← Book details Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 111

Sashe 8

Mar'adams Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari bai tashi da wuri ba sakamakon rashin baccin da bai samu ba adaren jiya ,sai bayan sallah asuba bacci mai nauyi ya daukesa ,shigowar mami biyu dubasa bai tashi ba ,da misalin karfe d’aya ya sauko nan ya iske mami tare da zabiba da yaranta biyu suna ganinsa suka zo gurinsa da gudu suna kiran sunansa d’aukar ammi yayi mai sunan mami ya cillata sama yna mata wasa sannna ya riko hannun siyam yana cewa “yaushe kuka zo gidan “? zabiba tayi murmushin jin dadi tace “bamu jima da zuwa ba ina yini yaya ?shareta yayi tmkr ba dashi take ba yace “good morning sweetheart?morning or afternoon adamcy ka kalli lokaci ka gani bai kalli agogo ba yace “ai dan bamu had’u bane da safen shiyasa sai yanzu .”murmushi ta saki tare da dafa hannunsa dake kan nata kai dai wallahi bahagon mutun ne” numfashi kawai ya sauke yana jan yatsun hannun ammi “mami ta kallesa a tsanake “yaakayi kanwarka tana gaisheka amman kayi mata banza ?ka dinga yiwa yanuwanka uzuri ka yafe masu wannan matslar fa ba wata matsla bace da zaka riketa gam a ranka yanzu ko bayan raina haka zaka dinga hukuntasu idan sunyi maka laifi ?” to a ina kake son su saka ransu idan wata matsla ta kunno kai cikin rayuwarsu ?.”uncle see aunty girl ta hanamu mu fita muje wajen yesmen kuma mu muna son zuwa siyam tayi maganr tana nuna masa mami da yatsanta .”

“murmushi yayi jin suna da take kirata dashi “karki damu aunty girl zata bari kuje kuga yesmin no kace ta barmu muje yanzu saboda yesmin mukazo inji cewar siyam “siyam take your sister and meet tabawa idan zamu wuce zan kaiku ku ganta shikenan tashi sukai suka wuce rike da hannun juna yayinda ata ya bisu da kallo yana lumshe ido yana jin ina ma yaransa ne .”ahankali ya bude idonsa yana motsa lips dinsa “shikenan sweetheart komai ya wuce amman gsky ban so na sauko hk da wuri ba har sai bayan shekaru masu yawa “Au yanzu nan ka sauko da wuri kenan wajen wata biyar ?ya lumshe mata tsumammun idanunshi kawai kallonsa zabiba tayi cike da tausayawa tace “allah dai ya huci zuciyar babban yaya in sha allahu bazamu sake ba “kuma sake ya fad’a tare da mikewa ya nufi kofar fita yana cewa “sweet heart sai nã dawo “bazaka karya bane ?bana jin cin komai sai dai na dawo kawai “to a dawo lafiya Allah ya tsare “Ameen !” ya amsa ya nufi kofar fita .”

kai tsaye hanyar kamaninsa aka nufa dashi yana zaune hannunwansa rike da jaridar daily trust yana karantawa yana son wani abu ya d’auki hankalinsa na son kawar da tunanin maryama acikin ransa amman aikin banza yayi domin duk shafin da zai bud’e sai fuskarta sai ta bayyana aciki wani dogon tsaki yaja ya ajiye jaridar hannunsa ko da yake shima yasan dole abun zai damesa kuma zai hana rayuwarsa sukuni har suka qarasa office dinsa tunaninta ne fal acikin zuciyarsa bai dade da zama ba sai ga some ta shigo bayan ta nemi izinin shigowa wasu file ta ajiye agabansa cike da girmamawa tace "sir ana bukatar saka hannunka anan” bai ce mata komai ba ,ya kar’bi biron data miko masa batare da bata lokaci ba duk ya sign ta kwashe file din ta fice tana satar kallonsa dan da alamun yana cikin damuwa duk da dai ko yaushe fuskar nan tashi a hade take amman na wannan karon ya zarta na sauran lukuta har tayi taku biyu sai kuma ta juyo ahankali ta dawo inda yake zaune ya d’an d’aga kwayar idanun shi ya kalleta sannan ya d’auke idanunshi “sir ko zan iya cewa wani abu ?shiru ya biyo bayan mgnrta na second biyar sannan yace “zaki iya “sir yau yanayinka yayi wani iri Kmr akwai wani abu dake damunka “yes akwai abinda ke damuna wanda nake jin kamar na kashe kaina .”

”what ?ta fad’a tana zaro ido kafin ta sake mgn yace “you can leave shiru tayi tana dubansa rike da file ganin haka yasa ya janyo wasu file gabansa ya shiga dubawa duk a qoqarinsa nason ya manta da komai alokacin amman ya kasa duk shafin daya bud'e still dai hoton fuskarta yake gani tana hawaye cikin mummunar tashin hankalin data bar office dinsa jiya ."tsaki yaja yana dukan table din gabansa da karfi “what’s all nonsense ya fad’a yana mai rike goshinsa da hannunwansa duka yana jin wani irin zugi from no where”ke kuma tsayuwar me kike yi ?yayi mgnr a tsawace da sauri ta nufi kofar fita cikin zafin zuciya ya zabura ya mike tsaye ya fara zariya acikin office kafin ahankali ya tsaya cak a tsakiyar office yana dogon nazari kusan minti goma yana tsaye yana qoqarin nemawa kansa mafuta domin dole ya nemowa kanshi mafutar da zai rabu da tunaninta gabad’aya ya huta saurin waiwayowa yayi sakamakon jin sautin muryar ammar a bayansa .”
Bai ce masa uffan ba yaja wani dogon tsaki yana mai d’auke kwayar idanunshi akansa cike da jin haushinsa domin a yanzu ya gane shine ma damuwarsa ,shine mutumin daya bari ya rasa duk wani farincikinsa duk yadda yasan halin da yake ciki amman yana ji yana kallo yarinyar nan ta zama mallakin wani bashi ba .”

