamarin ya faru domin kuwa tashin hankali ne da bazata ta'ba mantashi arayuwarta ."
"idan zata manta komai daya faru a past dinta ban da wannan al'amari mai firgici "No !ni ba kuka nace ki min ba "ya fad'a yana dafe kanshi sannan ya sake kai hanky ya goge mata hawaye sai daya tsareta da tsumammun idanunshi sannna ta d'aga masa gira tace "yes a gabana suka haqa rami suka binnesa ta bashi amsa ."ya sauke numfashi yana dora qafarsa d'aya akan nata  batare daya san yayi haka  ba duk da qafarsa  sanye take da safa amamn sai data ji yadda ya sauke wata naunayen ajiyar zuciya wanda tasa hawaye ya gangaro daga idanunta  sannan a can qasan makoshi yace "amamnan maryama idan aka yiwa mutun haka me kike tunanin halin da mutun zai shiga?" ko a minti goma né bare an d'auki sama da kwanaki sannna kuma ke karon kanki kin kasa gane inda abun ya faru "?naunauyen ajiyar zuciya ta sauke kana ta motsa labbanta tace "babu tantama mutun bazai rayu ba ." yayi saurin  matso da kujerar da yake zaune  still tafin qafarsa na saman nata yace "okay anyi haka a gabanki but what are you still waiting "tayi shiru ta kasa cewa komai "mutumin nan baya raye maryama me yasa zaki dinga imagenation dinsa over?"

na sani nasan baya raye amman na rasa dalilin da yasa nake jin kamar yana raye "wallahi bana jin daidai arayuwata sakamakon rashinsa atare damu domin kuwa bani kad'ai nayi rashinsa ba hatta yanuwa gabad'aya sunyi kewarsa amamn basu kai ni ba"tsakninki da allah kina jin soyayyarsa ko tausayin mahaifiyrsa ne ke dawainiya da zuciyarki "?kamar yadda na fad'a maka a farko hallacci ne amamn a yanzu ina son shi har ina jin bazan iya rayuwa da wani namiji ba idan bashi ba  I really love him son shi da qaunarsa sun mamayeni ."yayi mata wani irin kallo yana  mai jin zafin mgnarta aransa amman sai ya dane tare da d'auke qafarsa akan nata ya juya tare da janyo laptop dinsa gabansa ya soma da daddana laptop din da qarfi a yadda yake operating din laptop din kasan acikin zafi zuciya yake ,yana daddanawa yana fitar da zazzafan numfashi yana jin wani azababben kishi from know where na shigarsa ."

"wato duniya juyi juyi ne yau gareka gobe ga d'an uwarka ,abinda ya baka dariya wata rana shi zai sakaka kuka ,dan girgiza kanshi yayi yana zance zuci wato shi kuma haka qarshen soyyarsa ta zama yana son maso wani ,ina ma mafarkinta ya cigaba da yi da wannan lukutar matseefar da ta samesa .wai kamar shi yau soyayya take kutimememiya dashi haka ?""karkaji komai aranka adam, sannan karka manta ita soyayya allah ne yake sakata acikin zukatan wad'an da yaso ,kuma babu wanda ya isa ya rabata ko kuma ya hana faruwar abinda allah ya had'a kai kanka da kasan haka rayuwar soyayyarka zata zo a qarshe da duk yadda zakayi ka goge shi dakayi amman dake had'in Allah ne  har ma yake jin babu abinda zai iya sawa ya juya mata baya ko kuma ya daina sonta dan  a yadda yake jin  soyayya da qaunar da yake mata babu wani abu a duniyar da zai firgitashi har yaji zai iya hakura daita  to kuma ai ita zuciyarta ta tsundu ma acikin tafkin son wani ?"zuciyarsa tayi saurin tunatar dashi "uhm ai kuwa akwai bala'i dan  kuwa ta  qarfi da qarfafa zai shigar  daita tsundum cikin kogin sonshi har ta manta ta ta'ba son wani a duniya yayinda ita kuma maryama sai goge hawaye take wasu na sake gangarowa muryarsa a tsarke yace  "kiyi hakuri banyi miki wad'an nan tambayoyin dan na 'bata miki rai ba." karka damu sir dan nima banji komai ba"ni dai ina bukatar nadiya ina son nasan wani abu dan  gabadaya a tsorace nake tana bani tsoro matuka bansan me yasa take bibiyar rayuwata ba ."
Chapter 64 · 0% Book details