ahankali ata ya kasa dauke tsumammun idanunshi daga kan ammar yana jifansa da wani mugun kallo mai d’auke da fassara dabam dabam ahankali ammar ya dawo gaban ata ya tsaya yana kallonsa kamar yayi dariya amman sai ya share saboda ganin fuskar ata din har lokacin tana cikin yanayi na damuwa da tashin hankali wanda kuma yasan na rasa maryama ne shima ata kallonsa yake amman kallon tsana ammar ya saki fuska yana murmushi wanda bashi da maraba dana mugunta “mamaki murmushin ammar ata yake wato ya cucesa kuma yazo ya tasa shi gaba da murmushin mugunta ?sai da ammar ya bashi wasu mintun sannna ya fara magana “haba friend kar dai maryama ce ta gigita rayuwarka haka ?bai kulashi ba sai ma sake had’e fuska da yayi sannna ya juya ya bar wajen “cikin daga murya ammar yace “daman nasan sai tayi wuji wuji da rayuwarka tasa ka fad’i kasa warwasss cak ata ya tsaya yana cizan lip’s dinsa kamar yayi masa mgn sai km ya cigaba da taku ya nufi d’akin dake cikin office wata dariya ta subucewa ammar alokacin da ata yake qoqarin shigewa d’akin bai san sanda ya juyo a fusace yace “kai me kake nufi ne wai dani ?”

“Oho abinda kake nufi nima shi nake nufi yana daga inda yake ya girgiza kai had’e da cewa “ka shiga hankalinka ammar da wannan dariyar da kake “na shiga hankalina ko dai ka shiga hankalinka ina ta faman kiranka a waya tun jiya kaki dauka yanzu kuma nazo ina ta mgn ka min shiru sai faman cika kake kana batsewa “idan dan abinda ya faru ne kake fushi kayi hakuri amman dai yanzu abar duk wannna maganr nazo maka da wata magana ne mai mahimanci .”a wulakance ata yake kallonsa tare da cewa “bana bukatar komai daga gareka coz I hate you !I hate you ammar ganinka da maganarka babu abinda yake qara min ayanzu illa jin bakinciki da tarin tsanarka acikin zuciyata.” da sauri ammar ya matso kusa dashi yana qoqarin riko hannunsa yay saurin ja baya “don’t try me ammar! ya fad’a a matukar fusace ammar bai damu ba dan yasan halinsa ya matso sosai yana dubansa “wallahi ammar ka cuceni ,ka cuci rayuwata bazan ta’ba yafe maka abinda ka min ba sakamakon kasan duk wata damuwa dake tattare da shafukan rayuwata akan yarinyar nan amman dan mugunta irintaka ka cutar da zuciyata, yarinyar da zaka d’aukota musamman ka kawo min ita nayi tozali daita ba wai ka tsaya yi min wasa da hankali ba wallahi ka cutar dani ammar gashi har wani yayi galaba aureta “.

ka tsaya kaji mai zance maka yanzu “bana son jin komai ammar macuci mugu kawai mai bakar fuska ya fad’a yana hadashi da wani kyawawan mari. duk wannan maganar a zuciye yake yi yana cewa “get out from my office I don’t want to see your face again tare da point dinsa da hannusa kana ya cigaba da magana kamar zai zubar da hawaye” dan iska kawai da kai mai zaka fad’a ?bayan ka gama lalata min rayuwa sannna kazo kana cika ni da surutu banza da wofi “Adam ni ka mara ?an mareka wallahi idan ka cika da surutu zan qara maka kuma babu abinda ka isa kayi banza mara mutunci maci amanar abota wallahi ka gama cutata “enough ata bafa tsoronka nake ji ba na cuceka ko ka cuci kanka ?”ya fad’a tare da jan tsaki “.“Oh haka ma zakace kenan “?kenan har yanzu kana da karfin halin cigaba da bata min rai ?wai tsaya ma na tambayeka kai masoyina ko makiyina?”duk matsayin daka bani na kar’ba “okay na baka matsayin makiyina domin duk duniya kaine makiyina na farko kuma na tsaneka fiyye da tsanar da nayi maka daga yau ammar babu ni babu kai ka cire ni acikin duk wata danganta amman kafin nan zan shiga ciki dan girman allah ka cigaba da tsayuwa har na fito kaga yadda zanyi da kai yana gama fad’ar haka ya juya yana sauke numfashi sama sama .”jiki a sanyaye ammar yake kallon kofar daya shiga kamar ya shiga amman yasa shigarsa bazai haifar masu da mai ido ba kuma bazai sauraresa yaji abinda ya kawo sa ba cike da zafin zuciya ya fice .”

*******
Chapter 8 · 0% Book details